Page 3

1.5K 100 2
                                    

👉🏽💍 *KYAKKYAWAR ALAK'A* 💍👈🏽

                                     ©
              *_ZULAYHEART RANO_*

*Wattpad user name Zulayheartrano89*

*STORY AYSHA WAZIRI*

*Ina godiya gareku masoya wannan labari hakika bani da bakin gode maku domin tabbas na ga yadda kuka nuna kuna son wannan littafin fatana Allah ya bar Ni da ku har abada.*

                           *03*

Jikin Salmah ne ya ɗauki rawa kamar mai jin sanyi, ganin haka da sauri Hajja ta jawota jikinta tana mai sanyaya murya "ki nutsu Salmah kar ki yadda ki yi abin da zai bata ran iyayenki." A hankali ta saki ajiyar zuciya, sannan ta zame ta kwanta jikin Hajja idonta lumshe sai sauke numfashi take. Sam Baba Waziri bai ma kula da wani hali da Salmah ke ciki ba hasalima ci gaba da maganar sa ya yi
        "Kamar yadda na fara bayani a farko shi ne, ni da dan'wana mun yake shawarar hada auren Ummu Salmah da Yarima, haka kuma Ameena da Hamman ta ɗan Waziri, har dai yanzu muna nan akan al'adar mu ta iyaye da kakanni biki nan da kwana talatin." Ya dire maganar fuskar sa cike tam da zallar farin ciki, haka shima Maimartaba wani kyakkyawan murmushi ne kwance a fuskar sa domin wannan buri sun dade da shi a ziciyoyinsu, balle kuma Hajja Chub'ad'o da kusan ta fi kowa farin ciki sai dai bata wani nuna a fuska ba domin sanin halin 'yar rigimar ta. Hamma ɗan Waziri shi har ya kasa ɓoye farin cikin sa, haka sauran kananan su duk sai annashuwa ke fita a fuskokinsu, saɓanin Hamma Yarima da tun da ya dukar da kansa ya kasa ko da ɗagowa, domin a ganin sa an gama kashe masa rayuwa a rasa da wa za a hada shi sai wannan karamar yarinyar da bata waye ba, nannauyan ajiyar zuciya ya sauke da kyar ya iya gayyato wani murmushi wanda har Gara zubar hawaye da shi yace "Allah ya karawa Sarki lafiya tare da Baba Waziri mun ji dadin zaɓin ku Allah ya tabbatar da Alhairi." Hamma Yarima kenan shi ne ya yi wannan magana. Sosai kalaman sa sun yi wa kowa dadi, don haka cikin sauri suka amsa da Amin, bayan ya gama ne shi ma Hamma ɗan Waziri ya yi haka Hajja da Yawuro, wacce ta cika da farin cikin wannan hadi domin irin son da take yi wa Hamma Yarima baya misaltuwa.
     A haka aka tashi kowa ya koma bangaren sa, Hajja ce zaune ta sanya Salmah gaba tana kallo tare da mamakin ganin yadda lokaci ɗaya ta fita hayyacinta "Wai Salmah duk maganar auren ne ya maida ki haka?" Hajja ta yi maganar tana kara zuba idonta a jikin Salmah. "A'a Hajjata zazzaɓi ne kuma tun kafin na je wajen meeting, Amma Hajjata maganar Baba Waziri ita ta kuma sawa zazzaɓin ya yi yawa, Hajjata wai da Hamma Yarima za a hada ni aure?" Da sigar tambaya ta yi maganar. "Ba a gaban ki aka yi maganar ba? Menene abin ta yar da hankalin Salmatyy, ki kwantar da hankalin ki kar ki sanya komai a ranki kin ji?" "To Hajjata amma ina tsoron zama da Hamma Yarima Allah Hajja ba ya sona fa." "Ka da wannan ya dame ki yi addu'a nima zan ta ya ki, kuma muddin na ga yana cutarki da kaina zan sanya a raba auren." Da kyar dai Hajja ta lallashi Salmah har ta ɗan dawo nutsuwarta.
    A bangaren Hamma Yarima kuwa tun da suka fito daga dakin taro yake kaiwa da komowa tsakanin falonsa da dakin kwanansa daga shi sai singileti da gajeran wando, a haka Hamma ɗan Waziri ya shigo ya same shi "a'a lafiya kuwa Yarima?" Mtsww ya ja karamin tsaki ya ce "wannan wane irin tambaya ce? Ina tunanin kafin kowa sanin matsala ta tun kafin a zo nan wajen, me yasa Sarki da Baba Waziri zasu min haka? A rasa da wa za a haɗani sai wancan karamar yarinyar da bata ko waye ba maganar gaskiya bana sonta kuma ban ji zan iya sonta ɗin ba ko nan gaba." Saboda furucin Yarima na karshe sai da Hamma ɗan Waziri ya rintse ido domin sosai furucin ya shige shi. Shi ko Yarima bakina lura da yanayin ɗan Waziri ba, domin shi har ga Allah ya manta alakar Salmah da ɗan waziri, sai ma ci gaba ya yi da maganarsa "zan iya zama da ita sai dai ba da dadewa ba zan kara aure." Ya gama maganar yana mai furzar da wani huci. "Ni dai shawarar da zan baka kabi komai a hankali sannan ka dage da addu'a, Salmah dai kanwarka ce kuma mata a gareka mai shirin zama Uwar 'ya'yanka." A tausashe ya gama maganar. Sai a time ɗin Hamma Yarima ya ji kunyar abin da ya faɗa ɗazun sai dai fa magana zarar bunu ce, idan ta fito bata mai duwu, haushin kansa da kansa ya kama shi kusan ya manta da *KYAKKYAWAR ALAK'A* dake tsakanin su.
    Sakamakon maganin da ta sha ta samu sauƙin zazzaɓi, don haka wanka ta sake ta zura jallabiya baka mai kyau, wacce ta amshi kyakyawar jikinta, musamman da ta kasance farar mace, bata yi wata kwalliya ba don ba ma'abociya yin shafe shafe a fuska bace har ta daga kafa zata fara tafiya sai ta dawo gaban k'aton hoton nan ta tsaya, haka kawai ta samu kanta da sakar masa murmushi mai shegen tsada wanda ba kowa ake wa irin sa ba sai tabbataccen masoyi, a fili ta furta *"HAMMA YARIMA NI DA KAI MUN KUSA KULLA KYAKKYAWAR ALAK'A"* A karo na biyu ta kara yin murmushin sannan ta fita falo inda Hajja da su Adda Ameena suke, har su Adda Khadijah da Adda Hafsah suna falon.
   Hajja na ganin Salmah ta saki fara'a tana fadin "sai ina kuma haka matar Magajin Sarki?" Murmushi ta yi tana ɓoye fuska da kyar ta ce "bangaren Yawuro zan je Hajjata." "To a dawo lafiya a gaida Yawuro da kyau." Da kai ta amsa sannan ta tsuguna tana gaida su Adda Khadijah, wannan al'adar Salmah ce bata gaida wanda ya girmeta a tsaye. Cike da sakin fuska suka amsa gaisuwarta, domin kusan zan iya cewa ahalin gidan sarki kakaf Allah ya daura masu kaunar Salmah Hamma Yarima ne kaɗai ke nuna halin ko in kula da ita.
   Sallama ta yi cikin siririyar muryarta, Yawuro dake zaune suna hira da Hamma Yarima ta amsa fuska sake, zama ta yi kusa da Yawuro tana faɗin "ina yini Yawuro?" "Lafiya lau Ummu ya Hajjarki?" "Tana lafiya." Salmah ta bata amsa tana sauke idonta akan Hamma ɗinta wanda ke aika mata harara kasa-kasa muryarta ne ta daki dodon kunnensa "barka da hutawa Hamma." "Lafiya." Ya amsa yana mai kawar da kai gafe, Girman Yawuro ka dai ya sanya shi amsawa domin a yadda yake cike da haushinta bai ji zai iya ko kallonta ban. Ita kuwa ko a jikinta sai ma tashi ta yi ta nufi dakin kaninta Aliyu suka faɗa hira abinsu. Bayan shigewarta sai Yarima ya maida duban sa kan Yawuro tare da cewa "Yawuro gobe nake son komawa don ana ta kirana a wajen aiki saboda wasu ayyukan Ni ake bukatar na sanya hannu da kaina, amma ina tsoron yadda zan tunkari Maimartaba."  "A'a ɗan wannan karka damu tun da magana ce ta wajen aiki yana da kyau a daga maka kafa, ka bari Babanku waziri ya shigo." Cikin karfafa masa gwiwa ta yi maganar. Wani irin dadi ne ya kama shi domin har ga Allah ya tsani zama a garin Ningi gara ya yi komawarsa BAUCHI wajen aikinsa kila hankalinsa zai fi kwanciya. duk da dai yana jin abu ne mai wahala Baba Waziri ya yarda domin  al'ada ce ta gidan idan aka sanyawa mutum ranar aure baya zuwa ko ina sai bayan bikin. Sun jima suna hira har lokaci mai tsawo sannan ya yi mata sallama, bayan tafiyarsa Salmah da Aliyu suka fito domin dama sun guji masifar Hamma Yarima ne.
     Suna hira Baba Waziri ya yi sallama, Yawuro ta amsa ta mai tarba irin wacce matar kwarai ke yi wa mijinta, haka su Salmah suka gaida mahaifinsu fuska sake ya amsa, domin shi mutum ne mai tsananin kula da iyalinsa babu ma kamar Ummu Salmah ta yake so fiye da sauran 'ya'yansa, sai da ya kammala cin abinci sannan Yawuro ta fara yi masa bayani kamar yadda Hamma Yarima ya yi mata ta dara da fadin "A duba ma Magajin Sarki domin ya kawo babban uzuri, hakan ba yana nufin ya cire mana al'ada ce ba." Shiru waziri ya yi yana ci gaba da nazari zuwa can ya ce "Sai yadda sarki ya faɗa gobe." Daga haka ya bar falon.
     Farin ciki da bakin ciki suka kama Salmah na farko tana son Yarima ya tafi ko zata huta da muguwar kallon da yake mata, sannan na biyu bata son ta daina ganinsa a haka ta mik'e tare da barin falon cike da tunanin zuci, a natse take tafiya har ta fita bangaren Yawuro tana daf da shiga bangaren Hajja ta ji ya ce "Ummu Salmah!" Yarr ta ji tsigar jikinta ya tashi sai ta ji kamar a duniya shi kaɗai ya iya kiran sunanta, duk da tana ji a jikinta ba kiran Alhairi bane ya yi mata jiki na rawa ta juya zuwa inda yake tsugunawa ta yi tana faɗin "Gani Hamma..."

Team Yarima
Team Ummuna Salmah
Vote me
Shere
& Comment

YAR MUTAN RANO

KYAKKYAWAR ALAK'AWhere stories live. Discover now