COMPLETE

201 10 0
                                    


Tun da Hajja ta ja hannun Salmah ba ta sake ta ba har sai da suka shiga bedroom, a bakin gado ta zaunar da ita sannan ta fara magana cikin kwanciyar hankali “Kina jina ko Salmah? Ki ba ni haɗin kai wajen kwato maki hakkinki, ba wai ina son rabaki da mijinki ba ne a'a ina yin haka ne don nemar maki mutuncinki, abin da nake so dake shi ne karki kuskura ki sakar ma Yarima fuska balle har ya samu damar da zai shige maki, ki ɗauke masa wuta karki bari ya ji daɗi a wajenki nima ba zan sarara masa ba har sai ya yi hankali kin ji ko?” A ladafce Salmah ta amsa, don ta tabbatar Hajja ba cutar da ita za ta yi, domin duk son da take yi mata bai kai kwatan wanda take yi wa Yarima ba, tabbas tana son kwato mata 'yanci ne don haka ta sanya a ranta za ta yi wa Hajja biyayya ko da ita za ta shiga wani halin mara daɗi.
  Ai kam sun fara aiwatar da abin da suka yi niyya, domin duk wata hanya da Yarima zai bi ya ga Salmah Hajja ta toshe ta, kwata-kwata ba ta barin Salmah fita nan da can sai idan tare za su fita, shi ma sai dai ya hangesu daga nesa kuma ko kusa Salmar ba ta ma sakar masa fuska, shi ji yake ma kamar ta tsane shi ma gaba ɗaya. Kullum sai ya gwada sa'ar shi na shiga falon Hajja a zuwan zai shiga bedroom da Salmah ke ciki amma sai ya yi karo da Hajja zaune, duk kuwa da irin sammakon da ya doka a falo yake iske Hajja, ko kuma suna tare a cikin daki dole jiki babu ƙwari yake barin ɓangaren don kallon gargadi da Hajja take yi masa kaɗai ya fi komai daga masa hankali. Su dai yaransa kullum yana tare da su don ba a yi masa iyaka da su ba, sai da matarsa farincikin sa kawai Hajja ke son raba su, a daidai lokacin da ya ke tsananin buƙatar ta.
  Kai wa da komowa kawai yake tsakanin dakin barcin sa da falo, gaba daya ya tsani zaman garin Ningi to kuma baya son komawa Bauchi matuƙar ba tare da Salmah ba, kamar an tsikare shi ya miƙe zumbur tare da nufa ɓangaren falon zuciyarsa tana faɗa masa kawai ya shiga koma me zai faru ya faru. Ko sallama bai yi ba don ma kar a samu matsala da su Areef da Khairat wanda suke wasa a falo ya fara karo rungume yaran ya yi cikin so da kauna, a duniya idan aka cire iyayensa da Salmah yaran su ne mutane na uku da yake jin tsananin sonsu.
   “Ina Nennen ku?” Ya tambaya bayan ya yi masu kiss a kumatu, Khairat ne ta nuna masa ɗakin da Salmah ke ciki, ya yin da Areef ke faɗin “Tana ciki.” “Hajja fa?” Ya tambaya da sauri. “Tana wajen Maimartaba.” wani sanyin daɗi ya ji a ransa da bai samu Hajja a ɓangaren ba, da sauri ya fara magana “Ku je ɓangaren Maimartaba ku gaisar da shi kun ji ko? Idan na dawo zan kai ku wajen wasan yara.” Jin ya ce zai kai su wajen wasan yara ai da gudu suka kwasa, dariyar jin daɗi ya yi suna fita shi ma ya cusa kai cikin ɗakin.
  Lokacin Salmah ta fito daga toilet kenan jikinta daure da ƙaramin towel wanda iyakarsa cinyarta, tana zaune a kan dreesing mirror alamu sun suna wanka ta fito, daga ƙofa Yarima ya tsaya yana ƙare wa Salmah kallo tun daga sama har ƙasa, kamar yau ya soma ganinta.
  “Hajja tun ɗazun nake jiranki ki dawo Adda Khadijah sai kirana take ta yi fa.” A shagwaɓe ta gama maganar duk a tunaninta Hajja ce ta shigo, jin ba a yi magana ba ya sa ta juya da sauri cikin mamaki. Karaf! Idonsu ya haɗu da na Yarima ai take jikinta ya ɗauki rawa. A hankali cikin nutsuwa Yarima ke takowa ita kuma Salmah ganin haka sai ta fara ja da baya har sai da ta cimma jikin bango, ganin ba sarki sai Allah sai ta fara magana “Hamna karka ƙaraso.” Ta faɗa tana runtse ido. Ko a jikinsa don yana zuwa matse ta ya yi a jikin bangon yana faɗin “Mene ne abin guduna Ummuna? Nine fa Yarima mijinki Uban 'ya'yanki, shi kenan ke da Hajja kun sakani a tsakku sai azabtar da zuciyata kuke yi, kodayake bana ganin laifin Hajja laifinki nake gani, don ita Hajja kullum tana tare da mijinta ke kuwa sai dai ki kwana da tunanina don na san karya ne ki ce ba kya tunanina.” Kauda kai ta yi gefe ta ce  “Ni Wallahi bana tunaninka, to ai ba yanzu muka raba jaha ba ka ga kuwa babu yadda za a yi na zauna yin tunaninka, tun da dama can kai ba nawa ba ne ai kai da Nuwaira kuka dace.” Cikin rashin kunya take ba shi amsa. Shi kam ya ma kasa cewa komai sai kawai ya tsareta da ido, ajiyar zuciya ya sauke ya ce “Salmah kenan wato ke ba za ki bani uzuri ba ko? Kema kin san ai da ba haka nake ba.” “Babu wani nan kuma ni ba zan koma gidanka ba ka can ku ƙarata da matarka don da ita kuka dace, ina nan ina jiran takar...”  A zafafe ya katseta ta hanyar daga mata hannu, don maganar ta yi masa zafi sosai ya ce “Ba zan sakeki ba, wallahi idan ma mafarki kike yi to ki farka don wannan hannanun ba zai iya rubutawa Salmah takarda matukar ta sakin aure ce." “Amma ai an iya ɗaga shi da sunan marin fuskar Salmah ko?” Ta yi saurin katse shi. Wani irin wawura ya yi mata har sai da towel din jikinta ya kwance, bai tsaya jiran komai ba ya haɗe bakinsu waje guda, ya fara aika mata da saƙonnin sa masu saurin mantar da ita duniyar da take, idan ba haka ya yi mata ba ya lura so take ta caza masa ƙwaƙwalwa. Da ƙyar Salmah ta kwaci kanta tare da sakar masa kuka tana faɗin ni ka kyale ni “Gidan Adda Khadijah zan je shi ne don mugunta kake son hanani.” “Ba za ki je ba.” Ya faɗa a fusace. “Sai na je kuma bari Hajja ta zo sai na faɗa mata.” “Ce mata za ki yi na zo har na yi maki kiss? Kai Wallahi da za ki faɗi haka dana ji daɗi don ta tabbatar sonki ko girgiza daga zuciyata bai ba, kin ga sai ta tattara min matata ta ba ni abina.” Ya gama maganar yana sakin murmushi. Sabon kuka Salmah ta fashe masa da shi tana cewa “Ni dai wallahi sai na je gidan Adda.”
  “To shi kenan na ji amma sai idan tare za mu je, idan kuwa ba haka ba babu in da za ki je, kuma ki sani daga yau wasan ya ƙare a fannin ku, yanzu ni zan koma mai bayar da umurni kuma dole a bi.” Gungunai ta fara yi masa tana yi tana murguda masa baki aiko bai jira komai ba ya ƙara haɗa bakinsu waje ɗaya, wani irin sarrafa yake yi wa harshen ta wanda ya sa ta manta kowa da komai sai Yarima kawai da abin da yake yi mata tsayuwa ma ta gagaresu sai zubewa suka yi a kan gado, sosai ta sakar masa jiki suna niyyar lulawa wata duniyar. Hajja wacce sam ba ta san Yarima yana dakin ba, ta shigo ne domin ganin ko Salmah ta shirya sai kawai ta yi kyakkyawar ganin Yarima yana rungume da Salmah, ai da sauri ta juya tare da sakin ƙofar ya ba da sautin bamb! Wani ƙarfi ya zuwa Salmah don haka ta hankade Yarima tare da rugawa toilet tana mayar da numfashi.  Shi kam Yarima a firgice ya miƙe yana sosa keya sumi-sumi ya fita daga ɗakin, da kallon takaici Hajja ta bi Yarima.
   Salmah wacce kunyar duniya ta isheta, da ƙyar ta murzawa idonta toka ta fita falo bayan ta shafe kusan awa biyu cikin daki. “Wai Salmatyy hala kin fasa zuwa gidan Khadijah ne?” Hajja ta jefa mata tambayar tana cigaba da danna wayarta.
  “Em-umm dama dai Hamma Yarima ya ce ba zan je ba.” Ba ta san lokacin da bakinta ya buɗe har ta soma ba Hajja amsa ba, har sai da ta gama fada tukun.
  “Ya yi kyau.” Abin da Hajja ta ce kenan ta ja bakinta ta yi shiru. Tsabar kunya tun da Salmah ta sadda kai ba ta kuma magana ba, su Areef ne suka shigo da gudu suna kwallawa Salmah kira “Nenne Bobbon Areef ya ce yana jirankin mu je gidan Nenne Khadijah.” Ba ta ɗago kai ba haka kuma ba ta amsa ba, don kunyar Hajja take ji sosai. Duk da cikin ranta tana son zuwa amma fa ba za ta iya tashi a gaban Hajja ba.
  Tabe baki Hajja ta yi don ta daɗe da gama sanin halin Salmah, miƙewa ta yi tana faɗin “Salmatyy zan shiga kuma kwanciya zan yi kar a tashe ni.” To Salmah ta amsa, sannan ita kuma ta wuce. Hajja ta yi haka ne don ta fuskanci tana son bin mijinta, sai dai kunya take ji ta daɗe da sanin Salmah tana yi mata biyayya, zuwa yanzu kuma ta sauka da ga fushin da take yi ga Yarima sai dai ba ta nuna masa haka ba. Ganin Hajja ta wuce Salmah har rawa ta fara na jin daɗi wanda ba ta san Hajja tana kallonta ba. Areef ne ya kuma dawowa yana sanar mata Bobbon shi yana jiranta, Yaron ta aika ya dauko mata gyale.
  Ba su wuce gidan Adda Khadijah ba sai da suka biya suka gaisar da Baba Waziri da Maimartaba, lamarin da ya yi masu daɗi, sannan suka tafi. Duk da Hajja ba ta sakar masa fuska ba, sannan bai samu kasancewa da Salmah ba don ko ya nemi amincewar ta ba ta yarda saboda cika alkawarin da ta ɗaukarwa Hajja, Yarima ya yi kokarin sosai wajen wanke kansa da ƙara faranta wa Hajja rai ta hanyar sayan wani Katafaren fili wanda za a ginawa Salmah gida a garin Ningi, wanda Salmah ba ma san ana yi ba, don Yarima bai faɗa mata ba Hajja ma haka. gida ake ginawa na gani na faɗa Yarima bai bar garin ba har sai da aka fara gini, da zai koma sai ya damƙa komai hannun Hamma Ɗan Waziri. Aikan ana gina gida irin na zamani wanda kaf garin Ningi babu kamar sa. Yana shiga Bauchi abin da ya fara aiwatarwa shi ne kai wa Iyayen Nuwaira takardar sakinta, wanda ya rubuta mata uku ringis a nan yake samun labarin guduwar Nuwaira daga asibitin mahaukata da aka kaita, domin haukan na ta ya ƙara yawa fiye da na farko,  Yarima dai shi ko a jikinsa don wannan ba damuwarsa ba ce. Transfer ya nema don ya tsani zaman garin Bauchi gara ya koma Ningi ko Abuja, bai faɗawa kowa yana nemi transfer ba sai Hamma Ɗan Waziri, kuma ya ce masa kar ya sanar da kowa har sai komai ya kammala.
  Ba ɗauki tsawon lokaci ba aka kammala gina gidan, ku san komai na gidan an zuba shi gidan ya tsaru iya tsaruwa. Salmah zaune suna hira da Hajja Hamma Ɗan Waziri ya shigo bayan sun gaisa Ɗan Waziri ya dubi Salmah ya ce “Ummuna za ki rakani wani waje, muna jiranki da Nennen littel Salmah a mota.” To ta amsa.
   “Hajj...” Tashi ku tafi bana son dogon magana, dariya kawai Salmah ta yi tana miƙewa ta yarda Hajja ta fi kowa iya warwara, tun ba ta ji abin da za ta ce ba har ta katseta. A cikin mota ta samu Adda Ameena da su Areef don haka ita ma shiga ta yi Ɗan Waziri ya ta yar da mota, ba su zame ko ina ba sai gaban wani haɗaɗɗen gida mai masifar kyau, tun daga harabar gidan Salmah ta fara santi, ta ji Ɗan Waziri ya yi hon maigadi ya bude kofa “Wowww!” Salmah ta faɗa tana ƙara kallon gidan.
  “Kai Hamma amma wallahi gidan nan ya huɗu ta ko ina, yaushe ka gina gidan nan ban sani ba?” Gaba ɗaya suka tuntsure mata da dariya, a haka suka shiga cikin falon gidan tsabar haɗuwa kamar Salmah za ta zauce, ɗaki daki sai da suka shiga duk inda suka shiga sai Ɗan Waziri ya ce “Ummuna nan ya yi?” Baki na rawa Salmah ke ba shi amsa da eh Hamma gaskiya Adda Ameena kin ji daɗi wannan gida kamar a Turai, ina ma a ce ni ce a gidan nan da hmmmm! Sai kuma ta yi shiru. Adda Ameena dariya take yi wa Salmah ganin yadda ta dage tana santi gidan. Haka suka ci gaba da zaga gidan a ɓangaren da aka warewa yara aka zuba masu kayayyakin wasa suka yada zango, wajen ya yi kyau da tsaruwa sosai. Suna gidan har aka yi sallar magriba, wani gefe na zuciyarta ya cike yake da tunanin Hoton ta da Yarima wanda yake manne a falon gidan, ba ta manta lokacin da aka yi masu hoton ba, lokacin tana da karamin cikin Khairat suka je wani wajen shakatawa a can aka yi masu hoton suna cike da zallar farin ciki, to me ya kawo shi nan? Shi ne tambayar da take yi wa zuciyarta, ta dai ta san da a ce Yarima ya gina gidan da zai sanar mata, to ko dai mamaki yake son baki? Wata zuciya ta kuma jefa mata tambaya. Daga kafaɗa kawai ta yi don ba ta son ta ƙarfafawa zuciyarta abin da ba haka ba ne.
       51
Bayan sun dawo Salmah sai ba Hajja labarin gidan take yi “Kai Hajja amma wallahi gidan Adda Ameena ya haɗu iya haɗuwa, ina ma a ce ni ce na samu gidan don gidan ya gama tafiya da imanina.” dariya Hajja ta yi tana kallon Salmah don wani lokacin yarinyar ta fiye wauta.
  Hajja tana niyyar bata amsa suka ji sallamar Yarima hannunsa riƙe da Khairat wacce ya yi karo da ita a harabar sashin. Cikin ladabi ya fara gaisar da Hajja, fuska sake ta amsa sannan Salmah ta fara gaisar da shi. Bayan ya ci abinci suna hira da Hajja ya dubi Salmah ya ce “Ummuna zo mu je ki rakani gidan can mu ga gidan yadda yake.”
  “Gidan Hamma Ɗan Waziri? Kai Wallahi Bobbon Areef gidan nan ya haɗu ɗazun mun je da su Adda Ameena.”
  “To mu je nima na ga gidan.” Ya faɗa yana miƙewa. Shiga Salmah ta yi ta dauko gyale, har za su wuce Hajja ta kira su nusiha ta fara yi wa Yarima da Salmah, tana cigaba da jaddada masa da ya ji tsoron Allah, ita kuma ta zama mai biyayya. Jikinsu ya yi sanyi musamman Salmah da ta kasa fahimtar in da maganar ta nufa.
  “Kafin ku tafi ku je ku gaisa da Maimartaba da Babanku Waziri, gobe zan sanya a kawo waɗanda za su riƙa tayaki hidimar gida, bayan Zaituna za aka karo maki da wasu ma, Khairat kuwa sai kun ganta Allah Ya Yi maku albarka.”
   “Amin.” haka ma wajen su Maimartaba da Baba Waziri nasihohi suka yi masu mai ratsa jiki, daga can suka shiga wajen Yawuro ita ma dai kwatankwacin irin nusihar Hajja ta yi masu sannan suka tafi. A ciki mota Salmah shiru ta yi don ita kam jikinta a sanyaye yake, duk da wani gefe na zuciyarta cike yake da farin ciki yau za su kasance da Yarima a gida daya gado daya filo ma ɗaya, dama ta yi kewarsa sosai kullum tana fatan Allah Ya nuna mata ranar da za ta kuma kasancewa da shi. Suna shiga gidan Yarima da kansa ya buɗe mata kofar Mota sannan suka shiga, a falo suka yada zango ta ga ƙarfin halin Yarima har yana kunna tv. Kallon agogon da ke manne jikin bangon falon ta yi ta ga ya nuna mata ƙarfe tara har da mintina ta ce “Hamma wai ba za mu tafi ba ne?”
  “Ina?” Yarima ya tambaya yana kallonta.
   “Gida mana.”
  “Bayan wannan da muke ciki?” Ya tambaya yana kallonta.
  “Nan kuma? Nan ba gidan Hamma Ɗan Waziri ba ne?”
   “Na Salmah dai matar Yarima Hafiz, Nennen Areef.” Ya gama maganar yana dage mata gira ɗaya. “Ban gane ba?” Ta faɗa tana miƙewa ta nufo shi.
   “Yes! Wannan gidan mallakin Ummu Salmah ne Matar Yarima Hafiz, dama ina son ba ki mamaki ne shi ya sa har aka gama gina gidan ba tare da na sanar dake ba.” Tsabar jin daɗi Salmah ba ta san lokacin da ta rungume Yarima ba, shi ma cikin farin ciki ya yi mata kyakkyawar runguma. A wannan rana Yarima sun sha soyayya kamar ba za a mutu ba. A gurguje bayan wata biyu da komawar Salmah har ta kuma samun ciki, wannan karon cikin nata mai laulayi ne sosai ta wahala kafin ya yi kwari, wata tara na cika ta haifi ɗanta namiji wanda ya ci sunan Maimartaba, zuwa yanzu tuni Yarima da Salmah suka manta da duk wani damuwa da suka taba shiga, yanzu hankalin su kwance yake ba sa da wata damuwa arzikin Yarima sai ƙaruwa yake, hutu ya gama zama jikin Salmah da yaranta.

  Bayan shekara goma
Salmah ce zaune gabadaya yaranta sun zagayeta, Areef wanda yake zuwa lokaci zuwa lokaci, yana da shekara goma sha daya, sai Khairat mai shekara goma, kusan kansu daya sai Sultan da Nihal suma kusan kansu guda sai wanda ta ya ye kwanan nan mai sunan Yarima. Duk cikin yaran Khairat ce kawai ba ta fiye magana ba, tsabar muskilanci har ta fi Yarima jin jinin sarauta, sabanin sauran da su da kowa ma sake jiki suke yi, sun kaure da hayaniya Salmah ta biye masu har ba wanda ya ji karan wayar Salmah, Khairat ce ta mike tare da nufa wajen ganin sunan Bobbonta ya sanya ta ɗauki wayar da sauri tana faɗin “Allah Ya ƙarawa Bobbon Khairat lafiya.”  “Tare da ke Hajjata ina fatan kin yini lafiya?” “Alhamdulillah! Amma gabaɗaya muna kewar Bobbo.” “Karku damu ina nan tafe gareku kwana kusa.” “Allah Ya kawo mana kai lafiya.” “Amin Hajjata, mikawa Nennenki wayar.” To ta amsa tana mikawa Salmah wayar. “Mijin Ummu Salmah Bobbon Areef.” Ta faɗa tana saki dariya bayan ta bar falon. “A'a gyara magana dai Bobbon Areef haka yake mijin mace huɗu.” Wani faduwa gaban Salmah ya yi, don take ta tuno da irin zaman da suka yi da Nuwaira, sai kuma ta ce “Ai an wuce wannan babin ba mai iyawa da kai sai ni.” “Haba 'yammata kin san kuwa yadda yammata suke bina a garin Abuja? (Da yake tuni Yarima ya koma aiki Abuja kamar yadda ya buƙata) ya cigaba shi ya sa na yanke shawarar faɗa maki tun tafiya ba ta yi nisa ba.” Yarima ya gama magana yana tsuke fuska kamar Salmah tana kollonsa. Bugun kirjin Salmah fa ya tsananta har tana sa hannu tana dafe kirjin, maganar Yarima ya kuma ta yar mata da hankali in da yake cewa “Ga matar da zan aura ku yi magana muna tare da ita a office.” Kafin ta yi wani yunkuri sai kuwa ta ji muryar mace tana gaisar da ita ba ya shiga kunnenta, ba ta san lokacin da wasu hawaye masu zafi suka fara zubo mata ba.” “Wai ya ba za ki yi magana ba ne? Yarima ya faɗa bayan ya amshi wayar, banza ta kuma yi masa hawaye suna cigaba da sauka kan fuskarta.
   “Afuwan Nennen Areef da wasa Yarima yake yi maki, ai daga ke babu wata wacce za ta kuma shigowa gidan nan da sunan aure, ya kawo mana ziyara ne shi ne ya ce bari ya gwadaki, ni sunana Abdallah amma ana kirana da Alhaji da matata Zainab BURINA, wacce ta fara ma ki magana, ina fatan za ki yarda da magana na?” Shi ne abin da ta ji wani yana faɗa bayan ya amshe wayar a hannun Yarima. Can kuma ta ji Yarima ya tuntsire da dariya ya ce “Amma Wallahi Salmatyy kin fiye kishi, ke yanzu a naki tunanin idan ba giyan wake na sha ba akwai wata mace da zan kalla da sunan aure? Bai jira amsar ta ba ya cigaba “Kamar yadda Alhaji ya faɗa maki na ya kawo mana ziyara haka yake, yanzu haka gani a gidansu dama na kira ne don ku gaisa da matarsa don na ga kusan halinku ɗaya, ki yarda da ni Ummuna.” Murmushin jin daɗi ta saki ta ce “Wallahi Bobbon Areef ka kusa sanyawa jinina ya hau, da gaske ina matuƙar kishinka bana son na ga wata mace ko da yarinya ce ta kusanci wajen da kake KYAKKYAWAR ALAƘAR mu da kai ba za ta taba rabuwa ba, ba ni Kawata mu gaisa.” Da farin ciki take maganar, sosai Yarima ya ji daɗin maganar Salmah.
   Sun gaisa sosai da Zainab kuma take suka kulla ƙawance, kamar dama sun daɗe da sanin juna. Lokaci ƙanƙani har shakuwa mai ƙarfi ta shiga tsakanin Salmah da Zainab, kullum suna maƙale a waya suna ba juna shawararwari masu amfani.
Soyayya tsakanin Salmah da Yarima kullum ƙara gaba yake. Kuma tuni Yarima ya mayar da Salmah makaranta don yana son ta cika burinta na zama cikakkiyar likita, ai kam da taimakon Allah da addu'ar Iyaye Salmah ta kammala karatun ta ciki nasara, lokacin da aka yi masu yayen zama likita Salmah a asibitin ta ta fara aiki wanda Yarima da taimakon Maimartaba suka gina mata, asibitin da aka gina shi don taimakon talakawa, ai kam talakawan Ningi sun ji dadi sun kuma sa albarka.
  Sunan asibiti H&S Wato Hafiz da Salmah.

Tammat Alhamdulillah! A nan na kawo karshen wannan labarin KYAKKYAWAR ALAƘA, daidan dake cikin Allah Ya ba mu ladansa, kuskuren dake ciki kuma Allah Ta'ala Ya yafe mana, sai kuma Allah Ya haɗamu a wani sabon labarin.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Jun 16, 2023 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

KYAKKYAWAR ALAK'AWhere stories live. Discover now