Page 29

1.1K 59 6
                                    

👉🏼💍 _*KYAKKYAWAR ALAK'A*_💍👈🏼

*REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S* *_P.M.L_*

                     ©
   *ZULAYHEART RANO*
*Wattpad username zulayheartrano89*

*STORY AYSHA WAZIRI*

_Deducated  dis page for my wattpad fan's, kyauta na baku wannan page din musamman yadda kuke nuna soyayyar ku ga wannan labarin, i love You fisibilillahi!_

                 _*29*_

Har ta isa bangarenta bata daina hawaye ba, cikin zuciyarta tana dana sanin zuwanta ɓangaren Hajja a daidai wannan lokaci, tabbas da ta san irin wannan maganar zata ji babu abin da zai kaita, amma ba a tara sani ga mahalicci, sai dai har yanzu wani bangare a zuciyarta bata gasgata maganar da kunnen ta suka jiyo mata ba, duk kuwa da cewa a bakunan wanda ta ji maganar ba za su yi mata karya ba, balle su kirkiri magana.

A kujera ta zauna tare da zuba hannu biyu ta tallafe fuskarta, don ta rasa wane irin tunani zata yi, ambaton Allah kawai take, sai dai duk da haka bata samu kwanciyar hankali ba, a cikin haka Yarima ya shigo falon, hannunsa rike da Khairat dake kananun kuka, da kallo ya bi Salmah musamman yadda ya ga hawaye na kwarara a idon ta.

"Ummuna!" Yarima ya ambata da wani irin voice.

Sam bata ma san Yarima yana yi ba, domin sosai ta lula duniyar tunani, sai da ya kara matsawa sosai kusa da ita ya ce

"Ummuna!"

A dan firgice ta dago da kanta

"Nan na'am." Ta fada tana goge hawayen.

"Kuka?" Yarima ya yi tambayar hankali a dan tashe.

Bata yi magana ba sai sanya hannu ta yi tare da amsar Khairat, ta daurata akan cinya sannan ta fara shayar da ita.

Idon Yarima kyeer a kanta, sai da ya yi kusan minti uku kafin ya ce "Mai ya sanya ki kuka Ummuna?"

Murmushi ta yi, masu karatu  fatan dai kun gane wane irin murmushi Salmah ta yi, domin murmushi ne ta yi irin mai ciwo, sannan ta tattaro duk wani kuzari da take da shi ta ce "Babu komai Hamma kawai wani abu ne ya shiga idona, na yi na yi ya fita bai fita ba.

Sam Yarima bai yadda da abin da Salmah ta fada ba, domin yasan Salmah ya kuma san halin ta, tabbas akwai abin da aka yi wa Salmah har take kuka, kar dai a ce ta ji labarin aurensa? Ya jefa wa kansa tambayar da ya haddasa masa faduwar gaba.

Saurin tattaro nutsuwar sa ya yi ya ce "Ayya sannu Salmatyy ki sanya magani."

Toh ta amsa ya yin da ta ci gaba da shayar da yarta, shi kam Yarima hannu biyu ya sanya yana shafe sumar kansa, gefen zuciyarsa cike take da kewar Nuwaira, yana son kiranta sai dai yana tsoron kar Salmah ta ji... Tunanin sa ya tsaya ne daidai lokacin da ya ji wayarsa ta dau tsuwwa, hannu ya kai tare da ciro wayar daga aljihunsa, kai idonsa kan screen din wayar ta yi daidai da faduwar da gabansa ya yi.

Domin kuwa sunan Nuwaira ce ya fito ɓaro-ɓaro, juyowa ya yi tare da satar kallon Salmah, sai ya ga kamar bata ma san an kira wayar ba, duk da haka bai ji zai iya ɗaukar wayar ba, don haka sai  ya yi saurin aje wayar tare da jingina kansa da kujera, yana ci gaba da shafa sumar kansa.

Murmushi takaici Salmah ta yi kasa-kasa, domin kuwa tun daga farkon kiran wayar idonta ke kan Yarima, har sai da taga zai juyo ya kalleta sannan ta yi saurin dauke kai. Mik'ewa ta yi saɓe da Khairat a kafada wacce ta yi bacci, tana faɗin "Hamma bari na kwantar da Khairat, ashe bacci take ji."

"Allah sarki Hajjata, shi yasa take ta kuka ashe, idan kin shiga ki hada min ruwan wanka Please."

"Tom." Tana shiga bedroom.

KYAKKYAWAR ALAK'AWhere stories live. Discover now