Page 28

734 44 19
                                    

👉🏼💍 _*KYAKKYAWAR ALAK'A*_ 💍👈🏼

*REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S* *_P.M.L_*

                      ©
     *ZULAYHEART RANO*
_*My wattpad username zulayheartrano89*_

*STORY AYSHA WAZIRI*

'''Congratuletion SAFIYYAH ABDULLAHI HUGUMA, ina ta ya ki murnan kammala littafin ki KUNDIN KADDARA mai cike da dimbin wa'azantarwa da ilimantarwa, gamu da zallar nishadi, ina jinjina gareki Allah ya ƙara basira da kafin ƙwaƙwalwa Ubangiji yasa ki fi haka Amin'''

                   *28*

Gaisuwa na mutunci suka yi da Umman Nuwaira, sannan ya yi mata sallama ya koma gida cike da farin ciki, kamar wanda aka yi wa bushara da aljanna.

Haka dai kwanaki ke tafiya, da sauyi kala daban daban, musamman ta bangaren soyayyar Yarima da Nuwaira, sun yi wata irin shakuwa da soyayya ta ban mamaki, sai dai duk da haka wani lokacin ya kan zauna ya yi ta tunanin canzawar alakarsa da Nuwaira, yarinyar da ada ya tsaneta fiye da komai amma yanzu ita ya fi so fiye da komai, hukuncin Allah kenan.

Ya ta kasance ranar Lahadi ce, kowa yasan ranar Lahadi babu aiki, bacci Yarima ya shaka, hankali kwance, bayan sun sha wayarsu shi da Nuwaira, karfe hudu ya tashi wanka ya fara yi kafin ya gabatar da sallar la'asar, shiryawa ya yi cikin shiga ta alfarma, kai tsaye gidan su Nuwaira ya nufa.

A babban falon gidan aka aje shi kamar koda yaushe, bayan ya cika ciki da abincin da Nuwaira ta dafa masa mai cike da kayan sundabaru, duk don Yarima ya kara sonta ne, hira suka shiga yi har Nuwaira ta gangaro kan batun da take son yi masa.

"Prince!" Ta yi maganar da wata irin murya.

Idanuwansa ya dago, don ya kasa amsawa, musamman yadda haruffan suka ratsa ko ina na gangan jikinsa, har sai da tsigar jikinsa ta tashi 'yarrr.

"Prince!! Ta sake ambato a karo na biyu.

"Na'am Nuwaira." Yarima ya amsa yana zura idonsa cikin nata.

Shiru ta yi kamar ba zata ce komai ba, don kallon da Yarima ke mata, ita kadai tasan ma'anan sa.

"Uhmm ina jinki mana."

"Dama cewa zan yi har yanzu ban ji ka fara maganar kana son haduwa da Abbana ba."

"Oh sorry! Karki damu ina ta son yi maki maganar Allah ne bai nufa ba, amma ki fada masa ina son turo iyayena."

Wani tsalle ta yi na tsananin farin ciki, ta ce "da gaske kake yi Prince?"

Gyada mata kai ya yi alamar tabbatarwa.

A haka suka ci gaba da hira, har karfe shida kafin ya yi mata sallama, ko a gida da ya koma tunanin maganar da suka yi da Nuwaira kawai ya ke, sai dai ya lura babban mafita shine ya sanar da iyayensa "Ka sanar da iyayenka?" Wata cikin zuciyarsa ta jefa masa tambayar. "Eh in sanar da su shi ne mafita" ya yi maganar a fili.

_*"Amma ya kake tunanin Ummu Salmah zata ɗauki maganar matukar ta ji?" Nan ma zuciyarsa ta kara jefa masa tambaya.*_

_*"Ya Salam!  Ya furta a bayyane musamman da ya tuna da Hajja, don tabbas gara Salmah sau dubu da Hajja, akan maganar nan tana iya yin fushi da shi.*_

*_"Kar ka wani damu, ai akwai Baba Waziri, idan kowa bai yadda ba tabbas yasan Baba Waziri zai yadda, domin KYAKKYAWAR ALAK'AR dake tsakanin su._*

Wani wani irin murmushi ya saki na jin dadi, shi yasa ya daura niyyar zuwa Ningi don ya sanar da da wannan magana.

To sai mu ce Allah ya taimaka ya sanya a dace Amin

******

Kamar yadda Yarima ya ce wa Nuwaira ta sanar da mahaifinta, bayan ta sanar masa sai ya bukaci ganin Yarima, babu bata lokaci Nuwaira ta sanar masa da kiran mahaifinta, babu bata lokaci Yarima ya isa gidan, sosai suka tattauna da Yarima kuma ya yadda da shi dari bisa dari, musamman da yasan adalin Sarkin Ningi.

Don haka take sai ya ji yana sha'awar hada zuri'a da shi. Sun tsayar da magana akan Yarima za shi gida don sanar da iyayensa.

********

Salmah dake zaune a falo tana shayar da Khairat nono, kamar a mafarki ta fara jiyo kamshin turaren Yarima, a hankali ta fara daga kanta domin sosai kamshin ke kara karade falon, duk da dai wata zuciyar tana gargadinta akan ba Yarima bane, domin bai taba yi mata irin wannan zuwan ba, sai dai kuma jikinta ya bata ana kallonta.

Cikin nutsuwa ta daga kanta dake duke, aiko karaf suka hada ido da shi, yana tsaye hannunsa zube cikin aljihun rigarsa, tsadadden murmushi kwance a fuskarsa, a hankali ya fara takowa har ya isa gabanta, bai ɗauke idonsa akanta ba.

Ita kanta Salmah murmushi ne kwance a fuskarta, musamman na ganin mijin nata ne fa, uban ƴaƴanta abin alfaharin ta, cikin sauri ta ce

"Hamma Barka da zuwa."

"Yawwa Ummuna." Ya amsa yana kai hannu don daukar Khairat.

"Wooo Hajjata ta girma Ummuna." Yarima ya yi magana yana rungumar yarinyar.

"Hmmmm Hamma kenan zuwa babu sanarwa, sannu da zuwa ya hanya?" Ta gama maganar tana tsiyaya masa ruwa mai sanyi a glass cup.

"Ki bari kawai Salmatyy haka nan yau na samu kaina da son zuwa ganin ki da Hajjata, ina Areef ne?"

"Aiko mun gode da wannan zuwa, Areef ai dama ba namu bane yana wajen su Hajja."

"Ok, Ummuna Please a zo a ragen zafi."

Salmah bata ce komai ba sai amsar Khairat ta yi, tana faɗin "bari na mikawa su Zaituna Khairat don na ji dadin kula da Abbanta."

Zama Yarima ya yi akan kujera, ita kam Salmah ko minti uku bata yi ba ta dawo, ruwan wanka ta haɗa masa, sannan ta fito tana cewa "Hamma ga can ruwan wanka."

"Anya kuwa Ummuna zan fara yin wankan nan tukun? Kamar sai na samu nutsuwa." Ya gama maganar yana kashe mata ido ɗaya.

Murmushi ta wanda ya karawa Yarima sha'awar ta, bata yi aune ba sai ji ta yi Yarima ya yi sama da ita, kissing dinta Yarima yake kota ina, haka itama Salmah ta shiga maidar masa da martani, sosai suka murji juna sai da suka gamsu sannan suka yi wanka, a tare suka koma falo inda Salmah ta shirya masa lafiyayyen abinci, sai bayan ya koshi kafin ya fita don gaida iyayensa.

Sai da ya gama zagaye gidan yana gaida iyayensa, falon Hajja ce karshe inda ya dade sosai, don a can Salmah ta sameshi, suna ta hira da Hajja Areef na jikinsa, karfe biyar na yi ya mike yana faɗin "Hajja bari na je wajen Baba Waziri."

"Dawo lafiya ka gaidashi."

"Zai ji." ya fada yana kama hannun Areef suka fita.

Gyarawa Khairat kwanciya Salmah ta yi suka ci gaba da hira da Hajja.

      *YARIMA A WAJEN BABA WAZIRI*

Bayan sun gaisa ne suka fara dan taba hira, irin ta uba da ɗa, suna cikin hiran ne Yarima ya gyara zama tare da ce "Baba dama akwai maganar da nake so mu yi ne."

"Ina jinka Yarima." Baba Waziri ya fada ya yin da ya maida hankali sosai akan Yarima.

"Uhmm dama dai akan maganar ina son kara aure me." Yarima ya fada kamar mai ciwon baki, yana tsoron irin tarbar da Baba Waziri zai wa maganar.

Fadada fara'arsa baba Waziri ya yi ya ce "Kai madallah! A ina take?"

"Eh dama a can take Bauchi, mun fara magana ne da babanta shi ne ya ce na turo magabata."

"Wannan abu ya yi kyau, Allah ya tabbatar da alhairi, idan Allah ya so gobe zamu tafi Bauchi don nema maka aurenta."

Godiya sosai Yarima yake zubawa Baba Waziri, don tsananin dadin da ya ji, Yarima bai bar wajen ba sai da aka fara kiran sallar magriba.

*******

Kamar a mafarki Salmah ta fara jin maganganun da Maimartaba ke yi da Baba Waziri, wani irin faduwar gaba ne ya ziyarce ta, da sauri ta kai hannu ta dafe kirjinta dake barazanar tarwatsewa, da wata irin murya ta furta "Ya Allahu."

Da kyar ta iya daga kafarta wanda suka mata matukar nauyi, hawaye kam tuni suka fara wanke mata fuska "Hamma..." Ta furta da wahalalliyar murya.

Aradu na gaji, mu hadu gobe.

Yar mutan Rano.

KYAKKYAWAR ALAK'AWhere stories live. Discover now