Page 20

974 43 0
                                    

👉🏽💍 KYAKKYAWAR ALAK'A 💍👈🏽

                         ©
     *ZULAYHEART RANO*
*Wattpad username zulayheartrano89*

*STORY AYSHA WAZIRI*

Ina mika godiya ta gareku masoya wannan buk ɗin, Allah ya barmu tare da juna har karshen rayuwa.

                    *20*

"Hello kana jina kuwa?" Hajja ta tambaya. Dan daburcewa Yarima ya yi don ya ma manta waya yake da Hajja, ai da sauri ya amsa da "Eh! Hajja ina jinki, insha Allah goben zamu taho." "Allah ya kawo ku lafiya." Hajja ta fada sannan suka yi sallama. Salmah dake sauraron sa ta gyara kwanciya bata ce komai ba. "Wai hala Ummuna baki ji abin da Hajja ta ce ba?" "Uhmm ban ji ba Hamma, me Hajjar ta ce?" Kumatunta ya shafo fuska dauke da murmushi ya ce "Ummuna kenan kin iya basarwa fa nasan sarai kinji abin da Hajja ta ce amma yanzu kin ce baki ji ba."
    "Ni fa ban ji ba Hamma." Ta yi maganar tana bata fuska. "Na yadda to cewa ta yi gobe mu tafi Ningi wai a can zaki haihu." Da sauri ta tashi tare da zama da zallar farin ciki ta ce "Hamma gobe zamu je gida? Kai Allah na gode maka, zan ga Hajja da su Yawuro." Hade girar sama da ta kasa Yarima ya yi don ganin yadda take ɗoki, duk sai ya ji babu dadi wato tana farin cikin barinsa, don haka sai ya ce "Ummuna kamar baki sona." Ya yi furucin a ɗan zafafe, zaro ido Salmah ta yi a ruɗe ta ce "Me ya faru Hamma? Me na yi maka?" Ta gama tana tsare shi da ido.
     Harara ya aika mata ya ce "Ban ga kin nuna kin damu da rabamu da Hajja zata yi ba, sai ma wani jin dadi kike yi!" "Oh! Sorry Hamma! Amma ai kasan dole zan damu, don na saba da kai kusa da ni, sai dai wannan tafiya ta zama dole ko na damu ko ma dai kar na damu sai na je, ka yi hakuri kwana kusa ne zan dawo, kuma ai zaka rika kai muna ziyara." Hmmmm! Ya saki ajiyar zuciya, ya gamsu da bayanan Salmah don haka sai ya ɗan saki murmushi "Bari na sanar da su Zaituna su fara shiri." Salmah ta fada tana sauka daga gadon. "To." Yarima ya amsa yana sauka shi ma, suna tafe suna dan hirar su har suka isa bangaren, sosai suka yi farin ciki da jin zasu je gida, su Salmah na fita suka fara hada kayan su.
    "Hamma kawo na taya ka." Salmah ta fada tana jawo doguwar rigarta. "A'a zauna ki huta, zan iya ma." "To." Ta amsa tare da kwanciya tana kallo yana hada kayan, tana kara nuna masa abin da zata yi amfani da shi, shi kuma yana sanyawa cikin akwati bai kammala ba sai karfe goma, a lokacin tuni bacci ya fara ɗaukar Salmah, tsaf ya shirya kayan sannan ya dawo kusa da ita ya zauna yana kallon yadda take sauke numfashi a hankali, soyayyar ta tana kara ratsa zuciyarsa baya kaunar ko na sakan daya su rabu da Salmah, a duniya bai taba san wata diya mace haka ba, girgiza kai ya yi ganin dare na kara yi sai ya kwanta tare da kashe wutar dakin ya rungumeta, a haka bacci ya kwashe shi.
    *********  ********  ********** *****
    Washegari basu fita gida ba sai sha daya na safiya, karfe ɗaya suka isa garin Ningi, sai dai me? Mota na yin parking Salmah ta ce sam bata san wannan ba, a rikice Yarima ya dubeta yana tambayarta, da shashsheka ta ce "Hamma haka zan shiga gida?" "Me ya faru?" Ya yi tambayar cikin  matsuwa da son jin amsa. "Hamma kalli cikin jikina fa?" Ta gama maganar hawaye suna saukowa. Kallon cikin Yarima ya yi sannan ya kalleta ya ce "Ban ga komai ba Ummuna." Kuka ta kara fashewa da shi ta ce "Ka dubi yadda ya yi girma fa shi kenan kowa yasan abinda aka yi aka same shi?" Dariya ce taso kwace wa Yarima don sosai maganar ta ta bashi dariya, sai dai yasan yana yi zata kara kwaɓe masa don haka sai ya kunshe bakinsa ya ce "Yanzu ya kike so a yi?" "Kawai mu fasa shiga ciki mu koma, gaskiya Ni dai ina jin kunyar Hajja da su Yawuro." Wannan karon kasa ɓoye dariyar ya yi sai da ya dara, don sosai sakarcinta ya bashi dariya, sai da ta gama murna zata ga su Hajja amma yanzu tazo da wata rigima, maganar ta ce ta dawo dashi cikin hayyacinsa. "Au dariya ma kake yi?" Ta yi tambayar tana kara hassala.
    "Yi hakuri bari mu koma sai a fadawa Hajja kina kunyar ganinta." Ya gama maganar yana kunna motar. Da sauri ta riko hannunsa tana fadin "Mu shiga ciki amma ka dauko min hijjab don Allah." "Hijjab kuma? Kin manta suna cikin kaya?" "Eh nasan yana ciki kawai dai shi zan sanya." Bai ce komai ba sai da ya bude kofar motar sannan ya ce "Ni kam na shiga ciki don naga abin naki ba zai kare ba sai kin shigo." Yana gama fadin haka ya fita, bai ko tsaya jiranta ba ya wuce, shiru ta yi bata da zaɓi da ya wuce ta fita domin tasan kowa jiran fitowar ta yake jira. Haka ta fita daga motar tana kakkauda kai gefe. Babu kowa a harabar don haka da  sauri ta shiga ɓangaren Hajja aiko tana yin sallama su Aliyu suka rugo da gudu suka rungumeta suna yi mata oyo-yo tsawa Yarima ya yi masu don yaga suna shirin kayarta kasa.
    Farin ciki ya rufeta har ma ta manta da wani kunya, kar kuso kuga farin ciki wajen Hajja musamman yadda taga Salmah ta yi wani kyau ta canza kamar ba salmarta ba, hannunta Hajja ta rike ta shigarta cikin falon inda aka shirya masu abincin tarbar, sai nan-nan Hajja ke yida Salmah, ita kuma ta kasa sakin jiki don yau kunyar Hajja take yi, sai da suka huta suka ci abinci sannan suka nufi gaida iyayen, Yawuro da Baba Waziri sun yi farin ciki su ma da ganin Salmah, ita kam sai wani nok'ewa take wai kar su ga cikin jikinta don kunya take ji sosai, sun dade suna hira da Yawuro har da Aliyu sannan suka yi sallama, ko da suka fita bangaren Maimartaba suka yada zango, can suka samu Hamma ɗan waziri, bayan sun gaida Maimartaba suka shiga hira sosai Salmah taga soyayya wajen yan'uwanta, domin kafin su bar wajen Maimartaba har su Adda Khadijah sun iso, tana shiga suka fara yi mata sannu.
    Murmushi kawai take yi masu tana amsawa a hankali, don ta gane nufinsu bata tsaya a falon ba sai ta wuce bedroom don ta gaji hutu take son yi, bata kwanta ba sai da ta yi wanka tare da yin alwala, sallar azahar ta gabatar da la'asar don an kira. Tana kwanciya Hajja ta shigo ta ce ta tashi babu kyau baccin yamma, haka nan badan ta so ba ta tashi hira suke yi da Hajja cikin hikima da basira Hajja ke tambayar Salmah yanayin zamansu da Yarima a Bauchi, tana bata amsa a haka har ta nemi bacci ta rasa, suna hirar har  aka kira magrib basu fita ba sai da suka gabatar da sallar,  zaune suka samu Yarima suna hira da Hamma ɗan waziri, sai da suka gaisa sannan Hamma ɗan waziri ya yi sallama ya fita, dama Hajja bata tsaya ba Yarima da Salmah ne kawai suka rage a falon, dauke kai ta yi don tana jin haushin sa har yanzu, tashi ya yi daga wajen da yake zaune ya isa inda take zama ya yi tare da yin kasa da murya
         "Wai Ummuna ina kunyar da ake ikirari naga yanzu tare kuka fito da Hajja?" Banza ta yi masa, dariya ya yi mai sauti sannan ya kawo mata abinci "oya gyara zan ciyar da babyna ke kam naga kin koshi." Harara ta doka masa ta kauda kai gefe. "Zaki bude ko kuwa?" Ganin ya yi tambayar babu wasa yasa ta bude ya fara bata bai barta ba sai da ta koshi, ruwa ya bata sannan ya ce "Tashi mu je." Daidai da shigowar Hajja sai ko ta ce "Ina zaku je?"  Sosa Kai ya yi ya ce "dama dai gani na yi dare ya yi shi ne zamu kwanta." Harara Hajja ta jefa masa ta ce "Allah ya bamu Alhairi ai Salmatyy kuma ta dawo nan, ke wuce mu je." Shigewa suka yi suka barshi nan tsaye, haka ya ja kafa ya wuce.
    Da safe Yarima  bai fito ba sai da ya shirya don yau zai koma, fita ya yi ya nufi bangaren Hajja ko da ya yi sallama bai ji an amsa ba sai ya shige bedroom, can ya ga Salmah kwance da sauri ya karasa tare da rungumeta har yana sakin ajiyar zuciya, Salmah wacce ta koma ta kwanta bayan ta gama break a razane ta ɗago, ganin Yarima ne sai ta kara shigewa jikinsa "Ummuna na gama shiryawa fa." "Yau zaka tafi ne Hamma?" Ta tambaya tana lumshe ido. "Eh! Kin san na bar tarin ayyuka a office shi yasa zan koma." "Allah ya tsare ya kaika lafiya." "Au shi kenan sallamar da zamu yi dake?" Bude ido ta yi tana kallonsa ta ce "Wacce irin sallama zamu yi kuma?" "Mu je bangarenmu ki ga irin ta nan Hajja tana nan." Ya gama maganar yana kashe mata ido daya. Murmushi ta yi don ta gano nufinsa, ganin haka sai ya kara matseta a hankali yake matsawa da fuskarsa har ya isa bakinta, sosai ya ke yamutsa ta sai da ya gamsu kafin ya barta, sai da ya sauka daga gadon kafin ya ce "Zan tafi Salmah." Da kyar ta iya cewa "Allah ya kiyaye hanya." Sai da ya fita suka hadu da Hajja addu'a ta yi masa da fatan Alhairi sannan ya wuce cike da kewar Salmah.

    *******  ********** ******* *****
Kwanci tashi asarar mai rai yau dai ga cikin Salmah ya shiga wata na tara, ko da yaushe haihuwa tana iya zuwa, duk wani shirin haihuwa an tanadar ita kadai ake jira, ranar wata Alhamis ne Salmah ta tashi da nakuda tun safe, sai dai bata bari an gane tana nakuda ba, don ta iya dauriya sai dai idan abin ya zo gadan-gadan ta fara ambaton Allah, da rana Hajja ta lura da halin da take ciki "lafiya kuwa Salmatyy?" Hajja ta tambaya "Lafiya lau Hajjata me kika gani?" "Naga sai uban zufa kike yi ne?" "Ba komai kawai dai zafi nake ji." Salmah ta bata amsa. Gyada kai kawai Hajja ta yi ba dan ta gamsu ba, sai dai tun da ta ce haka sai Hajja ta barta, amma tana lura da duk wani motsinta a haka har dare ya yi, a lokacin ne fa abu ya tsananta zama ya gagari Salmah sai kai komo, ganin haka sai Hajja ta kira jakadiya suka duk'ufa kanta, duk wani abu an yi amma abin ya gagara har karfe sha biyu shiru, kuma faya ta fashe wahala sosai Salmah ke sha, amma da yake mai hakuri ce sai sunan Allah kawai take ambata da yada kai gefe
   To fa abin ya neman gagararsu don har gari ya waye Salmah bata haihu ba, don haka ne aka kira babban likita don asan abin yi, bangaren Yarima tun jiya yake jin kewar gida sai dai aiki sun sha masa kai, don a kwanakin nan baya samun  dawowa gida sai bayan magriba yana sallar ishsha yake kwanciya, to yau ma da safe har ya yi shirin office ya ji bai zai iya zuwa ba Salmah kawai yake son gani don sai ya ji kamar ba bu lafiya a can, don haka bai ko tsaya yin break ba ya dau hanyar Ningi. Mahaukacin gudu Yarima yake bai bata lokaci ba ya isa gida, bangaren Hajja ya shiga burinsa ya yi arba da Salmah, sai dai me tun kafin ya gama shiga falon kunnensa suka fara jiyo masa wasu maganganu da suka tayar da hankalinsa ai da sauri ya shige falon.

Vote me
Shere
& Comment on wattpad

Zulayheart Rano

KYAKKYAWAR ALAK'AWhere stories live. Discover now