Page 7

1.3K 85 17
                                    

👉🏽💍 *KYAKKYAWAR ALAK'A* 💍👈🏽

                          ©
     *ZULAYHEART RANO*
*User name Zulayheartrano89*

*STORY AYSHA WAZIRI*

                     *07*

Numfashin Salmah har kusan daukewa ya yi, shi kam Yarima murmushi ya jefa mata sannan ya fita, kai tsaye bangaren Yawuro ya fara zuwa, da fara'a Yawuro ta tarbi Yarima "ina kwana Yawuro an tashi lafiya?" "Lafiya lau Magajin Sarki, tun ɗazun ina ta aiko maku abin break ana cewa baki tashi ba?" "Wallahi Yawuro mun tashi tun ɗazun bamu dai buɗe kofar ba ne, yanzu ma yunwa tasa ni fitowa." "Ai gara da ka fito ɗin ga komai can a dining yanzu za a kawo maku." "To Yawuro zan lek'a Hajja." Yana gama faɗin haka ya fita, da sakin fuska Hajja ta amsa tana faɗin "ya Salmatyy na? Me yasa baku fito tare ba?" "Kai Hajja kamar wacce ta yi shekara? Yanzu idan muka yi break zamu fito." Da fara'a Yarima ya yi maganar. "Eh! Ai dole na yi magana tun da aka haifi Salmah jiya ne muka raba kwana ai kaga dole na yi kewa." "Haka ne anjima zamu shigo, daga haka ya yi mata sallama.
   Yadda ya barta haka ya shigo ya sameta, sai kulolin dake gabanta kusan guda biyar "sannu da shigowa Hamma." Salmah ta yi maganar tana tashi zaune. "Yawwa Salmatyy amma fa bana son irin wannan tarbar a rika yi min irin ta yan gata." Yana magana ne yana matsawa inda take, kasa ta yi da kai jin yadda ya rungume ta "a rika yi min irin wannan." "To." Ta amsa tana niyyar zame jikinta daga nashi. "Menene haka kuma Ummuna?" "Hamma yunwa." A shagwaɓe ta yi maganar. "Oh! Sorry Ummuna bari na baki break, ya ida yana nufa wajen kululin, mamaki hana Salmah motsi ya yi domin har ga Allah bata kowowa ranta Yarima mai matukar ji da kansa zai iya sake fuska a gaban karamar yarinya kamar ta ba, musamman yadda kafin auren su ko kallon arziki bai taɓa yi mata ba, amma a ranar farko ta kasancewarsu matsayin miji da mata har ya sakar mata jiki fiye da tunaninta "ko dai Hamma yana sona ne?" Tambayar da zuciyarta ta jefa mata kenan. "No! Ta faɗa a fili wanda har Yarima sai da ya ji ya ce "lafiya kuwa Ummuna?" Girgiza kai ta yi har da ya mutsa fuska wai su a dole mata ta ce "mai ka gani Hamma? Babu komai fa." Murmushi ya yi ya ce "Ok sorry yanzu za ki koshi." Gama maganar ta yi daidai da aje plet da cup na kunun gyaɗa a gabanta, da kansa ya ciyar da ita sai da ta koshi sannan ya fara ci, ko da ya koshi da kansa ya kwashe kayan ya kai kicin, duk yadda taso ta taya shi ki ya yi, tana ganin ya shige bedroom ta mik'e kicin ta nufa wanke kayan da suka yi amfani da shi ta yi ta gyara kicin ɗin sannan ta fito, zaune ta samu Yarima yana faman danna wayarsa can nesa ta zauna kuma a kasa, zaro ido ya yi yana cewa "Ya kika zauna a kasa kuma nesa dani?" "Babu komai na fi son zaman kasa ne." Amsa ta ba shi tana wasa da zoben hannunta.
     "A'a dawo nan Ummuna daga yau inda ina gida kusa da Ni ne wajen zaman ki, domin bana son matata ta zauna nesa da ni." "To." Ta amsa tana gyaɗa kai. "Ba To bane amsar dana ke son ki bani ba fa, buɗe baki za ki ke yi min." "Zan rika buɗewa." A kunyace ta ke bashi amsa. "Yawwa dauko mayafinki zamu shiga gaida su Yawuro, Hajja sai tambayarki take yi. Mik'ewa ta yi cike da farin ciki, sai da suka shiga ɓangaren Yawuro suka gaisa, a can suka samu Baba Waziri faɗa sosai da nusiha ya yi wa Salmah da Yarima, sosai jikinsu ya yi sanyi har Yarima ya ji a cikin abubuwan da ya yi wa Salmah tanadi ya cire kashi ashirin da biyar, ya yi alkawarin zai kula da ita iyaka karfinsa, daga can sashin Maimartaba suka yi wa tsinke ya yi farin ciki da ganin Yarima da Salmah, albarka ya rika sanya masu shi ma sai da ya yi masu nusiha, ko da suka fito a sashin Hajja suka yada zango, sosai Hajja ta yi farin cikin ganin Salmah fadi take "Salmatyy ya kika kwana babu wata matsala dai ko?" "Lafiya lau Hajjata babu matsalar komai." "Haka nake son ji idan da matsala ki faɗa min kin ji karki ɓoye min komai." Murmushi ta yi har tana daura kanta saman kafadar Hajja ta ce "To Hajjata." Cike da shagwaɓa ta kai karshen maganar. Yarima dake zaune a gefe kallonsi kawai yake yi domin su burgeshi, ya yadda soyayyar Hajja da Salmah daga Allah ne "Salmah ki yi sallah sai na zo mu tafi." Yana maganar ne yana mik'ewa domin lokacin sallah ya gabato har an kira. "Hamma tun yanzu? Ka bari sai la'asar mana." Tana maganar ne kamar dai tana shirin yin kuka. "Abin da na ce kenan, idan ba haka ba daga yau kin bar shigowa cikin gidan nan." A fusace ya gama maganar tare da ficewa daga falon.
       "Kin ga Salmah ki rufawa kanki asiri da ni kaina, kin san halin Hamma naki amma kike son ɗauko mana Kano ba gammo, yi a hankali kuma karki rika musa masa akan abin da ya umurce ki matuk'ar ba saɓon Allah bane, tashi ki je ki yi sallah." "To." Ta amsa jiki a sanyaye, bedroom din Hajja ta shiga bayan ta idar da sallah kwanciya ta yi akan gadon Hajja har da lumshe ido ita a dole bacci take son yi. Yarima na shigowa ya ga babu Salmah a falo sai kawai ya shiga bedroom din don yasan tana ciki, can ya hangota ta takure tana son sa kanta bacci "Ke tashi mu tafi." A razane ta ɗago ganin Yarima sai ta narke fuska ta ce "Bacci nake ji Hamma." "Idan mun koma can sai ki yi." Turo baki ta yi tana niyyar tashi daga kwancen kafin ta gama zama har Yarima ya isa wajen, ita dai bata san yadda aka yi ba sai jin bakinsa cikin nata ta yi, iya firgici ta firgita shi kam ko a jikinsa ci gaba ya yi da tsotse bakin sai da ya yi minti biyar cur kafin ya barta, hawaye kawai ke sauka a kuncinta domin ta tsorata, Muryar Hamma Yarima ta ji yana faɗin "Duk ranar da na kara maki magana kika turo baki wannan shi ne hukuncin ki kuma ki fito yanzu mu tafi." Bai tsaya sauraronta ba ya fita falo, sosai Yarima ya ji haushin abin da Salmah ta yi masa, a kwana ɗaya kacal don bai nuna mata shi waye ba har take cewa zata zauna wajen Hajja, hmmmm! Ya sauke ajiyar zuciya a ransa ya kudiri yau ba sai gobe ba sai ya nuna mata ko shi wanene.
     Fitowa ta yi falon ta ɗan jingina da Hajja ta ce "Hajjata zamu tafi." "To Salmatyy Allah ya yi albarka." Hajja ta yi maganar tana rike goshin Salmah, addu'a ta yi mata sosai sannan suka tafi. A hanya babu wanda ya yi wa wani magana suna shiga suka taras har an aje masu kulolin abincin rana, Salmah wacewa bed ɗinta ta yi ba tare da ta tsaya a falo, bin ta da kallo Yarima ya yi har ta shige, girgiza kai ya yi a ransa yana mamakin halin Salmah.
    Bayan ta shiga ciki toilet ta fara zuwa sannan ta fito kwanciya ta yi, duk da yunwar da take ji a ganinta Yarima takurata yake son yi, shiru yana zaune a falo shi daya ya yi kusan minti goma a zaune Salmah bata fito ba, har zuwa bed ɗinsa ya yi ya canza kayan jikinsa amma babu Salmah don haka sai ya mike ya nufi bedroom can karshen gado ya ganta kwance ta takure kamar wata mai jin sanyi, buɗe ido ta yi domin tasan babu mai shigo mata bedroom sai shi, tana ganin shi ne sai ta rufe ido abinta, a hankali yake takawa har ya hau gadon bata bude ido ba, tallafo kanta ya yi ya aza a cinyar sa yana shafa sumar kanta cikin wani salo "Wai fushin me Ummuna take yi ne har bata son kallon mijinta?" Shiru ta yi bata tanka masa ba Kuma har lau bata bude ido ba. "Haba a yi min magana ki na ji sanyi Hamma dinki ne?" Bata san lokacin da ta turo baki ba ta ce "Hamm... sai jin saukar bakinsa kan nata, harshen ta ya kama cikin wani irin salo yake sarrafa ta.

Vote me
Comment
& Shere on wattpad

Zulayheart Rano

KYAKKYAWAR ALAK'AWhere stories live. Discover now