34

8.3K 506 107
                                    

"Ki bari mu fita tare mana. Nima zanje gidan da mun dawo asibiti da Ateefa"

Labeeb ya fadi yana kallon zulfa da take shafa powder. Juyowa tayi tana ware mishi idanuwa.

"Nidai a'a...zamuyi walima fa anjima da yamma"

Dan Labeeb ya hana ma, tun jiya taso ya kaita ta kwana. Bazai gane farin cikin da take ji ba. Ta dade tana jin ina ma Abbq mami ya aura. Yau da fatan ta zai zamo gaskiya babu abinda take so daya wuce ta kasance cikin yan uwanta.

Suyi farin cikin tare su dukkan su. Shima Labeeb din jiya da dare ya dawo daga Abuja. Yau kam lallaba shi zatayi yabarta ta kwana a gida, tunda daman yau yana dakin Ateefa, ya karashe mata cikon kwana dayan.

"Saifa karfe sha biyu ma za'a daura auren. Kuma walimar ba karfe hudu naji Don yace ba?"

Turo baki zulfa tayi tana ci gaba da shafa powder dinta batare da ta sake ce mishi komai ba. Yasan ma'anar shirunta, kome zaice ba canza komai zaiyi ba.

"Sai mu fita tare in na sauke ki mu wuce..."

Tashi tayi daga gaban mirror din.

"Tayyab yaje karbo dinki... Nace ya biyo mu wuce..."

Ta fadi tana wucewa dan ta sa kaya. Fitowa tai sanye da atamfa, riga da zani, gashin kanta take gyarawa, Labeeb yabi hannuwanta da kallo, yana son gashinta, Tee dinshi bata da gashi haka.

Wayarta dake kan gado ta soma ringing, kamun ta karasa Labeeb ya daga.

"Ke gani nan kofar gidanku..."

"Yayi kyau Tayyab... Ba zaka iya shigowa a gaisa ba ko?"

Yana jin dariyar da Tayyab yayi a kunyace

"Sauri nake ne Ya Labeeb..."

"Ko ba ka sauri ba zuwa kake ba daman..."

Labeeb ya karasa maganar yana kashe wayar hadi da mika ma zulfa dake tsaye, kamun ta dauki katon mayafinta ta yafa tun daga kanta, jakarta dake ajiye kan gado ta dauka. Ta tsugunna tana sumbatar Labeeb.

"Sai na dawo..."

"Ki kula da kanki... Zan taho nima"

Ya karasa maganar yana saukowa daga kan gadon, sai da yaga ta fice daga dakin tukunna ya shiga wanka. Zulfa kam kasa ta sauka ta samu Tayyab da Ateefa dake gaisawa.

"Tayyab ashe ana ganinka"

Dariya yayi

"Kiji Aunty fa... Duk sakon gaisuwar da nake bama Yaya baya fada maki?"

Hararshi Ateefa tayi

"Zaka fadi gaskiya ne ma..."

Zulfa kam dariya take musu.

"Sai kun taho"

"In shaa Allah. Nasan bawani jimawa zamuyi ba...ki gaishemun da mami"

Kai zulfa ta jinjina suna ficewa tare da Tayyab din. A mota ne take ce mishi

"Allah raina kal nake ji"

"Ni so nake kawai inga an daura. Ji nake kaman wani abu zai iya faruwa kamun lokacin nan ya cika"

Dan kallon Tayyab dake tuqi zulfa tayi. Bata ga laifin shi ba. Itama can kasan zuciyarta tana wannan tsoron.

"Babu abinda zai faru sai alkhairi"

Dan daga kafadunshi yayi

"Ko dan ban saba abubuwa su tafar mana dai-dai na tsayin lokaci ba... Kwanciyar hankalin nan har tsoro nake ji wallahi..."

RAYUWAR MUWhere stories live. Discover now