Page 17

1.1K 61 5
                                    

👉🏽💍 *KYAKKYAWAR ALAK'A* 💍👈🏽

                         ©
     *ZULAYHEART RANO*
*Wattpad username zulayheartrano89*

*STORY AYSHA WAZIRI*

                    *17*

"Da gaske ki ke Ummuna cikinna nan?" Da zallar farin ciki da mamaki Yarima ya yi tambayar yana kara rungume Salmah. A hankali ta gyada masa kai alamar "eh." Murmushi ya sakar mata mai kyau ya furta "Alhamdulillah! Ina godiya ga Allah da yasa cikin na nan, insha Allah zan lallaɓa ki." Gama maganar ta yi daidai da shigarsu bedroom, tofa abin ya girmama don Yarima da Salmah Ali yaga Ali ne, iya soyayya sun gwada wa junansu haka kuma suka murji juna yadda ya kamata, amma an yi komai cikin natsuwa da lura, ba su saurarawa juna ba sai da suka ji ana kiran sallah, a gaggace Yarima ya yi wanka sannan ya fita Masallaci. Ita din ma Salmah wanka ta shiga ta yi sallah, yunwar da ta ji ya sanya ta zama gaban abincin da aka kawo masu ta zuba cikin plet ko jiran Yarima bata tsaya ba.
    Yarima kam bai shigo gidan ba sai bayan ya yi ishsha, a kwance ya samu Salmah da alama bacci zata yi "sannu da dawowa Hamma." Salmah ta fada tana tashi ta zauna. "Yawwa Ummuna har kin kwanta?" "Eh! Hamma bacci nake ji wallahi." "Tom amma a tashi a bani abinci." Yarima ya yi magana yana kwaikwayon muryarta, tashi ta yi tare da jawo flask din ta fara zuba masa "an gaida Ummuna bana son ki yi bacci da wuri har sai na kammala." "Kai Hamma don Allah!" "Eh! Mana." Haka Yarima ya yi ta ribatarta har sai da ya kammala cin abinci, ita ta taimaka masa ya kwashe kayan zuwa kicin sannan suka nufi bedroom, babu abin da Yarima ya yi mata don yasan ta gaji rungumarta kawai ya yi suka yi baccinsu.
     Washe gari bayan sun yi break suka yi wanka sannan suka ci gaba da soyayyar su, karfe huɗu Yarima ya umurci Salmah ta shirya su zaga gari, sosai ta ji dadi aiko cikin sauri ta shirya sai da suka biya suka gaida iyayensu kafin suka tafi, sun zaga gari sosai har sun kamo hanya zasu ko cikin gari Salmah ta riko hannunsa tare da marairaice fuska "lafiya kuwa Ummuna?" Cike da kulawa Yarima ya tambaya.
      "Hamma mu je wajen rafi Please." "Wajen rafi Ummuna?" Da mamaki ya yi tambayar. "Eh! Hamma." "Me zamu yo a rafi kuma yamma ta yi gaki ba ke daya ba." "Please Hamma wajen ne yake sanya ni nishadi." "Tom amma ba yau ba sai dai zuwa gobe don yanzu yamma ta yi." Dadi ne ya kama Salmah jin Yarima ya amince gobe zasu je wajen rafi. Daga nan gida suka yi a bangaren Hajja suka ci abincin dare ba su koma bangaren su ba sai karfe takwas, a gajiye likis suke don haka suna shiga Salmah ruwa ta watsa ta yi kwanciyar ta, ganin haka da Yarima ya yi sai ya barta kawai don baya son takura ta.
      Gari na wayewa karfe huɗu suka nufi wajen rafi, shimfidu na alfarma aka yi wa wajen da suka zauna, lallai ya lura Salmah tana farin ciki da zuwa rafi musamman yadda take ɗaukar kananun duwatsu tana jefa wa a ruwan, suna cewa tsulundum da sun fitar da wannan sauti sai ta saki murmushi, suna wajen har karfe shida sannan suka koma gida, cike da farin ciki Yarima ya kammala hutunsa ranar da zai koma bai tsaya wajen Hajja ba sai ya yi wajen Maimartaba, don har ga Allah so yake ya tafi da Salmah, yana tsoron Hajja ta hana shi tafiya da ita shi yasa ya nufi wajen iyayensa maza, ya ko yi Sa'a Hajja da Yawuro ma suna wajen suna tattaunawa, zama ya yi sannan ya fara gaisarsu cikin ladabi, da cikakkiyar fara'a suka amsa masa, ganin Hajja ya sanya ya yi shiru da faradar kudurinsa.
     "Ya aka yi ne Hafiz?" Baba Waziri ya yi tambayar cikin kulawa. "Ehm! Dama cewa zan yi don Allah a barni in tafi da Ummuna wajen aikina." A kunyace ya gama maganar. Murmushi Baba Waziri ya yi irin ta manya ya ce "ban da abin ka Hafiz don zaka tafi da Salmah har sai ka tambayi izini? Ai Salmah matarka ce kana da ikon zuwa ko ina da ita." "Abin da nagani kenan waziri, ni na ma rasa dalilin da tuntuni bai tafi da ita ba." Maimartaba ne ya yi furucin yana kallon Yarima. Kafin Yarima ya yi magana Hajja ta riga shi da cewa "ni na ce ya barta gida har ta kara girma, kun dai san har yanzu Salmatyy yarinya ce kuma bata saba da zama ita daya ba wannan ne dalilna." "Wannan ba hujja bane Hajja ki ba shi matarsa ya tafi da ita kowa da haka ya saba." Baba Waziri ne ya yi magana. "Ni ma abin da na ce kenan tun kwanaki amma Adda taki yadda, don Allah ki janye hukuncin nan zuwa yanzu kowa yasan akwai KYAKKYAWAR ALAK'A tsakanin yaran nan mu dai fatan mu Allah ya kara hade kansu." "Amin. Suka amsa gaba daya.
   Gyara zama Hajja ta yi sannan ta fara magana"da farko dai dole sai ya bi shardai na, domin ba zan bashi 'yata ba ya yi mata mugun abu, ta iya yiwuwa ganin ido yasa baya mata komai, shardai suke, matukar naga canji akan yadda na baka Salmah ta fannin komai ba zai kuma tafiya da ita ba, sannan ka tabbatar kana kula da ita fiye da yadda nake yi." Murmushi Yarima ya yi ya ce "Hajja na yi alkawari zan kula da ita fiye da tunani." "To Allah ya bada nasara." Amin a haka suka gama zaman cike da farin ciki Yarima ya bar bangaren, ko da ya koma zaune ya samu Salmah tana game a wayarsa, kyakkyawar rumguma ya yi mata yana fadin "Ummuna Hajja ta ce in tafi dake." "Da gaske Hamma?" Ta yi tambayar tana kara shigewa jikinsa. "Eh! Mana bari na hada kayan ki yanzun." Ya kara yana zame rikon da ya mata.
    Da kansa ya haɗa mata duk wani kaya da zata bukata, karfe sha biyu suka gama shirin su Salmah fa da ta tabbatar tafiyar da gaske ne sai ido ya raina fata, nan da nan ta fara kuka don gaba daya gidan tun daga kan Iyaye har yayyinta da yan uwanta tana da KYAKKYAWAR ALAK'A dasu, musamman da taga zata rabu da Hajja ita da bata taba yin kwana ɗaya ba tare da Hajja, ba yau ita ce zata tafi wani garin da sai ta yi wata bata ga Hajja ba, ai sai ta kara sakin kuka da kyar Hajja ta lallasheta tana fada mata wannan shi ne aure, Hajja tana ganin tashin motar sai da ta yi hawaye don ko kadan bata so rabuwa da salmarta ba, a haka suka tafi wannan karon direba ya ja motar Yarima sai aikin lallashi yake, mota biyu suka yi duk da nasu Zaituna da zasu rika taimaka mata da aikace-aikace, basu isa garin Bauchi ba sai karfe biyu da mintina, don tafiyar da motar dake kamar kar ta tafi haka Yarima ya umurci direban don kar a yi masa asarar ciki.
      Sakin baki Salmah ta yi ganin unguwar da suka shiga, unguwace ta masu kuɗi babu karamin gini a layin, gini ne da gani na manyan masu kuɗi wanda duniya tasan da su, bata gama mamaki ba sai da suka yi hon a wani katafaren get, da gudu getman din ya wangale kofar suka shiga ciki a farfajiyar gidan suka yi fakin motar inda aka tanadar domin motoci, kafin Yarima ya buɗe kofar har masu yi ma gidan hidima sun zagaye wajen suna jiran fitowar sa.
      "Hmmmm! Salmah ta sauke ajiyar zuciya ganin yadda Yarima ya wani hade rai kamar wanda bai taɓa dariya, glass din motar aka dage kawai ya bada umurnin su nuna wa su Zaituna bangaren su shi kuma, kiftawa da bismillah har sun bace sannan Yarima ya riko hannunta tare da yin kiss ya ce "Ummuna i love You." "I love You too." Ta faɗa da kasalalliyar murya. "Allah ya kawo ki gidan Hamma, yanzu ne zaki tabbatar kin shiga rayuwar Aure, wannan gidan domin ki na gina shi mu je ciki ki ga tsarin da komai." A hankali take mata maganar.
To kawai ta amsa, da kasan ya bude mata motar ta fita hannunta na cikin nashi suka shiga, a hadadden falon suka yada zango, duk da a gidan sarauta ta taso kuma suna da komai na morewar rayuwa haka bai sa ta rasa ganin haduwar wannan gidan ba, sai da suka zagaye gidan sannan suka yada zango a bedroom ɗinta da ya gaji da haduwa, komai pink da with, wanka Yarima ya yi mata don ya lura akwai gajiya a tattare da ita, shiryata ya yi sannan suka koma falo, a lokacin har an kawo masu abincin da ya yi order daga wani hotel, kadan Salmah ta ci ta ce ta koshi don zazzaɓi ne ke son rufeta, da Yarima ya lura da haka sai ya bata pracitamol sannan ta kwanta.
     Lokacin da ta tashi zazzaɓin ya sauka, don haka sai ta kara zagaye gidan ta shiga inda bata shiga ba ɗazun, sosai gidan ya yi mata kyau komai ya ji, rayuwar Salmah a garin Bauchi rayuwa ta jin dadi da kwanciyar hankali sosai Yarima yana cika alkawarin da ya daukarwa Hajja na kula da Salmah, shi yasa ta yi wani irin kyau fartar ta har wani santsi yake ga cikinta ya fara fitowa ya yi matukar yi mata kyau, don yana da wata shida kenan kullum sai ta yi waya da Hajja suna shan hira kamar basu yi nesa da juna ba.
     Salmah ce zaune a falo da misalin karfe huɗu na yammaci, duk ta kosa Yarima ya dawo don har lokacin dawowarsa ya yi ya wuce, tana son ya dawo ya sayo mata awara, don shi take jin ci.
         Zaune ta yi gabansa tare da kara narke fuska, ji take kamar zata rungume shi kasa ta yi da murya cikin sigar jan hankali "haba Prince ka yi min magana mana ko zan samu kwanciyar hankali, yau fiye da wata daya kenan ina zuwa office dinan ka hana a barni na shigo." Gama maganar ta yi tana masa far da ido, kallon bazan ya aika mata cike da takaicin halinta kamar ba zai yi magana ba sai kuma ya ce "Ke! Nuwaira tashi ki fitar min daga office ko na ce ina da bukatar ganinki ne? Tun tuni na fada maki Ina da mata ko so kike ki sanya Ni yin abin da ban shirya ba?" Fuska daure Yarima ya yi maganar yana harhada takaddun dake baje saman teburin gabansa, domin yasan yanzu hankalin Salmah ya gama tashi tun da har ya gota lokacin komawarsa gida. Bai kalleta na sai daukar jakar da yake sanya muhimman abubuwa a ciki ya kama hanyar fita, da sauri ta sha gabansa.
      "Me kake nufi Prince? Na taho wajen ka amma kana neman walak'anta ni?" Hannu ya daga mata kawai ya fita kofar office din "Zaki fita ko in rufe kofar dake a ciki?"

Wayyo wallahi na gaji gashi labarin yau ya fi min dadi don an fara zuwa dadin labarin, sai dai na gaji ga shi har yanzu ina jin ciwon ciki kunsan dai zafin ulsa😩

Vote me
Comment
& Shere on wattpad

Zulayheart Rano.

KYAKKYAWAR ALAK'AWhere stories live. Discover now