Page 6

1.3K 101 3
                                    

👉🏽💍 *KYAKKYAWAR ALAK'A* 💍👈🏽

                 ©
  *ZULAYHEART RANO*
*Wattpad user name Zulayheartrano89*

*STORY AYSHA WAZIRI*

                    *06*

SALMAH na tare da kawayen su Yahanasu, sai bayan magriba aka umurce ta da ta sake kayan jikinta, sabbin kaya ta sanya aka dauketa zuwa bangaren da zasu zauna, da yake ciki gidan ne babu wanda ya tsaya sai kawayen ta, kwana Salmah ta yi tana addu'oi akan Allah ya karkato da hankalin Yarima kanta, domin ta cika da mamaki tare da tsoron yadda ko kadan Yarima bai ko nemeta ba, washegari suna zaune bayan sun gama break kawayen ta sai hira suke hankali kwance amma ita Salmah tunanin da take har yasa bata jin abin da suke cewa.
   Da mutuwar jiki Salmah ta wuni har zuwa yamma, Adda Hafsah ta shiga bangaren tana faɗin ta shirya anjima za a yi budar kai, da kai ta amsa kawai ta kara kwanciya sai karfe hudu ta yi wanka, da taimakon Adda Hafsah ta shirya sannan kannan Yawuro suka dauketa zuwa cikin gida, gaban Yawuro aka aje Salmah, Yawuro ta fara bude kan Salmah sannan sauran mutane, kudi sosai aka tara mata ba na wasa ba. Sannan aka ba kowa damar ganin fuskar amarya.
    Ba su koma ciki ba sai bayan magriba, sallah ta fara yi sannan ta sake feshin jiki da turaruka, zaune ta yi a bakin gado tana kallon yadda kawayen ta keta shiri domin da angwaye sun shigo ko wacce zata tafi gidan ta, suna jin alamar shigowar su Yarima suka rufe Salmah tare da wasu daga cikin kawayen ta biyu cikin bargo, sallama su Yarima suka yi suka shiga cikin bedroom din direct wajen da aka rufe su Salmah suka nufa, gaban Salmah ya yi mummunan faduwa har wasu hawaye suka taru cikin kwar min idonta, domin tasan babu makawa yau zata shiga cikin gorin jama'ar gari don Yarima ba ganeta zai yi balle ya nuna ta, da yake al'adar su idan an rufe
       Amarya da kawayen ta biyu da katuwar blanket, Ango shi da abonka suke nufa wajen da aka yi boyon sai ango ya nuna amaryarsa, idan har ya kuskure ya nuna wacce ba amaryarsa ba to fa lallai kin shiga bakin mutanen gari haka za a yi ta ce wa ba ya sonki, sannan a ranar ke kaɗai za ki kwana ba tare da ango ba, amma da ya nuna ki farin ciki ne zai rufe ki da sauran jama'a hakan ya nuna zai iya gane ki ko a inane, kamar almara haka ta ji Yarima ya daura hannunsa akan Salmah, gaba daya kawayen suka ɗauki sowa, shi kam bai tsaya jiran su ba ya tsuguna tare da yaye blanket din yana faɗin "Barka da zuwa Salmatyy." Bata iya cewa komai ba sai mik'ewa ta yi tsaye tana binsa da kallo bai zame ko ina da ita ba sai bakin gado inda ya yi mata masauki,
      Mik'ewa ta yi cike da kwarin gwiwa ta nufi inda suka aje lafiyayyun naman kaji da madara mai zafi, amsa ya yi ya fara sha sannan su rabawa abokan angon nono suka sha, bayan sun gama suka kwashi kawaye aka bar Salmah da Yarima kadai a cikin dakin, takurewa Salmah ta yi can jikin bango kamar wacce ta yi laifi, Yarima kuwa hankali kwance yake kurbar madaran sa har ya kammala, hamdala ya yi ga Ubangiji sannan ya mik'e ya nufi toilet ba tare da ya kalli inda Salmah take ba, bai jima ba ya fito Salmah na kallo ya shimfiɗa sallaya, sallah ya yi raka biyu ya yi addu'oi bayan ya sha ya nade sallayar ya maisheta mazaunin ta, bakin gadon ya nufa inda Salmah ke rabe, kallonta ya yi na wasu mintina sannan ya ambaci sunanta "SALMAH!" A ɗan razane ta ɗago murya tana rawa ta amsa "na'am."
        "Tun da baki cin komai tashi ki yi alwala ki kwanta." Fuska ba yabo babu fallasa ya yi maganar. "To." Ta amsa jiki har yana rawa ta nufi toilet din, wanka ta fara sannan ta yo alwala sallah ta yi shafa'i da wuturi, bayan ta yi addu'oi ta mike tana hamma, babbar matsalar ta shi ne yadda zata sanya rigar bacci, domin bata iya kwanciya sai da rigar bacci gata kuma yau tare da Yarima tana kunyar yadda zata canza kaya, Yarima na kallonta sai dai bai ce komai ba sai tashi daga gadon ya yi, a nashi tunanin kila kwanciya zata yi kuma tun da yana kan gadon bata iya kwanciya, gani ta yi ya bude kofa ya fita falo cikin sauri ta dauko rigar ta sanya, mai kauri ce sai dai bata da wani tsawo kuma kusan saman a bayyane yake, zama ta yi a bakin gadon tana jiran dawowan Yarima amma sai ta ji shiru, ga bacci ga tsoro duk addu'ar da tazo bakinta karantawa take a ta kai kusan karfe uku bacci bai dauketa ba, sai da kyar bata ma san lokacin da ya kwashe ta ba cike da tsoro, shi kam Yarima dakin da yake a matsayin mallakinsa ya shiga, domin a ganinsa ya takura Salmah shi yasa ta kasa sakewa, shi kuma har ga Allah ba ya son takura ta, wanka ya yi ya shirya cikin tattausan rigar baccinsa ya feshe jikinsa da turaruka masu kamshi, sannan ya kwanta zuciyarsa fes domin yau cike yake da farin cikin ya samu mallakinsa, a duniya babu macen da yake so irin Salmah.
     Bacci ya yi mai dadi bai farka ba sai karfe biyar saura, alwala ya yo sannan ya tada kabbara, Salmah kam tana jin ankira sallar asuba ta yi saurin dira daga gadon, alwala ta fara sannan ta fito bata tsaya cikin bedroom din ba domin mugun tsoron da take ji, falo ta koma ta shimfiɗa sallaya sai da ta yi raka'atanil fijir sannan ta gabatar da asbah sai da ta yi addu'a sannan ta koma kan kujera ta kwanta babu jimawa bacci ya dauketa.
     Shima bangaren Yarima ko da ya idar da sallah bacci ya koma bai farka ba sai karfe takwas, jallabiya ya sanya fara sol sannan ya fita falo, turus ya yi ganin Salmah kwance akan kujerar falon ga sallaya shimfiɗe, hakan ya nuna masa a falon ta kwana kenan, girgiza kai ya yi ya matsa inda take kwance gani ya yi tana ta zufa don fankokin da A.C cikin falon a kashe suke, kamar ya barta sai kuma ya kai hannu ya cire mata hijjab ɗin ko motsi bata yi ba sai, gefe ya zauna tare da zuba mata ido yana kare mata kallo tun daga yatsun kafarta har tsakar kanta, a kirjinta ya tsayar da idonsa kusan rabinsu a waje suke domin rigar baccin jiya ne a jikinta da zata yi sallah dogon hijjab ta sanya.
     Kara tsira mata ido ya yi cikin wani irin yanayi da shi kansa bai ma san da shi ba, ya dade yana kallonta daga karshe daukarta ya yi cak zuwa bedroom domin yana tsoron kar wani ya zo ya samu tana bacci, cikin baccinta mai dadi har tana kara rungumarsa a kan gado ya yi mata masauki ya gyara mata sumar ta da suka barbaje, gefe ya koma yana rike mararsa shi yasa tun farko baya iya sakewa da mata domin yasan matsalar sa, ko kallon mace ya yi yana iya shiga wani hali balle kuma jikinsu ya gogu da juna.
      Yanzu zai nemi nutsuwa ya rasa, ga shi yau ya haɗa jiki da Salmah bai taba ko da kawo haka a ransa ba, da kyar ya tashi zuwa firij ɗin bedroom ɗinsa ya ɗauko maganin da ya zamar masa kamar abinci, sha ya yi sannan ya koma wajen Salmah don yana tunani tsoro ne ya hana Salmah kwanciya a bedroom, daga gefe ya kwanta bacci mai nauyi ya ɗauke shi, a hankali ta fara motsi tana buɗe ido har ta bude su duka, kara mutsuka ido ta yi ganin ta a bedroom kuma ga Yarima a gefe, mamaki ta fara shin yaushe ta shigo bedroom? Ita da ta yi kwanciyar ta a falo, ko dai a magagin bacci ta dawo bed din? Tambayoyi ta tawa kanta wanda bata da amso shin sa, daga karshe ta mike ta nufi toilet wanka ta yo sannan ta fito gaban mirror ta yi fakin kwalliya ta fara tsarawa fuskarta, sannan ta ɗauko kayanta riga da siket na atamfa wanda suka yi mata kyau sosai, har dai ta gama Yarima bai farka ba falo ta koma abinta don ta gaji da kwanciya.
   Yarima bai farka ba sai karfe tara, wanka ya fara yi ya fito daure da towel a kugunsa, da karami yana goge ruwan kansa, hankali kwance ya fita zuwa dakinsa domin ya shirya, tun da ya ga babu Salmah a dakin yasan tana falo, tana zaune sai gani ta yi ya fito ai da sauri ta sadda kai kasa tana wasa da zoben yatsun ta, bai bi ta kanta ba ya wuce abinsa a tsanake ya kammala shiryawa cikin dakakkiyar shadda blue wacce ta matuk'ar amshi jikinsa, ya yi kyau sosai sai fitar da kamshi jikinsa ke yi, falo ya fita Salmah na ganin ya fito ta yi saurin zubewa tana faɗin "Barka da safiya Hamma." Kallon karamin bakinta ya tsaya yi, sai kuma can ya saki murmushi wanda tun tsayin rayuwarta bata taɓa ganin ya yi murmushi ba "Ummuna haka ake gaida miji?" Ya yi tambayar fuska sake.
       Bata yi magana ba sai kara ƙasa ta yi da kai, a hankali yake takawa har inda take zaune bata yi aune ba sai ji ta yi ya jawota jikinsa yana faɗin "Kin ga haka? To irin sa ake ya yin gaida miji." Dire maganar yana dage mata gira daya, wata irin kunya ne ya saukar mata ta rasa yadda zata yi domin fuskarta na tafin hannunsa. Lumshe shanyanyun idonta ta yi tana sauraron abin da Hamma Yarima ke shirin yi mata.
     Kara matseta ya yi ya ce "wai magana ma yau ba zan samu arzikin a yi min ba ne? Ko sai na saya?" "Hamma yunwa nake ji." "Oh! Sorry My madam bari na amso mana abin break." Ya dire maganar yana manna mata tsadadden kiss a kumatu.

Vote me
Comment
& Shere on wattpad

Zulayheart Rano

KYAKKYAWAR ALAK'AWhere stories live. Discover now