33

163 12 4
                                    

    KYAKKYAWAR ALAƘA.

ZULAYHEART RANO

STORY AYSHA WAZIRI

                  33

Washegari da ciwon kai mai tsanani Salmah ta tashi, amma haka ta daure da gyara bangarenta ta tsaftace komai, tare da kunna turaren wuta sannan ta yi wa Khairat wanka ta shirya ta cikin kayan sanyi, don garin ya tashi da sanyi ba ta shiga kicin ba sai da ta shiga ta yi wanka ta shirya cikin wasu riga da siket na atamfa, sosai kayan suka amsheta ta yi fakin sumar kanta da ribom mai kyau kalar kayan, sannan ta nufi kicin.
  Cikin kwarewa take aikinta kunun Gyaɗa ta dama, sannan ta soya doya da kwai ta kuma yi farfesun kan sa, karfe takwas ta kammala da komai na break, sannan ta tsaftatacce kicin ɗin kai ka ce ba a girka komai ba.
  Kiran Zaituna ta yi tare da bata umurnin ta ɗauki kayan da ta haɗa a kan babban tire ta Kai bangaren amarya, dandanan Zaituna ta cika umurnin Salmah, ko da ta kai kayan ta dade tana ƙwanƙwasa ƙofa kafin Nuwaira ta buɗe tana jefa mata harara.
  “Lafiya?” Ta faɗa tana yi mata kaskantaccen kallo.
  “Babu komai dama uwardakina ce ta ce a kawo maku abin break.” Da ladabi Zaituna ke ba ta amsa.
   “Oh sannu mu kam...” “Baby yaya dai na ji kina ta magana?” Yarima ya yi tambayar lokacin da ya iso ƙofar.
  “Barka da fitowa magajin sarki, dama uwardakina ce ta ce a kawo maku abin karyawa.” Zaituna ta faɗa tana zubewa a ƙasa.”
   “Aiko mun gode, an gaisar da Salmatyy Allah Ya yi albarka.” Yarima ya fada yana matsa mata daga hanya. Wani kululun bakinciki ya rufe Nuwaira, jin yadda yake magana yana wani washe baki har yana shi mata albarka, kwafa ta yi sannan ta shiga ciki. Lokacin har Zaituna ta ajiye kayan sannan ta fita.
  Wasa-wasa sai da Yarima ya kwana biyu ba tare da ya leƙa idan Salmah take ba, ita kuma a kwana biyun da ya yi ba ta fasa aika masu da abinci ba a duk lokacin da ta kammala, a cikin zuciyarta sam ba ta jin daɗin rashin ganin Yarima, sannan kuma tana mamakin yadda har ya iya yin kwana biyu ba tare da ya zo ya duba lafiyar ta da yarinyarsa ba, amma sai ta danne don kar ta ba zuciyarta damar sanya shi ɓangaren marasa adalci, sannan kuma tana samun ƙarin kwantar da hankali wajen Hajja wacce kullum sai sun yi waya a ƙalla sau uku ko hudu, duk don kawai ta ƙwantar mata da hankali.

Misalin ƙarfe shida na yamma Salmah ce zaune cikin falonta tana ta famar lallashin Khairat wacce ke ƙananan kuka, jijjiga yarinyar take a son ta yi shiru amma fir ta ki, kamar a mafarki ta tsinkayi Sallamar Yarima.
Ɗago da kai ta yi tana kallonsa idanuwanta cike da ƙwalla, murya tana rawa ta amsa masa.
   “Barka da shigowa Hamma.”
   “Yawwa Salmatyy, me ya samu Hajjata take ƙananun kuka?” Ya gama maganar yana miƙa hannu don ɗaukar yarinyar.
  “Nima ban sani ba Hamma, amma kamar zazzaɓi ke son kamata, kila hakori za ta yi.”
  “Kin ba ta magani?” Ya tambaya yana dudduba yarinyar.
“Maganinta duk sun ƙare, dama ina jiranka ne ka shigo sai na yi maka maga...”
“Wannan wanne irin shirme ne? Yarinyar ba ta da lafiya shi ne ba ki sanar min ba, yanzu kuma ki ce wai kin tsaya jiran na shigo? Yanzu kuma da ban shigo ba fa? Kina nufin sai dai ta mutu?” Yarima ya rufe ido yana zazzagawa Salmah masifa, wanda ya matuƙar bata mamaki rabon da ta gan shi a irin wannan yanayin tun kafin su yi aure.
  “Ka yi haƙuri, da baka shigo ba zan ba Zaituna ta amso mana.” Cikin sanyin murya take maganar.
  “Karki ƙara yi mini irin haka, ɗauko Hijab yanzu mu je a kaita asibiti.”
  “Toh.” Salmah ta amsa tana nufa bedroom.
  Daidai da fitowar ta daga bed ita kuma Nuwaira ta shigo “Prince wai lafiya ina ta jiranka daga cewa yanzu za ka fito?”
  “Yi haƙuri Baby, ina shigowa na samu Hajjata babu lafiya shi ne za mu kaita asibiti.”
  “Asibiti? A ranar kwanana? Gaskiya haka ba zai yiwu ba, tun wuri gara ka bata yarinyar ta ta je ta nemo mata magani.” Cikin izza ta ke maganar. A zafafe Ya buɗe baki da niyyar ba ta amsa, sai dai me? Suna haɗa ido da Nuwaira jikinsa ya yi sanyi ƙalau, ya ji ba zai iya ce mata komai ba. Ga mamakin Salmah sai taga Yarima ya miƙo mata Khairat din yana faɗin ga ta nan Salmatyy ki kaita asibiti.” Bai tsaya jin me Salmah za ta ce ba ya fita.
Saroro Salmah ta yi tana kallon Yarima da Nuwaira, wacce ta tasa shi a gaba kamar wani yaronta, hawayen da ba ta tsammaci zubowar su ba suka sauko saman fuskarta, ba ta damu ta share su ba a tarihin rayuwar ta yau ne aka fara yi mata abin da ya mugun bakanta mata rai, ji ta yi dama mutuwa ta yi ta huta da wannan bakincikin, ashe dama haka kishiya take? Ta yi wa kanta tambayar da babu amsa.
  Haka Salmah ta zauna ta sha kukanta ta koshi, abinka da farar mace fuskarta sai ta kumbura, har da ƙyar take iya buɗe ido. Zaituna ta kira ta haɗasu da direba suka kai Khairat asibiti, don ita ba za ta iya fita a yanayin da take ciki ba, ga jikin Khairat ɗin ya ƙara dumewa da zafi.
  *****
Alamu da sun nuna Nuwaira dai ba ƙaramin shiri ta yi ba kafin ta shigo gidan Yarima, domin kuwa a shi tun ba a fita daga satin auren ba har Nuwaira ta fara yin abin da ta ga dama, shi kuma Yarima ba ya iya tabuka komai.
  Kamar dai yanzu bayan sun fita daga ɓangaren Salmah masifa Nuwaira ta fara yi masa a kan ya shiga wajen Salmah ranar kwanarta, babu yadda ya iya sai haƙuri da yake ba ta.
  Gabaɗaya Nuwaira ta gama karkatar da hankali Yarima, ta zama ita ce mai ba shi umarni, abin da ta so shi yake yi baya da lokacin kowa sai nata ita ɗaya, ya manta da wata Salmah da yaransa har ma da garin Ningi.
  
Rano.

KYAKKYAWAR ALAK'ADonde viven las historias. Descúbrelo ahora