Page 13

1K 62 2
                                    

👉🏽💍 *KYAKKYAWAR ALAK'A* 💍👈🏽

                               ©
              *ZULAYHEART RANO*
*Wattpad user name Zulayheartrano89*

*STORY AYSHA WAZIRI*

                     *13*

"Dauke da ciki fa, dubi yadda ta yi wani irin canzawa, yanzu kuma ga zazzaɓi ko a kira Dr ne ya duba ta?" "Eh! Kiran Dr ya fi, domin a tabbatar." A haka suka tsaya, bayan jakadiya ta Hajja wajen Salmah ta koma, yanzu kam zazzaɓin ya ɗan sauka har bacci ya dauke ta, babu jimawa Dr ya iso cikin gwaninta ya fara duba Salmah da yi mata tambayoyi. Sannan ya amshi fitsarin ta don yin gwaji. Dr bai wani dade ba ya dawo da sakamakon gwajin inda ya tabbatar da Salmah na dauke da cikin sati hudu, har goron albishir sai da Maimartaba ya ba Dr, cikin kankanin lokaci har maganar cikin Salmah ya karaɗe gidan Sarki, sosai suka yi farin ciki da samun wannan k'aruwa.
    Yawuro da Hajja sun yi matukar farin ciki, sai dai basu nuna afili ba domin Alkunya da kawaici, sai dai Hajja Chub'ad'o bayan jama'a masu zuwa duba Salmah sun yi sauki kyakkyawar alwala ta dauro ta zube gaban mahalicci tana nuna masa godiya da farin ciki, ta yi addu'a sosai kusan akan Yarima da Salmah ya fi yawa. Sai dai fa Maimartaba ya yi gargadi kar wanda ya sanarwa da Yarima, don a irin rawan kansa nasa zai iya dawowa duk da yau ya tafi.
    SALMAH ma ta yi farin ciki sai dai ta kasa ko da kallon Hajja, domin bata taɓa sanin tana da kunya ba sai yau, musamman da Dr ya faɗi tana dauke da ciki "shi kenan yanzu kowa yasan abinda da muke yi da Hamma Yarima a daki?" Tambayar ta yi wa kanta tana kuma lafewa akan gadon, sai dai duk da haka ta yi farin ciki, ma ra misaltuwa domin a rayuwa bata da wani buri sai na ganinta da jinin Yarima, tana ci gaba da addu'a Allah ya dauwamar da KYAKKYAWAR ALAK'AR su har karshen rayuwarsu. Zaituna ce ta yi sallama tare da zubewa gaban Salmah, tana kwasar gaisuwa da kulawa Salmah ta amsa, sannan ta ce "Uwardakina me za a dafa maki?" Cike da ladabi Zaituna ta yi tambayar. "Bana jin cin komai Zaituna amma ki kawo min inabi su kadai sun isa. "An gama ya shugaba ta." Zaituna ta faɗa tana fita. "Me take buk'ata Zaituna?" Hajja ta tambaya tana muskutawa. "Ta ce bata bukatar komai ya shugaba sai 'ya'yan itatuwa." A ladabce ta bata amsa. "Ki kai mata 'ya'yan itatuwan sai ki daura mata abincin mai ɗan ruwa-ruwa." "To shugabana an gama." Da azama Zaituna ta kai ma Salmah inabi ɗin kamar yadda ta bukata, kusan a tare suka shiga da Hajja, Zaituna tana ajewa ta ce "uwardakina ga inabi ɗin na kawo." "To na gode Zaituna." Salmah ta faɗa tana tashi zaune, sam bakinta babu daɗi "sannu Salmatyy ya jikin?" "Da sauki Hajjata." Salmah ta bata amsa tana kasa da kai, murmushi kawai Hajja ta yi tare da zama tana jawota jikinta.
    "Kin ce baki cin komai sai inabi?" "Eh! Hajja bakina babu dadi ne." "To sannu na sanya a yi maki girki mai ruwa-ruwa ki daure ki ci." "To Salmah ta amsa tana jawo tiren da aka zubo inabi din, a hankali take kaiwa baki har ta ci da yawa sannan ta mai da tiren gefe ta gyara kwanciya sam jikinta babu daɗi, kewar Yarima da ciwo sun hanata sakat, lumshe ido ta yi tana tunanin irin farin cikin da Yarima zai yi idan ya ji tana dauke da gudan jininsa.
BANGAREN YARIMA kuwa bayan ya sauka, a Bauchi duk sai ya ji babu daɗi musamman da zai shiga wanka, ya saba tare suke wanka shi da Salmah amma yau shi daya zai yi, jiki babu kwari ya shiga toilet dake cikin bedroom din, wanka ya yi shaf-shaf don yunwa yake ji, yana fitowa kananun kaya ya sanya bayan ya shafe jikinsa da cream nasu taushi, dambun nama da five aleve ya ɗauko yana ci yana sha, har sai da ya koshi ya kwanta jikinsa cike da kewar Salmah ko a wani hali take yanzu, da sauri ya dauki wayarsa tare da danna lambar ta, lokacin Salmah tana kwance bayan ta gama cin abincin da Hajja ta sa aka girka mata ringin biyu wayar ta yi Salmah ta dau da sanyin murya ta ce "Assalamu Alaikum Hamma." Daga daya bangaren Yarima ya amsa "wa'alaikumus salam Ummuna barka da warhaka!" "Barkammu dai Hamma fatar ka isa lafiya." "Lafiya lau Ummuna gani a gida har na yi wanka yanzu na kammala cin abinci." "Madallah! Da ka sauka lafiya, me ka ci Hamma?" "Dambun nama da Hajja ta bani, Ummuna ina kewarki sosai fa." "Nima haka Hamma zuciyata da gangan jikina suna kewar Hamma." "Ko in dawo gobe ne?" Yarima ya faɗa yana tashi zaune. "Da zaka dawo gobe zan zo haka." Ta gama maganar tana juya ido. "Da gaske Ummuna in dawo gobe?" Ta bude baki zata yi magana kenan adda Amina ta yi sallama, don haka amsa sallamar Aunty Ameena ta yi tana faɗin "Hamma sai anjima zamu yi waya." Kafin ya ce komai har ta katse wayar.
    Gaisar da Adda Ameena ta yi tana yi, sannan Adda Ameena ta fara mata ya jiki daga nan suka shiga hira, Adda Ameena na bangaren Hajja har bayan magriba, sannan Hamma ɗan Waziri ya zo suka tafi bayan ya duba jikin Salmah. Haka Salmah ke ta samun kula duk abin da take so ana yi mata, daga ko wane bangare Yawuro ma ba a barta a baya ba domin tana yi wa Salmah abu a matsayin uwar Yarima, Salmah yar gata gaba da baya har wani kyau ta yi na musamman.
   Wani lokacin zama take tana shafa cikin tana mamakin ta yadda har yanzu ko alamar tasawa cikin bai yi ba ( cikin da ke da sati shida yanzu shi ne ake cewa bai tasa, hmmmm! Anya kuwa Salmatyy na da alkunyar Fulani? Ko da yake goyon Yarima ce, ban ce komai ba team Yarima.) A daddafe Yarima ya yi sati Uku domin aikin da ya taso shi gaba, kullum kewar Salmah ke dawainiya da shi, da ya samu sukuni sai ya shiga tunanin Salmah, duk da kullum suna tare a waya, yau kam da ya samu sauƙin aiki a office karfe hudu ya dawo gida, ya ci burin a Ningi zai kwana, bai shirya ba sai da ya gama waya da Salmah yana jaddada mata kewarta da ya yi, bayan sun gama ne ya yi wanka ya shirya, kafin ya tafi sai da ya bada umurnin a gyara gidan domin tare da Salmah zai dawo.
   Bai dau hanya ba sai hudu da kwata, a hankali da nutsuwa yake jan motar, har Allah ya sa ya sauka lafiya, har a time ɗin Salmah bata san yana zuwa ba, bai shiga gida ba sai da suka gabatar da sallar magriba, a masallaci ya gaisa da iyayensa bai shiga ɓangaren Hajja ba sai da ya biya wajen Yawuro, sun gaisa har tana yi masa fadan tafiyar dare, murmushi kawai ya yi ya ce "to Yawuro na daina daga yau." "Gara dai a daina Allah ya yi albarka ya bada nasara." "Amin Yawuro." Yarima ya amsa yana fita, lokacin da ya shiga falon Hajja babu kowa sai Aliyu kanin Salmah yana zaune da wayar Salmah yana buga Game, yana ganin Yarima ya yi saurin tashi yana masa oyo-yo.
     "Yawwa Aliyu ina Hajja?" Yarima ya tambaya yana zama akan kujera. "Tana ciki yanzu ta shiga." "Ok Salmah fa?" "Itama tana ciki." Aliyu ya ba shi amsa yana mik'ewa.  Mika Yarima ya yi domin bai san ya gaji ba sai yanzu, yana nan zaune Hajja ta fito. Turus ta yi tana kallon Yarima don mamaki ya lullubeta "barka da warhaka Hajja." "Ashe kana hanya shi ne ka yi tafiyar yamma?" "Wallahi Hajja gani na yi na samu lokaci shi ne na taho." "Ai shi kenan amma a rika kiyaye wa." "Insha Allahu." Ya bata amsa cike da ladabi.
      Wucewa Hajja ta yi domin zata nufi ɓangaren Maimartaba, yana ganin ta wuce shima sai ya yi saurin shigewa bedroom don ya kosa ya ga Salmah
Sallama ya yi da muryarsa ta cikakken namiji, Salmah dake kwance ido lumshe kamar tana bacci ta amsa da kasalalliyar murya, ciki ya k'arasa tare da zama bakin gadon. "Barka  da zuwa Hamma." Salmah ta faɗa tana tashi zaune. "Yawwa Ummuna fatan na sameku lafiya?" "Lafiya lau shi ne ka yi tafiyar dare ko? Kuma kasan hanyar babu kyau." A shagwaɓe ta gama maganar. Jawota jikinsa ya yi yana gyara mata sumar da suka bazu a fuskarta ya ce "na daina Ummuna tun da baki so." Murmushi ta sakar masa tana zame jikinta daga nashi "Hamma mu je ka ci abinci nasan baka ci ba?" Tashi ya yi yana kare mata kallo don sai yaga ta canza masa take ya ji sha'awar ta ya saukar masa.

Vote me
Comment
& Shere on wattpad

Zulayheart Rano

KYAKKYAWAR ALAK'AWhere stories live. Discover now