35

199 15 5
                                    


KYAKKYAWAR ALAƘAR
  © ZULAYHEARTRANO89

STORY AYSHA WAZIRI

Bangaren Salmah kuwa tana shiga cikin falo kuka ta saki mai tsuma zuciya, tana tausayin kanta tana kuma tausayawa Yarima domin kuwa ta fara fahimtar duk abin da yake mata ba fa yin kansa ba ne, saboda ta san matukar Yarima na cikin hankalinsa ko giyar wake ya sha ba zai taɓa iya yi mata irin wannan wulakancin ba.
   Turo ƙofa aka yi wanda ya sanya ta yi saurin dagowa a tunaninta Yarima ne, amma sai idanuwanta ya sauka a kan Zaituna wacce ta shigo fuskarta babu walwala. Da sauri Salmah ta sanya hannu ta share hawayen dake fuskarta tana faɗin “Zaituna lafiya?” Salmah ta faɗa cikin kulawa  “Lafiya lau uwardakina.”
  “Na ga fuskarki da damuwa?”
“Damuwarki ta sanyani damuwa, duk abin da zai ɓata ranki nima shi yake ɓata nawa, haka abin da yake faranta maki shi yake faranta mini.”
  “Toh! Sannu da kulawa Zaituna, amma fa ni bana cikin damuwa, don haka bai kamata kema ki shiga ba.” Salmah ta faɗa tana nemo farin ciki ta daura a kan fuskarta, don ba ta son Zaituna ta fahimci tana cikin matsala, matsalar ma kuma da Yarima.
  “Shi kenan uwardakina yanzu ya maganar siyo masarar?”
  “A je a sayo mana, ai na ce maki raina ya biya ga Khairat ku tafi ni zan shiga toilet.” To Zaituna ta amsa sannan ta amshi Khairat ɗin su ka fita.
  *****
Su Yarima sun sauka Cairo cikin ƙoshin lafiya, sun kuma fara gudanar da hutun su kamar yadda suka zo yi. Nuwaira dai ta samu nasarar raba Yarima da kowa na shi, ita kadai ke sarrafa shi.
   Kamar yanzu da Nuwaira ke zaune Yarima kuwa ya fita, hasalima ba ta san wajen da ya nufa ba, jikinta babu komai sai pant waya take yi hankali kwance “Wato Rauda ba zan ɓoye maki ba, prince ya zama nawa ni ɗaya sai yadda naga dama nake yi da shi, komai zai yi sai ya tambayi izini na.” Wata mahaukaciyar dariya Rauda ta fashe da shi ta ce “Dama ai kin san mai yanzu-yanzu ya faɗa maki hakan za ta faru, don haka sai ki dage ki ƙara himma don ki kuma mallake shi.”
  “Muguwa yanzu duk wannan mallakar da na yi masa sai na ƙara masa wani? Ni fa yarinyar can har ta fara bani tausayi wallahi.”
  “Tausayi? Wanne irin tausayi kuma? To shi kenan ki tsaya tausayi karki yi abin da ya kamata sai shirinmu ya warware.”
  “A haba dai dagewa zan yi sosai, zan ma turo maki wasu kudi a ƙarawa mai yanzu-yanzu, kema zan aiko maki da na ki don ki yi wasu bukatocin.”
  “Na gode sosai Ningi Princess.”
“Sakamakon wannan kirarin kin samu ƙarin wasu kuɗin, duk da ban taɓa zuwa gidan sarautar ba amma ina son Sarauta sosai.”
  “Kwantar da hankalinki kamar kin shiga kin gama, ke da kike auren Yarima guda wanda wata rana shi ne zai maye gurbin sarautar, kin ga a lokacin kin gama zama sarauniya.”
  “Hmmm! Rauda kenan ni gaba ɗaya yan gidan haushi suke bani, don ba su da mutunci sai mugun girman kai, kalli fa wancan halittar ta Prince magana ma sai mutum ya wahala take yi ma, kin mata shi ma da haka yake? Kuma kin san duk a wajen wa suka yi gado?” Nuwaira ta tambaya kamar Rauda tana gabanta.
  “Wajen uwar su kai matar nan tana da jin kai duk da ban taɓa ganinta ba, amma ai Yarima yana bani labarin ta ga shi ko kaɗan aikinmu ya ki yin tasiri a kanta, a yanzu haka kafin na sa a rabasu ko waya suke suna zaune kusa dani bana jin me take cewa, kuma har su gama ba za ki ji ta tambayeni ba na rasa irin kiyayyar da take yi mini.”
  “Barta za mu yi maganinta ne, sai ta so ki dolenta ma.” Nuwaira ta buɗe baki da niyyar magana ta ji ana ƙwanƙwasa ƙofa, ta san ba kowa bane sai Yarima don haka ta yi sallama da Rauda.
Da sauri ta rungume Yarima tana aika masa da wasu lafiyayyun kiss, wanda nan take jikin Yarima ya amshi sakon Nuwaira musamman da jikin nata damar abu kaya, don haka shi ma da zafi-zafi ya soma bata kalar tashi, sosai suka dage har sai da suka gamsar da junansu.
**********
Haka rayuwar Salmah ta kasance a gida na rashin walwala, musamman idan sun rabu da Zaituna, don idan har suna tare bata nuna wani damuwa, amma da zarar sun rabu shi kenan za ta afka cikin tunani da damuwa, addu'a kam kullum cikin yinta take tana miƙa kukanta ga Allah a kan ya karkaro mata da hankalin Yarima kanta.
Tana lissafe yau satin su Yarima uku a tafiyar da suka yi, a sati ukun nan da suka yi ba su taɓa waya ba ko text message ba, hasalima ita ta manta lokacin da suka yi waya da Yarima, shi din ba ya kiranta ita kuma ko ta kira shi ba ya shiga.
  Ƙarar wayarta ya katse mata tunanin da take yi, lambar Hamma Ɗan Waziri ta gani don haka da sauri ta ɗauki wayar tare da karawa a kunne tana faɗin “Assalamu alaikum.”
  “Wa'alaikumus Salam!” Hamma Ɗan Waziri ya amsa. Sannan Salmah ta fara gaisar da shi cikin ladabi, har tana tambayarsa littel Salmah. “Duk lafiyar mu lau, dama dai kira na yi mu gaisa, kuma ina ta kiran Yarima bana samunsa har yanzu ba su dawo bane?”
  “Eh! Hamma ba su dawo ba, amma ina tunanin kila yau za su dawo.”
“Toh shi kenan Allah Ya dawo da su lafiya.”
Amin suka amsa a tare sannan suka shiga hirar su irin ta yan'uwa masu tsananin son junansu. A cikin hirar ta su ne Hamma Ɗan Waziri ya ke ƙara yi wa Salmah nusiha ciki hikima a kan irin zaman da take yi, duk da shi din bai san halin da take ciki ba amma yana dai ƙara jan hankalinta. Sosai kuma nusihar ta shiga kunnen Salmah, ta ƙara jin za ta cigaba da riƙe sirrinta har zuwa lokacin da Yarima zai dawo cikin hayyacinsa.
  ****
Kai wa da komowa kawai Salmah ke yi, gidan gabadaya ya kaure da kamshin girkin da take yi don kuwa yau gidan zai amshi baƙuncin manya yayyi wato Adda Khadijah da Adda Hafsah. Ƙarfe goma sha ɗaya ta kammala girke-girken da taimakon Zaituna, har gidan sun gyara shi fes sai kamshi ke tashi.
  Wanka Salmah ta yi ta shirya cikin doguwar rigar atamfa, wanda ya yi mata kyau ta kuma karbi jikinta, sosai ta yi kyau sai dai ta faɗa ta kuma yi duhu. Haka ta shirya Khairat cikin doguwar riga yar kanti, yarinyar da tuni ta fara takawa abin ta.
  Ƙarfe sha biyu su Adda Khadijah suka iso, farin ciki sosai ya kama Salmah da ganinsu. Cikin farin ciki suka ci suka sha sai su ka shiga hira, har aka kira yi sallah bayan sun yi sallah suka cigaba da hirar su.
Bayan magriba suna zaune suna hira bayan sun ci abinci Adda Hafsah ta kalli Ummu Salmah sannan ta fara magana, domin tun da suka shigo ta fahimci yanayi mara daɗi ga Salmar.
  “Wai Ummu Salmah ciwo kika yi ne?”
  “Lah! Adda baki san na yi rashin lafiya ba?” Salmah ta yi saurin ba ta amsa, a niyyar ta waskewa maganar su, yana daga cikin abin da ya ke hanata zuwa Ningi, don ta san dole ne Hajja ta tasa ta a gaba da kwatankwacin wannan tambayoyin, ita kuma ba ta shirya sanar da kowa halin da take ciki ba.
  “Ciwo Salmah? Yaushe kika yi ciwo ba wanda ya sani? Don ko da Hajja ta sani za ta sanar mana.” Ta ƙara jefa mata tambaya tana tsare ta da ido.
  “Eh! Adda ai ban faɗawa kowa ba, bana son hankalin kowa ya tashi ne kuma ai Alhamdulillah! Na samu sauƙi sosai.” Salmah ta faɗa tana ɗaukar Khairat wacce ke barci za ta kaita bedroom.
  Inkiyar da Adda Khadijah ta yi mata ne ya sanya ta ce “Ai shi kenan Allah Ya ƙara sauƙi, amma ki bar yin haka, idan ba ki da lafiya ki riƙa sanarwa.”
Toh ta amsa tana nufa bedroom.
“Haba Hafsah ke ma kin san dai Salmah ba za ta taɓa faɗa maki damuwarta ba, kowa ya kalli Salmah zai shaida tana cikin damuwa ki duba fa tun da muka zo ƙarfe goma sha daya har zuwa yanzu ban ga sun yi waya da Hamma Yarima ba, tun a nan za ki fahimci babu lafiya Hamma da kullum yake nanike da ita amma yau a ce sun yini zungur har yanzu babu waya? Ni dama tun asali ban so Hamma yin aure ba amma Baba Waziri ya goya masa baya, ai ga irinta nan yanzu ina KYAKKYAWAR ALAƘAR da Hajja take tunanin suna ciki?” Cikin ɓacin rai ta dire maganar.
  “Haka ne kam! Nima na lura da hakan ne kuma ko jiya mun yi magana da Hajja a kan wannan lamarin, don ita ma ta ce tun da ya yi aure bai fi sau biyar suka yi waya ba, ta ma ce yanzu ba za ta iya cewa ga ranar ƙarshe da suka yi waya da shi ba, ko ta kira ba ta samunsa amma idan ta kira Salmah ce mata take wayar ce ta lalace, duk ta toshe hanyar da za a bi domin a fahimci halin da take ciki, shi ya sa ta karfafa mana gwiwar zuwa mu ga halin da ake ciki.”
“To ai shi kenan mu zuba ido mu gani, amma ina matuƙar tausayawa yarinyar, ko mu da muka girme mata bama cikin wannan halin sai ita.”
“Haka ne kin san waman ƙaddarallahu hakkal'kadarihi, ita wannan shi ne na ta ƙaddarar Allah Ya ba ta ikon cinyewa.” Amin suka amsa a tare, a haka Salmah ta dawo suka cigaba.
Sai ƙarfe goma suka bar falon.

KYAKKYAWAR ALAK'AWhere stories live. Discover now