Page 22

1K 54 3
                                    

👉🏽💍 *KYAKKYAWAR ALAK'A*💍👈🏽

                    ©
*ZULAYHEART RANO*

*My wattpad username zulayheartrano89*

*STORY AYSHA WAZIRI*

*A yi hakuri da fa, Aradu ayyuka ne suka min yawa, kuma kwana biyu an bikin Yayana, ga kuma wayar tana bani matsala yau ma na yi maku ne saboda kila daga yau sai kuma lokacin da Allah ya so zan dawo online, a yi min afuwa insha Allah very soon zaku ji ni. I love You fisibilillahi.* 😍😍😍

*DEDUCTED TO DUK WANI MAI KARANTA KYAKKYAWAR ALAKA*

                        *22*

Hajja na ganin Yarima ya fita ta dawo da hankalinta kan Salmah "Salmatyy kina da hankali kuwa? Daga haihuwa yau shi ne har kika fara sakar masa jiki, da wannan laɓuɓun Yaron? To bari ki ji na fada maki shi namiji mijin mace huɗu ne, da zarar yaga kin lalace wata zai nema ya aura, ba niyya ta raba ki da mijinki ba a'a ina fada maki ne ki bi a hankali, domin bani da yancin hana shi yin aure." Shiru kawai Salmah ta yi kanta a kasa ta kasa daga shi balle ta kalli Hajja don sosai take ji kunyar Hajja.
     Hajja tana gama yi mata fada ta fice don dama abu ta zo dauka a dakin, to haka dai aka ci gaba da harkoki kullum gidan cike yake da yan'uwa da abokan arziki, masu zuwa taya Yarima da Salmah murnar samun karuwa, har ranar suna ta zo ranar da Maimartaba ya bayyana sunan jariri wato ABDULMUMIN sosai jama'ar gidan suka yi murna da sunan, Yaro ya ci sunan Waziri. An yi taro lafiya an tashi lafiya, an bar Salmah da jaririn ta tana ci gaba da shayar da shi, yau da aka yi kwana biyu da yin suna Yarima ya haɗa kayansa zai koma Bauchi, don tun da ya taho bai koma ba sai da ya kimta kayansa sannan ya nufi bangaren Hajja.
    Babu Salmah a falo don haka sai ya shiga bedroom, yana shiga ya samu Yaron shi kadai a kwance da sauri ya karasa wajen tare da ɗaukar sa yana yi masa wasa, zama ya yi don ya ji motsin ruwa a toilet hakan ya tabbatar masa da Salmah tana ciki, bata jima ba ta fito "Hamma ashe ka shigo?" Ta tambaya bayan ta zauna. Kallonta Yarima ya yi cikin wani yanayi har ya kasa ɗauke idonsa akanta, don ji yake kamar ya jawota jikinsa musamman kirjinta da suka wani ciko, ko ya ta motsa rausaya suke, leben kasan bakinsa ya tattara ya cusa cikin baki tare da dan cizawa har dai yanzu idonsa na kanta, Yaron ne ya fara motsin kuka amma sam Yarima bai lura ba.
    "Hamma wannan kallon fa? Ga AREEF nan ya fara kuka." Sunan da suke kiran yaron kenan. A jiyar zuciya ya sauke tare da sakar mata murmushi, ya ce "Ummuna kallonki nake yi kin yi kyau, Aradu jego ya amsheki kina kallon madubi kuwa?" Bata yi magana ba sai da ta sanyawa yaron nono cikin baki sannan ta ce "Kai Hamma har wani jego ne ya amsheni kullum ina ruwan zafi." "Ai ruwan zafin ba mai cutarwa ba ne na gyara jiki ne shi yasa kika yi kyau." Ya dire maganar yana kai hannun saman nonon da Yaron ke tsotsa. "Hamma zai kware fa!" Salmah ta yi maganar da shagwaba.

"Oh! Sorry Ummuna na gama shiryawa fa."

"Lah Hamma har ka gama shiryawa baka kira mun shirya maka ba?"

"Ku din ne zaku shirya mi?"

"Eh mana ni da AREEF."

"Yawwa tashi mu je yar albarka, daga nan zan nuna maki wani abu ma." Yarima ya dire maganar yana kashe mata ido daya.

"Wai Ni? Rufa min asiri Hamma ina tsoron Hajja."

Murmushi kawai ya yi don yasan dama ba binsa zata yi ba, shi yasa ya ce haka, bai ce komai ba ya dauki Areef ya fara yi masa photo, sanna ya aje Yaron yana manna masa kiss ya ce "ki yi min addu'a Ummuna sai kuma na dawo."
"Allah ya tsare hanya ya bada sa'a."

"Amin." Ya amsa yana fita. Ko da ya fita wajen Maimartaba ya je ya yi masa sallama, sannan ya yi wa Baba Waziri da Yawuro, a karshe ya kara komawa bangaren Hajja sallama suka yi tana ta yi masa addu'a. Sannan ya wuce cike da kewar Salmah da Yaron sa.

KYAKKYAWAR ALAK'AWhere stories live. Discover now