38

155 12 1
                                    

KYAKKYAWAR ALAƘA
      38

    Ƙarfe biyu da mintina su Hajja suka shiga garin Bauchi, kai tsaye gidan Yarima suka nufa Hajja ji take uwa ta yi tsuntsu ta ganta a cikin gidan. Yana yin fakin bata tsaya jiran komai ba ta fita daga motar babban burinta ta yi arba da Salmatyy.
    Salmah ce zaune ta rafka uban tagumi tana kallon Khairat wacce ke kwance magashiyyan tana jan numfashi da ƙyar, mugun zazzaɓi yarinyar ke fama da shi tun jiya duk wani magani da take da shi taɓa yarinyar amma jin babu sauƙi, ga shi ta rasa yadda za ta yi da ita ko ta je faɗawa Yarima ba za ta samu damar ganinansa ba ma, da ta tuno cin mutuncin da ya mata shekaran jiya sai jikinta ya ƙara sanyi shi ya sa ta zubawa sarautar Allah ido, lokaci-lokaci hawaye suna zubowa daga idanunta.
     Motsin buɗe kofa ta ji ya sanya ta yi sauri ta waiwaya wa don ganin wanda ya shigo, karaf! Idonsu ya haɗu da na Hajja wani irin faduwar gaba ya ziyarce ta, kenan dai su Adda Khadijah sai da suka faɗawa Hajja kamar yadda suka sanar mata? Duk sai ta ji hakan bai mata daɗi ba, cikin sauri ta miƙe tare da nufa wajen Hajja tana faɗin “Oyo-yo Hajjata.”
      “Oyo-yo Salmatyy, lallai kam biri ya yi kama da mutum, ashe dai su Hafsah ba ƙarya suka yi ba.” “Hajja me ya faru?” Salmah ta yi maganar tana sakin murmushin ƙarfin hali.
     “Babu komai.” Ta faɗa tana sakin Salmar ta nufi wajen da Khairat ke kwance tana cewa “Lafiya kuwa na ga yarinyar nan a kwance?”
     “Am wallahi Hajja ba ta jin daɗin ne, duk magungunan da ya kamata a bata an bata amma jikin har yanzu da zafi.”
     “An kaita asibiti?” Ta ƙarasa maganar tana kai hannu jikin yarinyar, mugun zafin da ta ji ya sanya ta yi saurin ɗauke hannu.
     “A eh dama dai...” Salmah fa ta daburce, don fa sosai Hajja ta tsareta da ido.
    Takaici ya sanya Hajja ba ta bi ta kan Salmah ba ta ɗauki Khairat ɗin ba tare da ta ce komai ba ta fita, a hanya suka haɗu da Hamma Ɗan Waziri “A'a Hajja lafiya kuwa?” “Babu lafiya Al-ameen mu je ka kai mu asibiti mafi kusa.” “Subhanallah!” Ya faɗa yana amsar Khairat ya sanya a mota Hajja ma ta buɗe tare da shiga, ya tayar da motar suna shirin barin wajen Salmah ta fito hankali tashe, tsayawa ya yi ta shiga sannan ya ɗauki hanya don tuni maigadi ya bude masu kofa.
    Cikin wani asibiti dake kan layin ya shiga, nan da nan aka amshi Khairat tare da sanyata a dakin A&E don ceto ran yarinyar, ruwa suka shiga sanya mata da allurai a ciki.
  Hajja don tsabar takaici kasa magana ta yi tana dai zaune cikin ɗakin da aka kwantar da yarinyar hannun na riƙe dana Khairat ɗin, lokaci-lokaci tana sakin ajiyar zuciya. Tana nan zaune sallah kawai ta iya tashi ta yi har kusan ƙarfe biyar a lokacin ne Hamma Ɗan Waziri ya shigo, don tun da aka sanya mata rufa ya fita zuwa masallaci bai dawo ba sai yanzu.
  “Hajja ya mai jikin?”
“Da sauƙi, amma har yanzu dai ba ta farka ba.”
“Allah Ya ƙara sauƙi.”
“Amin.” Hajja ta amsa cikin takaici ta dubi Salmah wacce ke zaune a gefe ta haɗe kai da gwuiwa, ta ce “Ke kam kin yi sallar la'asar?”
  “A'a Hajja ban yi ba.”
“Ya yi kyau.” Hajja ta faɗa tana kawar da kai ga dubanta.
  “Hajja na ce ko za a yi wa Yarima magana ne?” “Magana wacce irin magana kuma Al-ameen?”
“Ina nufin a sanar masa muna nan.”
  “To ban aikeka ba.” Dole ta sanya Hamma Ɗan Waziri yin shiru.
  “Za ki iya tashi ki je ki sama mana abin da za mu ci ko kuwa?”
  “Yadda kika ce Hajja haka za a yi.” A ladafce Salmah ta amsa.
Tare suka fita da Ɗan Waziri don shi ya kaita, wannan karon a cikin gidan suka samu motar Yarima hakan na nufin ya dawo gidan kenan. Ba dan Hajja ta hana shi yi masa magana ba to tabbas da sai ya je ya yi masa magana ko da hakan na nufin su ɓata har abada.
Cikin sauri-sauri Salmah ta kammala girka masu abincin, ba ta nufi asbitin ba sai da ta yi sallar magriba tare suka koma da Ɗan Waziri.
  Lokacin da suka koma asibitin Khairat ta tashi kuma Alhamdulillah! Jikin da sauƙi don a jikin Hajja suka sameta tana wasa. Sai da suka kwana suka yini kafin aka sallame su. Zuwa yanzu tuni Hajja ta kuma tabbatar da Yarima fa ba ta Salmah ya ke ba a yanzu, duk da ta hana a sanar da shi ai da a ce lafiya-lafiya ne da yanzu duk inda suke sai ya nemo su, kenan hakan na nufin da yarinyar mutuwa ta yi da sai a kaita ma ba tare da ya sani ba kwafa kawai ta ja, tana ƙara tanada masa irin hukuncin da za ta yi masa.
  Yamma ta yi sosai shi ya sa Hajja ta ba Hamma Ɗan Waziri umurnin su kwana a gidan Salmah washegari sa koma Ningi tun da kafin su kai dare zai yi. Shi dama Ɗan Waziri ko cikin yi wa Hajja biyayya yake a yau ma bai yi wata musu ba, duk da zaman garin Bauchi ya gundure shi ko kusa bai taɓa kawowa Yarima zai iya share Salmah ba, duk da wani gefen na zuciyarsa tana zargin matar da Yarima ya aura, don babu tantama ita ce ta tarwatsa tsakaninsa da yan'uwansa da matarsa har ma da 'ya'yansa. Ya san a yanzu duk abin da zai faɗawa Hajja ba za ta yarda ba shi ya sa ya bari har ya koma gida sannan zai yi wa Yawuro bayani.
  Suna shiga cikin gidan Hajja wanka ta soma yi sannan ta yi alwala ta fuskanci alkibla kamar yadda ta saba a kullum, ita ma Salmah haka wanka ta fara yi sannan ta shiga kici ta fara girka masu abin da za su ci, bayan sun ci abinci suka ɗan taɓa hira kafin Hamma Ɗan Waziri ya yi masu sallama ya nufi hotal ɗin da ya sauka in da ya kwana jiya. Salmah kawai ce aka bari a falo don haka ta miƙe tare da nufa ɓangaren Nuwaira a kan ta sanar da Yarima Hajja ta zo.
  Tana ƙwanƙwasa kofar Nuwaira ta buɗe, ganin Salmah sai ta ƙara haɗe rai ta fara magana “Lafiya cikin daren nan?” “Lafiya lau wajen Hamma na zo.” Hankali kwance Salmah ta ba ta amsa. “Oh! To yana barci.” “Ki tashe shi ki faɗa masa cewar Hajja ta...” “Da Allah dakata.” Nuwaira ta yi saurin katse Salmah, sannan ta cigaba “Ba zan tashe shi ba ba Hajja ba koma wace...” Tsabar yadda zuciyar Salmah ke tafasa ba ta san lokacin da ta daga hannu ta shararawa Nuwaira mari ba, ji kake tasss! Za ta iya jure komai amma ba za ta juri a ci mutuncin Hajja. Saukewa Nuwaira mari ya yi daidai da zuwan Yarima don ya ji ta ambaci sunan Hajja. Nuwaira tana ganin Yarima ta fashe da kuka.
Ita ma Salmah saurin ja baya ta yi, don kuwa ba ta manta da ranar da ya so dukan Adda Khadijah ba. “Ke ba ki da hankali matar tawa kika mara?” A zafafe ya gama maganar.
  “Hamm...” Ganin da ta yi ya nufo ta gadan-gadan ya sa ta ruga da gudu ya yin da Yarima ya take mata baya. Har cikin falon ya shiga cikin zafin zuciya a jikin bango Ya matse Salmah tare da daga hannu da niyyar tsinkawa Salmah mari. “Hafizu karka kuskura hannunka Ya sauka kan Salmah da sunan duka.” Ya tsinkayi muryar da ke sanya shi cikin ladabi ko a wanne hali yake, muryar da ba zai taɓa manta mamallakiyar ta ba. Da sauri ya waiwaya don tabbatar da ko itan ce. Idonsa ya hadu da na Hajja da sauri ya zube kan gwuiwowinsa.
  “Ke Salmah zo nan ashe har dukanki yake ban da labari?”
“A'a Hajja tsaya ki..” Tashi ka fita karka ce mini komai, don ba ka da abin da zaka faɗa mini ba dai ka ce wannan rayuwar ka zaba ba? Ka je ka yi idan har hakan shi ne daidai a gareka. Magana ya ke son yi amma ya kasa sai dai jikinsa ya yi sanyi.
  “Prince lafiya na ga ka zo ka dade?” Ya tsinkayi muryar Nuwaira, wacce ta shigo falon. Wani kallon tsana da kyama Hajja ke aikawa da Nuwaira, tana son ta yi wa matar rashin kunya amma sai ta ga matar ta yi mata matuƙar kwarjini, tunda take bata taɓa ganin macen da ta yi mata kwarjinin irin wannan ba, idan har ba gizo idonta yake yi ba sai ta ga kamar ita ce mahaifiyar Yarima, don ta ga photu nan ta da yawa a cikin wayarsa.
  “Zaman me kake yi mana anan Hafizu?” Hajja ta faɗa tana jefa masa harara. Tun da Hajja take ba ta taɓa ambaton Yareema da sunansa kai tsaye ba sai yau. Shi kansa Yareema ya ji abin banbarakwai, don haka sai ya yi ƙasa da kai tare da soma ba ta haƙuri.
  “Ki yi haƙuri Hajj...” “Na ce ka fitar mana daga nan ko?” Ta gama maganar cikin daka masa mugun tsawa, wanda ba shi ba hatta Nuwaira da Salmah sai da suka firgita.
 

KYAKKYAWAR ALAK'AWhere stories live. Discover now