40

345 16 4
                                    

KYAKKYAWAR ALAƘA.
STORY AYSHA WAZIRI

WRITERS ZULAYHEATRANO89

Jiki babu lakka ya juya, ko da ya shiga a kujeran falo ya zube, kansa na wuni irin sarawa “Me yake faruwa dani ne? Me na yi wa Salmah har Hajja da kanta ta zo ta ɗauke ta?” Ya yi tambayar a fili yana kai hannu saman kansa. Sai yanzu ma ya fara tunanin wanne dalili ne ya sanya shi auren Nuwaira to wai m ta ya aka yi har ya aureta ne? Shi fa ba zai iya cewa ga dalilin da ya aureta ba. Kala mata kira ya soma da ƙarfi “Nuwaira! Nuwaira?” Wai a son ta zo ta bashi amsar tambayoyinsa. Shiru ya ji bata amsa ba, ya ji mamaki da ya leƙa dakinta bai ganta ba, haka kuma ya shiga na shi dakin bata ciki, to yaushe ta fita? Ya yi tambayar a kasan zuciyarsa don shi ya san a cikin bedroom ɗinta ya barta.
  Falon dai ya kuma komawa yana dubata, wani abu mai sanyi ya ji a watsa masa a fuska da sauri ya waiwaya don gani waye idansa ya haɗu dana Ɗan Waziri da Malam Liman, Malam Liman bai yi ƙasa a gwuiwa ba ya kara kwara masa ruwan maganin nan yana cigaba da tofa masa addu'a, wani yunƙurin mai da Yarima ya yi da sauri suka ƙarasa Hamma Ɗan Waziri ya riƙe shi, sosai yake kwara amai kamar zai amayar da yan hajinsa, yana ganawa wani barci mai nauyi ya kwashe shi, gyara masa kwanciya suka yi suka nufi aiwatar da abin da ya kawo su, dama sun shirya haka don aikin sati hudu aka yi wa Yarima kuma Alhamdulillah an samu nasara, tun jiya su ke garin Bauchi don yau Malam Liman da kansa zai zo ya fitar da binne-binnen da aka yi a cikin gidan. Kuma sun zo da maganin da za su ba Yarima ya sha wanda zai karya sihirin dake jikansa, shi yasa suka baro hotel ɗin da suka sauka tun safe. Sai kuma ga shi sun samu nasarar yin komai cikin lalama, kaf abin da aka binne sai da suka hake, haka na cikin ɗakunan da na ko ina sai da suka cire shi waje guda suka tara suka banka masa wuta. Sannan suka koma wajen Yarima dake barci har a lokacin Malam Liman ya cigaba da addu'a.
    *******
    Ita kam Nuwaira ta fice tun lokacin da Yarima ke buga kofar Salmah, don sun riga da sun gama tsara wajen wanda za su je ita da Rauda. Tana fita hankali tashe suka nufi wajen boka na kan tsauni hankali tashe, da ƙyar ma suka hau kan tsaunin da bokan yake bayan sun gama baje masa damuwarsu sai bokan ya babbake da dariya ya fara magana “Kun zo a daidai domin kuwa aljanin da zai yi maku aiki yana kusa.”
    “Mun gode sosai, boka yanzu nawa za mu biyaka?”
    “Ba kuɗi za ki biya ba, amfani za mu yi dake a maimakon kuɗin aiki.” Da farko Nuwaira ta ji tsoro don ba ta saba irin haka ba, ta dai saba bayar da kuɗi a yi mata aiki amma yanzu wannan kazamin ne za ta haɗa jiki da shi? Ita sai yanzu ma ta lura da shigar dake jikansa, gabaɗaya kayan a yayyage wani irin wari da ƙarni kawai ke fita daga jikinsa, suke bakinsa da haƙoransa sun dafe sun yi baƙinƙirin. “Ina gaskiya ba zan iya ba.” Ta faɗa tana miƙewa.
    “Yarinya matuƙar kina son aikin ki ya ci sai kin yarda an yi wannan abu da na ce maki.
    “A'a bana so.” Ta faɗa tana ja baya.
    “Nuwaira? Kina son ki rasa Prince ɗinki? Ashe dama ba sonsa kike yi ba?”
     “A'a Rauda ina sonsa kuma bana son rabuwa da shi, amma haka dai a'a.”
    “To idan kina son prince sai kin yarda, kuma ai na lokaci kadan ne nima nan haka duk gayun da kike gani sau nawa ina ba shi kaina? Kawai Malama ki yarda, kin manta ɗazun kika gama faɗa min aiki ya warware hankali a tashe? To ki yarda a yi maki sabon aiki da ya fi wancan.” Haka Rauda tai ta ribatanta har ta yarda ta amince, amma fa yana sarara mata ta rika kwara amai kamar zata amayar da hanjinta, wani bakin ruwa kawai ya ba ta a cikin ƙwarya ya ce ta shiga ta san yadda za ta yi ta zuba wa Yarima a jiki duk abin da take so Yarima ya zama zai zama amma ta kula da ruwan kar ta bari wani abu ya same shi, idan kuwa har wani abu ya same shi to za ta haukace.
    Shi ya sa ta yi masa kyakkyawan riko, ranta fal murna suka baro wajen, da yake a motar Rauda suka fita har kofar gida ta kawota sannan ta wuce, sai da ta ajiye ƙwaryar ruwan sannan ta ƙwanƙwasa ƙofa, ta daɗe tana ƙwanƙwasa ƙofa kafin suka zo suka buɗe mata, aiko ta fara yayyafa ruwan masifa har da cewa yau za ta sanya Yarima ya koresu.
    Cikin rashin sa'a tana masifa sosai idonta ya rufe ba ta ma kula da zuwan Ɗan Waziri ba sai ji ta yi ya buge ƙwaryar ta faɗi ƙasa ta tarwatse, wani razanannen ƙara da ta saki shi ya yi sanadiyar farkawar Yarima daga barcin da yake yi da sunan Salmah a bakinsa ya farka
    Take Nuwaira ta fara wasu irin surkulle na hauka tuburan “A wallahi ba zai yiwu ba, ai boka ya ce idan na zubawa Yarima wannan ruwan sai yadda na yi da shi don haka sai ka biyani abuna, ba ka san ni na raba shi da wannan matar tasa ba? Kuma ni na raba shi da wannan Uwar ta shi tun da ba tasona, Kai Ni ce ma na raba shi da kowa na shi.” Ta gama maganar tana sakin mahaukacin dariya. Ganin haka ai da gudu Ɗan Waziri ya ruga cikin daki da gudu, ita ma kuwa ta bishi ciki tana maimaita maganar da ta faɗa masa a waje, sosai Yarima ya cika da mamakin jin furucinta, babu abin da ya fi ba shi takaici irin yadda take cewa ta raba shi da iyayen shi, ai kuwa cikin zafin nama ya shakota ya fara zuba mata duka, daga Ɗan Waziri har Malam Liman babu wanda ya hana Yarima dukanta, sai dai da ya yi mata lilis sannan ya kyaleta kuma har a lokacin bakinta bai yi shiru ba wajen magana.
     Su Hamma Ɗan Waziri suka sanyata a mota da ƙyar suka nufi gidan iyayenta da ita, don Yarima ya yi rantsuwar ba zai taɓa kaita gida ba. Yana ganin sun fita shi ma ya fara shiri musamman yadda jikinsa ya ɓaci sai da ya sake wanka duk da ransa a jagule yake.
   Da kyar Iyayen Nuwaira suka amsheta saboda irin mugun aikin da suka ji tana faɗa da bakinta ta aikatawa Yarima, korar kare suka yi mata har sai da Malam Liman ya yi masu nasiha kafin suka sassauta har suka amsheta, shi ma sun ce ba za su iya ba za dai su kaita asibitin mahaukata, don ba su aiketa yin abin da ta yi ba.
    **********
  Shi kam Yarima mugun gudu yake Allah dai Ya tsare shi har ya isa gida lafiya, tun daga ƙofa mutane suke yi masa barka da zuwa har ya isa harabar ajiye motoci, ko da ya fita bai nufi ɓangaren Hajja ba sai ya nufi na Yawuro, don ya san fa ba zai ji daɗi ba a wannan karon kuma ba ya da hujjojin kare kansa.
Yawuro tana zaune bayan sun gama waya da Ɗan Waziri yana sanar mata da nasarar da aka samu, suna ta yi wa Allah godiya sai jin sallamar Yarima ta yi. Da sauri ta juya tana faɗin “Lale-lale da zuwan Magajin sarki.” Kai a ƙasa tun da yake bai taɓa jin kunyar Yawuro irin na yau ba, don tabbas jikinsa ya ba shi ya aika ba daidai ba shi ya sa Hajja da kanta ta je ta dauko Salmah. Kuma dole Yawuro ta ji haushi sa a matsayinta na mahaifiyar Salmah, to amma ya ya iya? Dole ne ya nufo ta don a wajensu kawai ne zai samu sauƙi.
  “Ina kwana Yawuro?”
“Lafiya lau Magajin sarki, kai ne haka da safe.” Fuska sake take ba shi amsa.
  “Wallahi kuwa Yawuro.”
“Madallah bari a hado maka abin karyawa, don kila baka karya ba ka taho?”
  “Eh!” Ya amsa.
Take aka cika masa gaba da abin karyawa, ba ya jin yunwa shi yanzu damuwarsa kawai yadda zai ɓullowa lamarin, amma a haka ya tuttura abincin. “A'a Magajin sarki ba dai har ka ƙoshi ba?” Yawuro ta tambaya lokacin da ta fito daga ɓangaren Baba Waziri, don ta shiga ta sanar masa da zuwan Yarima.
  “Eh na ƙoshi ne, Allah Ya sa Baba Waziri ya tashi?”
“Eh! Ya tashi na sanar masa da zuwanka ma, yanzu zai fito.” Tana gama rufe baki yana fito. Da girmamawa Yarima ya fara gaisar da Baba Waziri, shi ma ya amsa masa da sakin fuska. A tare suka fita ba su zame ko ina ba sai ɓangaren Maimartaba don lokacin bai fita faɗa ba, shi kansa Maimartaba ya yi mamakin ganin Yarima musamman yadda ya koma ya yi baƙi ya lalace.
   Bayan gama jin bayanin Yarima Maimartaba da kansa ya kira Hajja da Salmah, kusan a tare su Hajja suka shiga da Hamma Ɗan Waziri da Malam Liman. A lokacin Yawuro da Jakadiya suka shiga. Hajja tana ganin Yarima ta wani haɗa rai kamar za ta ce wayyo Allah! Kaɗan take jira ta fara fadar, aiko Yarima da ganganci ya ce “Ina kwana Hajja?” “Idan da ban kwana ba za ka ganni? Wallahi Hafizu ka fita daga idona tom!” Ta ja kwafa. Yarima kam runtse ido ya yi don a tarihi bai taɓa jin Hajja ta ambaci sunansa ba sai yau.
  “Haba ki yi haƙuri mana Hajja.” “A'a babu fa maganar hakuri, abu ɗaya kawai zan yarda da shi Hafizu ya ba Salmah takardar ta, domin ba zan lamunci cin mutunci da wulakanci ba, tun da shi ya zaɓi wancan.” Gaba Yarima da Salmah lokaci guda ya buga, don kalmar ta yi masu girma.
  “Duk maganar ba ta kai haka ba, ai duniya komai hakuri ake yi da shi yanzu mu ba ma wannan maganar ta haɗa mu ba, don gaba daya shi Yarima baya da laifi matarsa ce ta shiga ta fita duk ta haddasa wannan abu da ya faru, don ga Malam Liman nan da Jakadiya za su yi maki bayani.”
Hmm! Kawai Hajja ta ce ta juyar da kai.
Nan dai Malam Liman ya fara bayani kamar yadda ya yi wa su Jakadiya bayani, shi ma Ɗan Waziri ya kara tabbatar masu da abin da Malam Liman ya faɗa. Gabaɗaya sun cika da mamaki amma ban da Hajja da ta miƙe tare da riƙe hannun Salmah ta ce “Babu abin da ya dameni da asirin da aka yi masa, idan da asiri to ya tadda hali don haka wanann matsalar sa ce.”
  “Haba Adda yanzu don Allah ba za ki zauna ki fahimci yadda abin yake ba, babu laifin Yarima fa a maganar nan kina ji fa ta ce tun ranar da ta fara ganinsa ta kai sunansa wajen boka, sai da ta shiga ta fita har asirin da take yi masa ya kamashi, kuma Alhamdulillah tun da yanzu an karya ai shi kenan.” Yawuro ke maganar cikin sigar lallashi.
  “Wannan bai dameni ba, da ya sani ma ya yi zamansa da matarsa, tun da tana sonsa kuma da ita ya dace,  Salmah dai ba zata koma gidansa ba, yanzu haka ina zaman jiran takardar salmah.” Tana kai wa haka ta ja ta suka yi waje, Baba Waziri zai sake magana Maimartaba ya daga masa hannu dole ya hakura. “Ku kyale ta har ta sauko don kanta, Hauwa'u ta yi fushi ne sosai wannan karon, ku barta za ta sauko da kanta kai ma Yarima kar ka kuskura ka je wajen da take ka bari har ta sauka.”

KYAKKYAWAR ALAK'AWhere stories live. Discover now