Page 15

1K 59 1
                                    

👉🏽💍 *KYAKKYAWAR ALAK'A* 💍👈🏽

                     ©
     *ZULAYHEART RANO*
*Wattpad username zulayheartrano89*

*STORY AYSHA WAZIRI*

*This page deducted to My Besty Khadija S Moh'd*

                     *15*

Yana aje wayar ya kuma kankameta domin gani yake idan ya tashi zata mutu, ba a fi mintina uku da yin wayar ba har jakadiya da Hajja sun iso bangaren ( kowa dai yasan matsayin Salmah a wajen Hajja da da yawa takan matsar da kunyar Yarima ɗan fari ne take nuna kula ga Salmah, shi yasa yauma ta yi gaggawar isa bangaren don ganin halin Salmatyy ke ciki.) Ai ko sosai ta firgita da yadda taga halin da Salmah ke ciki da sauri ta kira Dr a waya tana sanar masa ya yi sauri, a cikin minti biyar har Dr ya iso, cikin kwarewa ya fara bata taimakon gaggawa, don tuni ta fita hayyacinta, lallai abin ya girmama yau Yarima har da su hawaye, ko da Dr ya ce ya fita daga dakin kin fita ya yi a gabansa aka yi mata komai, zuciyarsa ta raunana har cikin ransa baya fata ya rasa babyn su, domin ya ci burin ganin cikin Salmah. Yana cikin dakin Dr ya kammala komai, har da karin ruwa domin bata zubar da jini da yawa ba, shi yasa kawai ya daura mata ruwa "Dr ya cikin da fatan bai zube ba?" A raunane ya yi tambayar, yana gyara mata kwanciya. "Ka kwantar da hankalinka ranka ya dade, ka yadda da kaddara domin ta riga fata, duk yadda na so kar cikin ya fita abin ya gagara, sai dai ban tabbatar ko cikin ya zube ba sai nan da sati huɗu zuwa shida, amma ina rokonka da ka yi haku..." Bai gama ba Yarima ya shakoshi cikin zallar tashin hankali "Anya Dr ka san kan aikinka kuwa? Ta ya zaka ce ka yi iya bakin kokari amma sai da cikina ya zube, to bari ka ji..." A haukace Yarima ke magana jikinsa na tsuma kamar mazari. "Sake masa wuya tun kafin na k'araso wajen, ashe baka da hankali ban sani ba?" Cike da ɓacin rai Hajja ta dire maganar tana aika masa harara.
          Zame hannunsa ya yi yana barin dakin, don sosai ya gano kallon takaici da Hajja ke aika masa "Ka yi hakuri Dr kasan halin Yarima sai a hankali." Hajja ta yi magana da kwanciyar murya. "Babu komai ranki ya dade, Allah ya bata lafiya amma a kula da ita sosai, idan da hali a rika barinta tana samun isasshen huta." "Insha Allah Dr muna godiya." Daga haka Dr ya yi masu Salmah. "Jakadiya ga Salmah nan ki kula da ita da kyau idan ta farka sai ku taho bangarena." "Insha Allah ranki ya dade zan kula da ita kamar yadda zaki kula da ita." "Yawwa ina godiya." Hajja mai sanyin hali da hakuri kenan, sam bata nuna ita wata ce, bangaren ta ta koma cikin zuciyarta ta kudiri aniyar sai ta nunawa Yarima kuransa a wannan lokaci, domin ta lura sam baya da tausayi. 
    Yarima na fita wajen Hamma ɗan waziri ya nufa, don yasan tabbas idan ya zauna cikin bangaren su zai gamu da fushin Hajja, bayan sun gaisa da Hamma ɗan waziri sai shiru ya ratsa, ɗan waziri ya kula da Yarima baya cikin natsuwa don haka sai yake tambayar sa "menene naga kamar kana cikin damuwa?" Gyara zama ya yi tare da shafa sumar kansa ya ce "wallahi kai dai bari ina cikin damuwa ɗazun tsautsayi ya afka mana har cikin dake jikin Salmah ya fita." "Subhanallah! Ga rin ya haka ta faru?" "Tsautsayi ne kawai." "To Allah ya kyauta gaba ya kawo wani mai albarka, yanzu ya jikin Salmah?" "Da sauki har ta samu bacci ma sai dai har ga Allah ban so haka ba." "Ka yi hakuri ka yi addu'a Allah yasa haka shine mafi Alhairi." Haka ɗan waziri ya yi ta ba Yarima baki har ya ɗan rage damuwarsa, sai dai yana tunanin yadda Salmah zata karbi lamarin.
      Jakadiya ce ta ci gaba da kula da Salmah, wacce ke bacci a lokaci ƙalilan har ta fada, fuskar ta yi fiyau kamar ba salmar Hajja ba, bata farka ba sai karfe biyar da mintina, a hankali take bude ido har ta gama buɗe su duka, jakadiya ta gani a kusa da ita a zaune, kallonta ta yi tana mamakin yadda jakadiya ta zo bangaren, zafin da ta ji a hannunta yasa ta kalli wajen, karin ruwa taga an jona mata gabanta ya yi mummunar faduwa take abin da ya faru ɗazun ya dawo mata fes a zuciya, wasu hawaye ne masu dumi suke sakkowa daga idonta. "Shi kenan na rasa babyna a karan farko?" Tambayar ta yi wa kanta mara amsa. A jiyar zuciya mai karfi ta sauke tana gyara kwanciya "Sannu Uwardakina ya jikin?" Jakadiya ta yi tambayar cikin kulawa. Kasa bada amsa Salmah ta yi don kukan na shirin cin karfinta, ganin haka sai jakadiya ta nufi toilet ruwan zafi ta haɗa mata sannan ta fito.
      A lokacin Salmah ta zame karin ruwan dake hannunta, don ya kare bata yi magana ba sai shiga toilet ta yi, tana fitowa ta sanya riga da zani, ta zauna bakin gado sosai haushin Yarima ya cika zuciyarta, saboda a lokacin da take ba shi hakuri da ya saurara haka ba zata faru ba. "Ki yi hakuri Uwardakina duk abin a kika gani rubutacce ne, ki yi addu'a Allah yasa haka shi yafi zama Alhairi, ya baki wanda ya fishi." Kau da kai gefe Salmah ta yi a ta ce "to." Amma a zuciyarta fadi take "ai duk wanda ya rasa Yaron fari dole ya yi kuka." "Tashi mu je idan zaki iya tafiya, Hajja ta ce ki je can bangaren ta." Jakadiya ce ta katse mata tunanin da take yi.
     A hankali take tafiya jikinta babu kwarai, hijab kawai ta sanya suka nufi bangaren Hajja, suna shiga Hajja ta yi saurin tasowa ta tari Salmah tana fadin "Sannu Salmatyy ya jikin?" Shigewa jikin Hajja ta yi ba tare da ta ce komai ba, su Zaituna ne suka yi sallama dauke da food plask da Hajja ta sanya a yi wa Salmah hadadden abinci, a gaban Hajja suka ake suna fadin "an kammala komai ya shugaba." "Sannunku da kokari." Sai da suka amsa sannan suka fita. "Tashi ki ci kin ji Salmatyy." "Ni Hajja ba zan iya ci da kaina ba, kalli hannun fa a kai aka tsira allura." A shagwaɓe ta gama maganar. Murmushi kawai Hajja ta yi ta ce "To dawo nan ki zauna, ai dama Ni ke baki abaki yau ma bari na baki." Dire maganar ta yi tana dauko cokali, a hankali take bata taɓa ci babu laifi ta ɗan ci da yawa sannan ta ce ta koshi. Duk yadda Hajja ta so Salmah ta kara abincin ki ta yi dole ta barta ba don ta so ba.
          Yarima bai koma bangaren su ba sai bayan magrib, turus ya yi ganin babu Salmah a ɗakunan gidan, domin babu dakin da bai shiga ba bata ciki "kenan Hajja ta dauketa?" Ya yi tambayar tare da faduwar gaba. Tabbas tana bangaren Hajja domin babu inda zata je sai can, yanzu babbar matsalar shi ne yadda Ai tunkari bangaren Hajja, mugun kunyar ta yake ji. Haka dai ya daure ya mike jikinsa babu wani dadi ya fice daga ɓangaren su. Zaune Hajja da Salmah suke tare da Adda Ameena da Hamma ɗan waziri da suka zo duba Salmah, sai hira suke yi abinsu hankali kwance.
      Haje rai Hajja ta yi uwa bata taba yin dariya ba, Salmah kuwa tashi ta yi ta shige bedroom, don bata kaunar ganin Yarima don shi ne silar faruwar komai, amma har yanzu bata ji KYAKKYAWAR ALAK'AR su ta raunana ba, sai dai abin da ta sani bata son ganinsa, kwanciya ta yi abinta tare da lumshe ido tana tuna lokacin da take rokonsa ya barta ya ki. A falo kuwa duk yadda Yarima yaso Hajja ta yi masa magana abin ya gagara, har su ɗan waziri suka yi sallama suka tafi bata ce masa komai ba, gyara zama ya yi ya ce "Hajj..." "Tashi ka bar min nan." Rai a matukar bace ta yi magana tana masa nuni da yatsa, babu yadda ya iya dole ya mik'e jiki a sabule. Yarima fa ya shiga tsaku domin duk inda ya juya babu dadi, musamman ta wajen Hajja don ko kallon arziki baya samu, duk iya yadda zai yi ya yi amma a banza, ita kanta Salmah da tagan sa shigewa bedroom take bata fitowa sai ya gaji da zama ya wuce, don tana shiga Hajja ke gyara zama taki fita nan da can har sai ya gaji ya tafi. A haka har ya cinye sati biyu babu canji yana son tafiya wajen aiki amma yan tunanin ta yadda zai fara, Yau dai ya kudurci sai ya ga Salmah ko ta halin k'ak'a. Don haka karfe takwas na dare ya shiga falon Hajja da Sallama, Salmah ce kawai a falon tana cin abinci, don tun da abin can ya faru wani shegen cin abinci ya sameta, a rana sai ta ci sau goma har cikin dare tashi take ta ci. Ganin Yarima da sauri ta mik'e zata shige cikin bedroom da zafin nama ya rikota "Lafiya Ummuna?" Ya yi tambayar yana kallon fuskarta.
        Shiru ta yi don kyakkyawar rikon da Yarima ya yi mata ya bala'in kashe mata jiki, gani bata ce komai ba ya ce "fada min Ummuna menene laifina? Don ciki ya samu matsala sai a hau yin fushi dani? To idan don wannan ne wallahi ki bani dama daga yanzu zuwa safe da yaddar Allah zan sake yi maki wani cikin." "Hamm." Bata gama rufe baki ba ya jefa bakinsa cikin nata, duk abincin dake cikin bakin sai da ya kwashe ya hadiye wani salo yake mata har tsayuwar tana neman gagararsu ya ji wani irin muguwar tsawa a bayansa "Kai wato rashin kunyar yanzu har a gabana yinsa kake yi ko? To maza kazo ka bar min falo tun ban bata ranka ba." Juyowar da zai yi sai suka yi ido hudu da hajj...

Vote me
Comment
& Shere on wattpad.

Zulayheart Rano

KYAKKYAWAR ALAK'Aحيث تعيش القصص. اكتشف الآن