Prologue

17.8K 1.5K 128
                                    

DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN KAI.

*Ranar daka gani itace taka. Ka daina bata lokacinka na ranar da kake da ita akan ranakun da baka da tabbas din samun su*

*Kai hamdala. Ka so. Ka yafe. Kai dariya. Kai farin ciki. Kayi rayuwa a ranar da kake da ita kaman ba zaka sake samun wata ba*

*Kayi kirki wa kowa a ranar ba lallai ka sake samun wata ranar ba. Ba lallai na kusa dakai su sake samun wata ranar ba*

Shimfida.

Iliyas Muhammad Maska dan asalin garin maska ne ta jihar katsina. Kasuwanci yake kaishi garin kaduna. Kaman yanda ya tashi yaga mahaifinshi Alh. Muhammad yanayi kamun ya rasu.

Shi kadai ne wajen iyayenshi. Inda yakan saro shaddoji daga kan gezna,galila harma da kamfala daga Mali yana kaiwa kano da kaduna.

Sai harkar tashi tafi karkata a garin kaduna. Anan ya auri zainab Aminu. Da ita kuma yar asalin kauyen kauru ne na nan kaduna.

Allah ya azurta su da yara biyar da ita kamun Allah yai mishi rasuwa. Maza uku mata biyu. Ibrahim, Auwalu, Haruna, aisha sai karamarsu jamila.

Bayan rasuwar shi da shekaru hudu itama hajiya zainab Allah yai mata rasuwa. Ko da aka raba gado aka ba kowa nashi duk cikin ya'yan maza babu wanda ya ci gaba da kasuwancin da suka gada sai Alhaji ibrahim.

Allah ya albarkaci kasuwancin shi dan ba iya kaduna kadai abin ya tsaya ba. A yanzun haka yaranshi biyar da matarshi hajiya habeeba

El-labeeb shine na farko, Anees da Asad yan biyu ne, zainab sai autansu Arif.

Kasancewar duk yafi sauran yan uwanshi wadata yasa shi gina gidaje guda uku iri daya a unguwar dosa ta nan kaduna. Suke zaune tare.

Alhaji auwal ma da matarshi Aisha yaransu biyar kamun su rabu. Dawud, tayyab, zulfa, sajda, khateeb. Matarshi ta biyu hajiya beeba. Allah bai basu haihuwa da ita ba.

Alhaji haruna da tashi matar hadiza suna da yara hudu. Jarood, uzair, mardiyya sai Aseem.

Haka kannensu ma Aisha na aure a katsina da ya'ya shida. Jamila kuwa tana kano da yaranta uku.

Wannan kenan!

****
Hat din dake kanshi ya cire ya ajiye kan kujera hadi da wayoyinshi da keys.

Belt din suspenders din jikinshi ya kwance kasancewar yasan shi kadaine a gidan yasa shi zare kayan anan falon.

Daga shi sai boxers yake takawa zuwa kitchen dinshi. Fridge ya bude ya dauko robar coke.

Baibi takan cup ba yasha da bakin robar. Ya daure ya ajiye shi nan kan counter din kitchen din. Ya dawo falo. Wayarshi dake faman ruri ya dauka cikin budaddiyar muryarshi ya amsa da fadin.

"Mamdud yane?"

"Kana ina?"

Mamdud ya bukata daga dayan bangaren. Dan murza goshin shi yayi yanayin shiru.

"El-Maska kana ina? Ko baka jina?"

"Ina gida fa"

"What!"

Janye wayar daga kunnen shi El-labeeb yayi saboda ihun da Mamdud din yai mishi cikin kunnen. Daman kanshi na ciwo.

A hankali ya mayar da wayar yanajin yanda yake masifa da cewar.

"Wanne irin wulakanci ne mutane zasu zauna jiranka. Kana sane da shooting din nan fa ba....."

Katse shi yai da fadin.

"Suyi wani abin daban. Ai holding nawa part din. Kaina ciwo yake yi bacci zan"

Bai tsaya jin masifar da Mamdud din zaiyi ba ya kashe wayar gaba ki daya. Yana jan guntun tsaki. Sam baya son takura. Bedroom dinshi ya wuce dan ya watsa ruwa ya kwanta.

Duhun dake dakin baisa shi kunna switch din ba. Sosai kanshi ke ciwo ya karasa kan gadon yadan zauna yq huta tukunna ya shiga wankan.

Zama yaji yayi kan abu kaman mutum. Kara ya saki yana mikewa. Ya tsorata ba kadan ba. Ba arziqi ya lalubi switch din dakin ya kunna.

Kwance take kan gadon tana kokarin kare idanuwanta daga hasken dake dakin. Lumshe idanuwanshi El-labeeb yayi yana kirga daya zuwa goma cikin kanshi.

Sanda ya bude su ya sauke kan yarinyar dake kwance dakin tama sake gyara kwanciyarta ta koma bacci.

"Kutuma...."

Ya fadi ranshi a bace. Karasawa yai kan gadon ya dauki pillow din dake gefe ya kwada mata a baya. Mikewa tai tana yamutsa mishi fuska.

"Ta ina kika sake shigowa? Wai bama nasa an canza mun locks din gidan nan ba"

Murmushi tai a kasalance wanda ya sake daga mishi bacin rai.

"Meye abin dariya a jikina? Ban fada miki yan sanda zan dauko miki ba kika sake shigomun gida?"

A hankali ta mike. Yabi fitsararriyar shigar dake jikinta da kallo. Muryarta can kasa tace.

"Ban fada maka bacci kawai nake shigowa inyi ba? Godiya ya kamata kamun. Ko baka ganin gidanka a share?

Yaushe rabon daka ba flowers din daka ajiye ruwa? Yaushe rabon da ka sa a wanke maka toilets? Dan nai bacci zakamun ihu"

Ta karasa tana rabawa ta gefenshi ta wuce. Binta yai da kallon mamaki.....!

****

Sajda yake hangowa jikinta sanye da uniform tsaye gaban mai awara. Da hanzari ya karasa ranshi a bace. Yarinyar nan bata da hankali.

Kullum taci awarar nan sai cikinta ya baci. Ya hanata ashe bataji ba. Siya take ta tafi islamiya. Sajda dake tsaye kaman ance ta dago ta ko sauke idanuwanta kan fuskar Dawud.

Gabanta taji ya fadi ganin yanayin dake fuskarshi. Yana karasowa kafa yasa yai harbi da bokitin awarar yana fatali dashi cikin kasa.

Matsawa sajda tai idanuwanta na cikowa da hawaye.

"Me nace miki? Kin rainani ko? Ban isa in hanaki ki hanu ba!"

Girgiza mishi kai take alamar A.a dan ta kasa magana. Ji yai ana taba mishi kafada. Yasa hannunshi ya ture hannun koma waye batare daya juya ba.

Idanuwanshi na kafe kan sajda. Zagayowa mai awarar tayi. Cike da masifa tace.

"wallahi saika biyani awarata. Tafdi!"

Batare daya kalle ta ba ya zaro wallet dinshi daga cikin aljihu. Dubu biyu ya zaro ya watsa mata. Hadi da fadin.

"Abinda yafi wannan zai faru idan kika sake siyar mata da wannan banzar awarar"

"Kanwarka zaka jama kunne ko budurwarka ce oho. Bani zaka bude ma idanuwa ba"

A fusace ya juya yana sauke idanuwanshi kan yarinyar da take jin zata iya fada mishi duk abinda ya fito daga bakinta.

"Uban......"

Kasa karasawa yai. Ya nemi inda kalamanshi suka makale ya rasa. Abu dayane yake da tabbaci akai. Abinda ke cikin idanuwanta ya taba shi.

Ya tabashi ta inda bai taba zato ba....!

*Bance wannan tafiyar mai sauqi bace ba. Bance tafiyar nan perfect bace. Bance tasu rayuwar babu emotional conflicts ba.*

*Suna da nasu perfections din suna kuma da nasu imperfections. Abu daya zan iya baku tabbaci. Yan gidan Maska zasuyi rocking dinku*

*Zasu tabaku ta fanni na rayuwa da dama. This is a reality ride. I don't believe in fictions and i hardly like hardly believe in happily ever afters*

*You won't regret this In shaa Allah. I am not the BEST. But i am EXCEPTIONAL.*

Please. Abeg. Biko. I take God name beg you. If you like this story. Put a smile on my face. Vote, comment and share!

I love you all.

#AnaTare

RAYUWAR MUWhere stories live. Discover now