Page 11

1.2K 72 2
                                    

👉🏽💍 *KYAKKYAWAR ALAK'A*💍👈🏽

                       ©
     *ZULAYHEART RANO*
*Wattpad username zulayheartrano89*

*STORY AYSHA WAZIRI*

*Hhhhhhhhh wayyo! Aradu comments na yau da kika yi min na yi matukar jin dadi, har wani suna kika sanya ma Salmah da Yarima sunan da ya dace da su, tofa lallai suna godiya har nima Yar Mutan Rano na taya su godewa. Shi yasa na baki wannan shafin kyauta ki yi yadda zaki yi da shi idan kin ga dama ki ce kar kowa ya karanta, ni dai burina ki karanta ki yi min comments.*

Dis page for you *SISTER SADIYA ZABURA*

*TEAM UMMREEMA*

                     *11*
Haka Yarima ya ci gaba da lallaɓata yana samun abinda yake so har suka cika wata daya, kuma a ranar ne ya kamata ya koma wajen aiki, sam baya kaunar raba wajen kwana da Salmah sai dai ya zama dole su raba ɗin, don da ya yi wa Hajja maganar zai tafi da Salmah ce wa ta yi ba yanzu ba, sai idan ya dawo zai sake komawa sannan zai dauketa ba dan ya so ba ya yadda, ga yi yan office din sun addabeshi yadda suke ta kiransa a waya aiki ya taru a office abin har tsoro yake ba shi.
      Yana kwance ya yin da Salmah ke shirya masa kaya cikin karamin akwati, wanda zai yi tafiyar da shi, idonsa kyar akanta ya kasa ɗauke su, ko ya ta motsa jiki sai ya ji har tsakar kansa, babu ma yanzu da kayan da ke jikinta gaba daya masu tada sha'awa ne, rigace karama iyakarta cibiya, sai siket karami ko gama rufe mata cinya bai ba, santalasantalar cibiyoyin ta a waje suke kanta babu dankwali, sai sumar da suka bazu a gadon bayanta. Jikinta na fitar da ni'imantaccen kamshi mai sanyaya zuciyar masoyi.
      "Ummuna zo." Yarima ya yi furucin yana sakin murmushi. "Hamma ban fa gama ba, ka bar na k'arasa." A shagwaɓe ta ba shi amsa. "Zo dai ki ji yanzu zaki koma fa, wani abu zan nuna maki." Matsowa ta yi kusa da shi tare da dafa hannayenta akan gadon ta ce "Gani." Irin yadda ta yi ba karamin tafiya da hankalin Yarima ta yi ba domin gaba daya dukiyar fulanin ta sun fito daga cikin rigar, saboda babu abinda ya tare su daga ciki. Bai jira komai ba ya kai hannu ciki da wani irin salo, lumshe ido Salmah ta yi cikin yanayi mai daɗi "Ummuna za ki bini?" Yarima ya tambaya yana ci gaba da wasa da kirjinta, wani nishi ta saki tare da bankaro masa kirji ta ce "A'a Hamma kabarni wajen Hajja." "Haba Salmatyy." "Wayyo Hamma zaka kasheni da salonka fa, Please ka bari na gama haɗa ma kayan time na tafiy." Ko sauraronta bai ba sai ci gaba da sarrafata yake bai barta ba sai da ya samu nutsuwa, a tare suka yi wanka suna fitowa ta karasa hada masa kayan, cikin doguwar riga ta shirya na atamfa.
        Fita suka yi tana rike da akwatin, shi kam Yarima jin tafiyar ya yi sam babu daɗi, don babu Salmah a tare da shi, bai shiga cikin gida ba sai da suka sanya kayan cikin mota, ɓangaren Yawuro suka fara shiga, bayan sun gaisa ta yi masa fatan alheri da samun nasara, sannan suka nufi sashin Hamma ɗan Waziri, basu dade ba suka isa ɓangaren Maimartaba, shima sai nusiha ya yi masa da, a bangaren Hajja Chub'ad'o suka daɗe, sosai Hajja ta ji dadin ganin yadda Yarima ya sake da Salmah. A takaice dai Yarima bai bar garin Ningi ba sai kusan biyun rana.
    Salmah tana ganin ya shiga mato, sai hankalinta ya tashi hawaye suka fara turuwa a idonta, babu yadda zata yi ne musamman da Hamma ɗan Waziri yana wajen, har Yarima ya shiga mota zai tada hada idon da suka yi da Salmah ya hango hawaye a idonta ya sanya ya fasa tada motar ya fito, bai ce komai ba sai riko hannunta ya yi can gefe ya jata.
"Menene abin yin kuka Ummuna?" Cike da lallashi ya yi mata tambayar. "Babu komai Hamma ba kuka nake yi ba." "A'a Ummuna kin yi kuka kalli idon ki fa, ko zaki bini ne?" "A'a Hamma ka barni a wajen Hajja." "Shin kenan amma bana son kina shiga cikin damuwa kuma fa ba dadewa zan yi ba da na samu lokaci zan dawo, kuma ga waya zamu rika yin magana." A tausashe ya gama maganar. "To." Ta amsa tana sakin fuska.
   Murmushi Yarima ya yi yana bata kiss a kumatu, sannan ya wuce, a hankali take daga masa hannu har ya fita, bangaren Hamma ɗan Waziri ya ji dadin yadda Yarima ke nuna kula ga Salmah, har cikin ransa bai yi tunanin haka Yarima zai yi saurin sauka ya kula da Salmah ba, amma yau ya tabbatar Salmah yar gatace gaba da baya, addu'a ya ci gaba da yi masu ita da Yarima, bayan tafiyar Yarima Salmah komawa cikin gida ta yi a falon Hajja ta sameta zaune tana cin 'ya'yan itatuwa, zama ta yi tana faɗin "Sannu da hutawa Hajjata." "Yawwa Salmatyy kin dawo?" "Eh Hajja." Ta dire maganar tana kwanciya akan kafet. "Tashi daga kwanciyar kasa ki koma kujera Salmatyy." "A'a Hajja na fi son nan." Salmah ta bata amsa tana kara lafewa. "Kin ci abinci ne?" "Sai anjima zan ci." Daga haka bata kuma cewa komai ba ta lumshe ido, tun yanzu har ta fara kewar Yarima don a zaman da suka yi ta saba sosai da jikinsa, amma yanzu sai ita ɗaya ta kwanta, wasu hawaye ta ji suna shirin zubo mata ta yi saurin mai da su.
     Haka da dare da kyar bacci ya dauke ta, bayan sun sha hira ita da Yarima yana ci gaba da jaddada mata matsayinta a zuciyarsa, haka ta ci gaba da rayuwa kullum makale da waya, yau juma'a tun da Salmah ta tashi ta yi break bata zauna a bangaren Hajja ba, ita da su Zaituna suka nufi bangaren ta domin yau Yarima zai zo, farin ciki sosai ya mamaye Salmah, har Hajja tana mamakin yadda Salmah ke ɗokin dawowarsa, karfe sha biyu suka kammala komai na gyaran gidan, lungu da sako duk an turare da turaruka masu kamshi, wanka ta yi ta shirya kanta cikin kananun kaya, bak'ar jallabiya ta sanya mai botira, babu wanda zai ga kayan dake ciki, sai Yarima domin shi ya ce ta yi masa irin kwalliyar. Bai shigo ba sai da aka idar da juma'a,  bangaren Yawuro ya fara shiga suka gaisa sannan ya je wajen iyayensa maza Maimartaba da Baba Waziri, daga karshe ya shiga bangaren Hajja Chub'ad'o sun gaisa sai zare ido yake yana jiran ta ina Salmah zata bullo, amma sai ya ga wayam kasa daurewa ya yi har sai da ya tambaya "Hajja ina yar shagwaɓar ki ne?" A kunyace ya gama tambayar.
        Harara ta jefa masa ba tare da ta ce komai ba, ganin haka sai ya mike don ya fahimci inda ta dosa, Salmah tana zaune a falo ta ji sallamar Yarima, ai da sauri ta isa kofar tare da fadawa jikinsa, bai yi wata wata ba ya sureta ya dagata sama, juyi ya rika yi da ita kamar ya dauki babyn roba daga karshe suka zube akan kujera "Oyo-yo Hamma." Salmah ta faɗa cike da murna. "Yawwa Ummuna kin yi kyau." "Na gode Hamma, ya hanya?" "Alhamdulillah!" Ya bata amsa, zaune ta yi saman cinyarsa, cikin nutsuwa ta fara ɓalle masa botira.
Duk wani kaya dake jikinsa sai da ta raba shi da su, sannan ta ce "wanka Hamma! Da wata mayaudariyar murya ta yi maganar. Ajiyar zuciya ce ta kwace wa Yarima wacce bai shirya ba, domin sosai sakon da ta aika ya isa zuciyarsa da jikinsa gaba daya.  Ganin yadda ya kasa ɗauke ido akanta, sai ta hura masa iska tana faɗin "wannan kallon fa Hamma kamar zaka cinyeni danya." Murmushi ya sakar mata tare da lumshe ido ya ce "salon ki ke tafiya da hankalina Ummuna bana jin zan iya rayuwa ba tare da ke ba, Please ki soni ko rabin wanda nake maki ne." Kwanciya ta yi a jikinsa ta daga kanta tana kallonsa cikin ido ta ce "Haba Hamma kar dai kana kokwanto da soyayyar da Ummu Salmah ke yi maka? To idan kana yi daga yau ka bar yi domin har abada Salmah taka ce, domin ka aka yi Salmah shi yasa iyayenmu suka kulla mana KYAKKYAWAR ALAK'A."

Team UMMREEMA😻😻

Vote me
Comment
& Shere on wattpad

Zulayheart Rano

KYAKKYAWAR ALAK'AWhere stories live. Discover now