Page 26

776 43 3
                                    

👉🏼💍 *KYAKKYAWAR ALAK'A*💍👈🏼

*REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S* _P.M.L_

                      ©
     *ZULAYHEART RANO*
*My wattpad username zulayheartrano89*

*STORY AYSHA WAZIRI*

*Oh! Allah ina baku hakuri fa fan's, aradu lamarina sai addu'a, yin typing ya zama babban aiki a wajena, sai dai duk da haka masu bibiya basu fasa ba, kullum cikin tambaya suke to yau dai ga yi na yi maku duk da dai babu yawa, sai kun dai ci gaba da hakuri fa.* 😅😅😅

           *26*

"Yawwa ƙawata yin haka kawai shine samun farin cikin ki." Rauda ta kara jaddada mata.

Gyada kai Nuwaira ta yi domin ta gamsu da shawarwarin Rauda, dari bisa dari. Sun ci gaba da hira har tsayin lokaci rabi duk akan ala'karta da Yarima ne, sannan suka yi sallama.

Shi kam Yarima bai ma san ana yi ba, harkokin sa kawai ya sanya a gaba tunda ya dawo, domin wasu ayyuka ne suka dumfaro shi daga ofis, aiki ne na ci gaba domin kuwa karin girma zai samu daga office din na su, shi yasa yake aiki babu kakkautawa.

Bangaren Salmah kam rayuwa take mai daɗi a garin Ningi, tattali da kula kawai take samu daga wajen Hajja da sauran yan'uwa, sosai ta yi kyau jikinta ya murje.

Yanzu cikin jikinta ya shiga wata na tara, a koda yaushe za ta iya haihuwa, komai na shirin haihuwar sun kammala sai haihuwar kawai suke jira.

Salmah ce kwance a bangaren Hajja, ya yin da Areef ke zaune kusa da ita yana wasa da kayan wasansa, wayarta ce ta fara ruri don neman agaji, ɗan mik'ewa ta yi da kyar tana cizon lebe, don yau sam bata jin dadin jikinta, hannu ta kai tare da dauka ta furta "Assalamu alaikum."

"Wa'alaikums Salam hajiyata." Yarima ya amsa daga daya bangaren.

Gaisar da shi Salmah ta fara cikin ladabi, shima cike da farin ciki ya amsa sannan ya fara tambayar ta nauyin jiki.

"Alhamdulillah Hamma gamu nan dai wallahi."

"To Allah ya raba lafiya."

"Amin." Ta amsa.

"Ina Areef ne Ummuna?"

"Ga yi nan wasa ya ɗauke hankalinsa, baima san dawa nake waya ba." Ta bashi amsa tana kallon Areef din.

"Areef ga Bobbo yana magana... Ai tun bata gama rufe baki ba har ya watsar da kayan ya amshi wayar, murmushi kawai take yi jin yadda ake hira da Hamma Yarima da Areef, duk da maganar Areef din ba sosai take fita ba, amma tana fahimtar abinda yake fada, sun dade sosai kafin suka yi sallama.

******* *********** **********

Zaune suke gaban mai yanzu-yanzu, gyara zama Nuwaira ta yi ta soma faɗin

"Wato abin da ke tafe damu shine, akan wani..." Bata gama rufe baki ba ya yi saurin katse ta.

" Kar ki ce komai yammata nasan abinda ke tafe daku, ko ba akan saurayi ba ne? Ke kina sonsa shi kuma baya sonki ko?"

Da sauri Nuwaira ta daga kai cike da mamaki.

"To ki kwantar da hankalinki, bukatar ki zata biya, sai dai akwai matsala babba."

"Wacce irin matsala kuma mai Yanzu-yanzu?" Bakin Nuwaira har yana rawa ta yi tambayar.

"Eh! Akwai matsala, musamman ta bangaren yaron, domin kuwa a yadda taurari suka nuna, yaron yana tare da albarkar iyaye, ma'ana ba kowane iri magani za a masa ya kamashi ba, amma kada wannan ya dameki zamu san yadda zamu yi, in dai kina da kudi"

KYAKKYAWAR ALAK'AWhere stories live. Discover now