Page 9

1.4K 72 2
                                    

👉🏽💍 *KYAKKYAWAR ALAK'A* 💍👈🏽

©
*ZULAYHEART RANO*
*Wattpad user name Zulayheartrano89*

*STORY AYSHA WAZIRI*

😒 *Team Ummuna Salmah*

BURINA FAN'S na ga alama kuna team Yarima☹ to ni dai ina *team Ummuna Salmah* ehe🤨

*09*

Da takaici Hajja ta gama maganar tana tallafo Salmah jikinta, ruwan da ta gani kusa da gadon ta ɗauko bayan ta yi bismillah ta fara sha fa mata a fuska, wata doguwar ajiyar zuciya Salmah ta saki tare da bude ido, bata gama dawowa hayyacinta ba abin da ya faru ɗazun ya dawo mata fes cikin kwanya, wani razanan nen kara ta saki jikinta ya dauki rawa tana faɗin "Hamma zan mutu." "Salmatyy bude ido Hajja ce a gabanki bar yin kuka." A tausashe Hajja ke mata magana, buɗe ido ta yi tana ganin Hajja ce da gaske sai ta kankameta tare da sakin sabon kuka.
"Ya isa haka Salmatyy bar yin kuka kar ya haifar maki da zazzaɓi." Shiru ta yi tana dai rungume a jikin Hajja hawaye ba su bar fita daga idonta ba, a haka jakadiya ta fito tana faɗawa Hajja ta gama haɗa ruwan. "To jakadiya ga Salmah nan ki taimaka mata kuma ki kula da ita kamar yadda zan kula da ita, sannan bana son a cikin gida kowa yasan na zo bangaren nan." "In Allah ya yadda babu mai sani." "Yawwa." Hajja ta faɗa tana barin ɓangaren cikin sauri ( domin a al'adance uwar miji bata zuwa ɓangaren danta musamman a irin wannan lokaci da Yarima aka sha love da Salmah, yanzu sai ka ji an fara maganar mutum a cikin gari.)

Bayan tafiyar Hajja da kyar da lallashi jakadiya kai Salmah bathroom, cikin ruwan nan mai zafi jakadiya ta sanya Salmah shiga, ko cikin ruwan zafin ban da hawaye babu abin da Salmah ke yi, sau uku jakadiya tana canza mata ruwa, aikam ta samu sauƙin raɗaɗin sai dai kafin su fita daga toilet har jikinta ya yi mugun gashewa da zazzabi.
Sai rawan sanyi take haƙora suna haduwa da juna, Salmah tana bayi don jakadiya ta barta ta yi wankan tsarki, ita kuma jakadiya ta sauya zanen dake kan gadon, ta cire wancan don haka gado daret Salmah ta nufa, kwanciya ta yi tana maida numfashi shayi mai zafi jakadiya ta kawowa Salmah, bata ta rika yi abaki tana sha, duk da bata sha mai yawa ba ta ce ta koshi, bayan ta gama sha jakadiya ta ciro mata kayan sawa a wardrop ta sanya, gaba daya kwanciya take son yi sai dai zazzaɓin kara gaba yake ga babu magani a bangaren don haka sai kawai ta ba Salmah babban blanket dake gefen gadon ta ce ta kwanta tana zuwa, fita ta nufin wajen Hajja ta amso mata magani.
Cikin sauri Yarima dake zaman jiran fitowar jakadiya ya mik'e "Jakadiya ya jikin Salmah ta farfaɗo kuwa?" A rude yake tambayar, domin ɗazun da Hajja ta fita ko da ya tambayeta harara ta banka masa ta wuce. "Kwantar da hankalinka Magajin Sarki Salmah ta farfaɗo, sai dai akwai zazzaɓi a jikinta, magani zan amso mata wajen Hajja." Murmushi ya saki wanda ya k'ara fito da asalin kyawunsa ya ce "Masha Allah! Allah na gode maka, sannu jakadiya da k'ok'ari, akwai magani a cikin dakin Yanzun idan na shiga zan bata." Babu kunya Yarima ya gama furucin yana niyyar shiga cikin bedroom din.
"Magajin Sarki don Allah ka bita a hankali, domin dai Salmah yarinya ce karama, karka rika mata ta karfi." Kunya ce ta kama Yarima da sauri yakai hannun kan sumar kansa yana shafawa ya ce "to." Sannan ya shige can ya hangota kwance rufe da blanket, bai hau gadon ba sai da ya dauko pracitamol da ruwa sannan ya hau gadon tare da ya ye blanket din, jikinsa ya jawota ya ji zafi zau tausayinta ya kama shi sosai, dagota ta yi cikin tausayawa ya ce "Ummuna buɗe ido ga magani ki sha." "Hamma sanyi jikina ciwo yake don Allah ka rufeni." A wahalshe take magana. "To ki sha magani sai na rufeki." Da sigar lallashi ya yi furucin, da kyar ya samu ta sha maganin sannan ya rungumeta jikinsa a hankali yake matsa mata jikin, dumin jikinsa yana shiga jikinta nan da nan bacci ya dauke ta.
Jin saukar numfashin ta a hankali yasan bacci ya kwashe ta, gyara mata kwanciya ya yi ya matsar da sumar da suka rufe mata fuska, tsira mata ido ya yi cikin so da kauna, soyayyar ta da sha'awar ta suna ci gaba da ratsa duk ilahirin jikinsa, kiss ya manna mata a kumatu ya ce "ina sonki Ummuna." A haka bacci ya dauke shi.
Kiran sallar farko ya farkar da Yarima, a hankali ya raba jikinsa da nata murmushi ya yi kamar tana kallonsa, domin jin zazzaɓin ya sauka toilet ya shi, wanka ya fara sannan ya dauro alwala, ko da ya fito kan sallaya ya hau ya fara nafilfili duk addu'oin da ya yi akan Salmah suke, babban burinsa kasancewa da ita, bai tashi akan sallayar ba sai da ya yi sallar asuba, har alokacin Salmah bata farka ba ganin time ɗin sallah na neman wuce wa sai kawai ya nufi gadon, cikin bargon ya shiga tare da jawota jikinsa a hankali yake magana "Ummuna lokacin sallah ya yi tashi ki yi sallah Salmatyy." Buɗe ido ta yi cike da bacci bakinta ɗauke da addu'ar tashi daga bacci, idonta ta sauke kan Yarima wanda ke sakar masa murmushi "Hamma bacci ka bari sai anjima." "No! Ummuna ki daure ki yi." Shagwaɓe fuska ta yi kamar zata yi kuka, ganin haka da Yarima ya yi sai kawai ya dauketa sai toilet ruwa mai zafi ya haɗa mata ciki ya sanyata, kamkameshi ta yi cikin azaba hawaye suna saukowa kan fuskarta, buɗe cinyoyinta yake ruwan suna shiganta yana mata kalami masu sanyaya zuciya.
A haka ya gama gasa mata jiki, wanka ya yi mata sannan ta yi alwala, babu laifi sauki ya samu domin har tana iya takawa da kafarta, sallayar dake shimfiɗe ta hau ta tayar da sallah, bayan ta idar da sallah ta yi kasa da murya tana faɗin "ina kwana Hamma, an tashi lafiya?" Sai da ya yi murmushi ya kafin ya k'arasa inda take ya dagota ta shige jikinsa, sannan ya ce "Lafiya lau Ummuna, ya gajiya ko dai Salmatyy bata gaji ba mu koma?" Sinne kai ta yi tana karamin murmushi ta yi ba tare da ta iya faɗin komai ba don sosai maganar Hamma Yarima ya bata kunya.
Sama Yarima ya yi da ita sai kan fadaden gadonsu, da sauri Salmah ta zabura zata sauka "me ya faru?" Yarima ya tambaya da mamaki. Hawaye ne suka fara saukowa saman kuncinta, jikinta babu inda baya rawa ta ce "Don Allah Hamma ka yi hakuri wallahi bani da lafiya." Da kuka rashe- rashe Salmah ta k'arasa maganar. "Babu abin da zan yi maki Ummuna kwantawa za mu yi mu yi bacci, kwantar da hankalinki." "To." Ta amsa badan ta yadda da abin da ya faɗa mata ba, cikin hikima da dabara ta zame jikinta daga nashi can gefe ta matsa tana sauke numfashi, domin sosai ta firgita da Yarima a daren jiya, shi kam murmushi ya yi ganin yadda ta koma nesa da shi bai matsa inda take ba sai da ya ga bacci ya kwashe ta, kanta ya daura a kirjinsa har tana sakin ajiyar zuciya, sumar kanta ya shafa tare da yi mata kiss, rigar jikinta ya cire sannan ya manta da da jikinsa a haka bacci ya dauke shi. Ba su farka ba sai taran safe, sosai Salmah ta yi mamakin ganin ta a jikin Yarima ai da sauri ta zame jikinta, bata tsaya a bedroom ɗinsa ba ta wuce nata, wanka ta sake sannan ta fita falo domin yunwar dake azalzalar ta, a zaune ta samu Yarima a falon fuska ɗauke da murmushi bude mata hannu ya yi alamar taje gare shi, babu musu ta je ta shige kirjinsa.
"Allah ya yi wa Salmah albarka." "Amin." ta amsa tana kara lafewa a kirjinsa.
"tashi ki yi break bana son kina zama da yunwa." "To Hamma." Salmah ta amsa tana gyara zama, break ɗin suka yi bayan sun gama Yarima ya mike yana faɗin "bari na shiga wajen su Hajja ki kwanta ki huta kin ji ko?" Gyaɗa masa kai ta yi ta ce "A dawo lafiya." "Amin Ummuna." Yarima ya amsa cike da jin dadi. Tana ganin ya fita ta fara gyara ɗakunan da falo zuwa kici, babu wani bata lokaci ta kammala komai zamanta kenan a kujera Yarima ya shigo "sannu da zuwa." Ta faɗa tana rungumoshi. "Yawwa Ummuna ga su Karima da Zaituna zasu taimaka maki da aiki." "To Hamma ya Hajjata?" "Tana lafiya lau ta ce a gaida Salmah." "Ina amsawa ta bashi amsa lokacin da suke shiga bedroom ɗinsa, bata fi minti biyar da shiga ba ta fito, a kofar falo ta same su tsaye suna jiran umurnin ta "ku shigo mana Zaituna." Salmah ta faɗa da fara'a.
"Barka da wannan lokacin uwar dakinmu." A ladabce suka yi maganar. "Barkammu dai sannunku, ku k'araso daga ciki." Babu musu suka shiga, nan da nan suka shiga aikin abincin. ( A al'adar masarautar su, duk ranar da Ango ya kwana da matarsa matuk'ar ta kawo mutuncinta gidan sa, da safe ango zai sanya a turo masa Bayi biyu bayan ya yowa amarya cefane mai yawa, za ta yi girki mai yawa kala daban-daban a kaiwa iyaye wannan shi zai nuna amarya ta karbi ragamar ango da danginsa sai ta yi tsawon kwanaki bakwai tana girki safe da rana da kuma dare, ranar da ta cika kwana bakwai sai Uwar miji ta yanke hukunci ko amarya ta ci gaba da girka masu abinci ita da mijinta, ko kuma uwar mijin ta hutar da ita daga yin girki a rinka kawo masu daga babban gida, sai ko abin da ta yi marmari shi zata rika girkawa.)
Karfe sha biyu suka kammala komai ciki har da tsaftace wajen da suka yi girkin, su Zaituna ta sanya suka kwashi abincin zuwa ɓangaren Hajja da Yawuro, lokacin da abincin ya isa ɓangaren Hajja wani irin farin ciki ne ya rufeta, duk da bata nuna haka a fili ba amma zaka iya fahimta ta dalilin farin cikin da ta yi.
Salmah kam bayan sun gama aikin wanka ta yi ta canza kaya ta feshe jikinta da turaruka masu kamshi, sannan ta nufi dakin Yarima kwance ta same shi yana ta sharan bacci, hayewa gadon ta yi ta ɗaura fuskarta akan tashi tana hura masa iska a fuska.

Wayyo! Yaseen na gaji fa🤪

Team Ummuna Salmah
Vote me
Comment
& Shere on wattpad

KYAKKYAWAR ALAK'AWhere stories live. Discover now