Page 27

710 40 4
                                    

👉🏼💍 *KYAKKYAWAR ALAK'A*💍👈🏼

*REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S* _P.M.L_

                      ©
     *ZULAYHEART RANO*
*My wattpad username zulayheartrano89*

*STORY AYSHA WAZIRI*

*Yau dai na daure na yi maku typing, amma har ga Allah da na ce na daina typing Novel gaba daya, amma damun da wasu daga cikin masu son wannan labarin suka yi kadai ya sanya zan ci gaba, da yaddar Allah har na kammala.*

'''Ina alfahari da ku masoya a duk inda kuke.'''

           *27*

Shagulgula na suna sun kankama, domin kuwa yau saura kwana ɗaya suna, duk wani abin da za a yi a shagalin sunan, Yarima bai koma Bauchi ba don ya ce sai an yi suna tukun zai koma.

Ranar suna yarinya ta amsa suna *Hauwa'u* inda za su rika kiranta da *Khairat* sosai aka kashe kuɗi, su Salmah maijego an yi kyau tare da uban gayya, washegarin suna Yarima ya koma Bauchi domin yana da ayyuka da yawa a gabansa, ita kuwa Salmah ta ci gaba da shayar da yarta, kula suke samu kota wane ɓangare, tsakanin ta da Khairat sai idan nono aka kawo ta ta sha, amma ko da yaushe a bangaren Hajja take yi.

Sai muce Allah ya kara lafiya.

*****

Cikin sauri ya nufi office din domin, da kyar ya iya yake ce aikin ya fita, musamman da yake idan ya sake lokacin sallah yana iya wucewa, tun kafin ya gama sanya kansa ciki ya fara shaƙar sassayan kamshin turaren da ta yi amfani da shi, da niyyar yi mata walakanci ya ƙarasa shiga, amma sai me ji ya yi ba zai iya yi mata komai ba.

Sai ma lumshe ido ya yi tare da budesu, fes a kanta ta ci wani uban kwalliya, wanda ya yi matukar yi mata kyau, fuskar ɗauke da wani mayen murmushi mai saurin sace zuciyar cikakken namiji.

"Ya Allahu! Ya furta a zuciyarsa domin wani shu'umin kallo da take jefa masa.

Cikin takun nan nasa na cikakken namiji, ya isa kan kujerar sa tare da zama, hannu biyu ya sanya tare da shafe sumar kansa, (Ya zuwa wannan lokacin nasan da yawa sun fahimci wacece a office din Yarima Hafiz ko? Idan ma wasu basu san ko wacece ba to ba kowa bace illa *NUWAIRA*).

"Prince!" Ta furta da da wata murya mai cike da sanyi.

Yarima namijin duniya ne, duk da yadda yake jin son ta na fizgarsa amma sai ya dake, tare da shan mur kamar wanda bai taɓa sanin wani abu dariya ba, ganin baya da niyyar yi mata magana ne yasa ta kai hannu tare da matsar da tarin file da ke kan teburin gabansa, hannu biyu ta sanya tare da rankwafawa ta ce "Wai don Allah Prince me na yi maka ne? Dan nace ina sonka shi kenan kullum kai kenan cikin sanya zuciyata a azaba da radadi?" Ta dire maganar tare da zubowar hawaye.

"Oh sheet! Nuwaira menene abin yin kuka?" Ya yi tambayar bayan ya aje biron dake hannunsa, sannan kuma gaba daya ya maida hankali kanta.

Gani haka sai ta kuma fashewa da sabon kuka, ai ko tabbas tarkonta ya kama kurciya, don sosai hankalin Yarima ya tashi, jikinsa har yana rawa ya ce

"Please Nuwaira ki bar yin kuka, inda akan wannan maganar ne na yi maki alkawarin zuwa gidan ku anjima ina tashi daga office." Cikin muryar lallashi yake mata maganar.

Wani irin dadi ne ya kamata, lallai ta yadda da aikin mai Yanzu-yanzu, dubi yadda Prince ya ke mata a ranar yau, da kwanaki ne masifa da cin mutunci ne zai shiga tsakaninsu, amma yau sai wani lallashinta yake, ganin haka sai ta kara narke masa cikin zallar shagwaɓa.

"Prince nasan ba zuwa zaka yi ba, kawai dai so kake na bar maka office."

"Na taɓa yi maki irin wannan maganar?" Ya tambaya yana kallonta.

Girgiza kai ta yi.

"Ok! Tunda Ni nace ki je, to ki je din yau zan zo." Fuska babu alamar wasa ya yi maganar.

"To idan da gaske zaka zo me zan dafa maka?"

Tsadadden murmushi ya sakar mata ya ce "Duk abin da kika dafa min na yi alkawarin zan ci."

Gyada kai ta yi cikin gamsuwa da maganar sa, sannan ta yi masa sallama.

Bayan ta fita girgiza kai Yarima ya yi, haka kawai ya tsinci kansa cikin wani irin farin ciki mara misaltuwa, cikin zuciyarsa yana alla-alla anjima ta yi.

******

"Wai wannan rawan kan da kike ta yi yau kam lafiya?" Maman Nuwaira ta yi tambayar tana tsare ta da ido.

"Mama Prince Hafiz ne fa zai zo wanda nake baki labarin sa."

"Au shi yasa kike ta rawan jiki haka? To Allah ya kawo shi lafiya."

"Amin Mama yau zaki ga Prince." Cike da jin dadi Nuwaira ta gama maganar.

"Ai kuwa dai." Daga haka Hajiya Hadiza ta wuce ciki, inda ta bar Nuwaira tana shirye-shiryen tarbar Yarima.

Shi kam Yarima Karfe biyar na yamma ya kammala  shirinsa  cikin wata dakakkiyar shaddar sa mai kalar milk, jikinsa sai fitar da daddadar kamshin turare yake, kansa sanye da jar hula mai suna ( *ministar*) sosai ya yi kyau, ya fito a Fulanin asali. Hadaddiyar motarsa ya dauka wacce aka kawo masa ita ƙarshen watan daya gabata, yau ce ranar farko da ya fara fita da motar.

Har ya shiga motar zai tayar sai yaji kamar kar yaje, shi kansa yana cike da mamakin yadda lokaci guda ya ji yarinyar ta samu gurbi a zuciyarsa, sai dai tuni wata zuciyar ta gargade shi kan ba zata samu sukuni ba har sai ta kara yin arba da Nuwaira a yau.

Haka nan ya ja motar zuwa unguwar su, a bakin ya tsaya da motarsa tare da kiran lambar ta, bugu biyu ta ɗauka ya fara sanar masa da ga yi ya iso, ce masa ta yi ya yi hon maigida ya bude masa kofar.

Haka kuwa aka yi horn ya yi inda take maigida ya wangale masa kofa, a farfajiyar gidan ya yi parking sannan ya fito daga cikin motar tare da jingina, yana jiran fitowar Nuwaira.

Bai fi minti uku a tsaye ba Nuwaira ta karaso, cikin yauki da yanga "Barka da zuwa Prince."

"Barkammu dai yammata." Yarima ya fada yana tattaro dukkan wani farin cikin sa ya daura a fuskarsa. Don tunda ya shigo gida ya nemi farin ciki ya rasa, ta iya yiwuwa ko rashin farin cikin nasa yana da nasaba ne da text din da Salmah ta tura masa, wanda kafin ya bude motar sai da ya karanta.

Sako ne ta tura masa kamar haka

*Barka da warhaka Yarima Hafiz Angon Salmah, Baban Areef da Khairat, fatan ka yini cikin koshin lafiya? Domin kasancewar ka cikin lafiya shine nawa, a kullum ina mai yi maka addu'a Allah yasa karka mata da KYAKKYAWAR ALAK'AR dake tsakanin mu, don Allah Hamma bana son ka dubi wata diya mace da sunan soyayya, duk da ban ji a jikina Hamma zai iya yin haka ba, a karshe Khairat ta ce a fadawa Bobbo tana kewarsa. Ka huta lafiya daga Ummu Salmah matar Yarima Hafiz*

Lokacin da ya gama karanta text din ya tsinci kansa a damuwa, har ya yi dana sanin zuwanshi gidan su Nuwaira. Amma ganin isowar ta sai farin ciki ya saukar masa.

Jagora Nuwaira ta yi masa har falon baki dake cikin gidan, cikin lokaci kankani har an cika masa gaba da kayan motsa  baki, alkawarin da ya ɗaukar mata na cin abinci da ta yi masa ya cika, duk da dai bai wani ci da yawa ba.

Sun ɗan taba hira kafin Yarima ya mike, don tafiya bayan ya aje mata rafan yan dubu-dubu.

"To Nuwaira ko yanzu na cika alkawari, don haka zan koma gida." Yarima ya gama maganar yana mik'ewa tsaye.

"Kai Prince tun yanzu?" Ta tambaya kamar zata yi kuka.

"Eh! Saboda ina da ayyuka ne."

"To Please ka shiga ku gaisa da Mama."

"No! Ki bari dai idan na kara zuwa."

"Please Prince..." Da kyar ta sawo kansa har ya amince.

KYAKKYAWAR ALAK'AWhere stories live. Discover now