19

7.4K 557 114
                                    

Wannan karin Mamdud ya rasa me ya samu labeeb, har sukaje bauchi suka gama aikin da zasuyi acan party ko daya labeeb bai attending ba.

Sai dai Mamdud yaje shi kadai. Shi kam baya cikin yanayin yin party. Gaba daya yarinyar nan ta tsaya mishi a zuciya. Ba ita bace ta farko da ta fara zubda cikin shi ba.

Amman itace ta farko da alhakin bacin ta yake gabaki daya akanshi. Sauran duk rabawa suke. Kudinshi suke so, shi kuma jikinsu yake so. Wannan karin barnar dayai babbace.

Cikin dakin su na salama hotel Mamdud ya shigo wajen karfe uku na dare ya samu labeeb yana hada kayansu cikin jaka, zama yai gefen gadon.

"Wai meke damunka ne? Baka da lafiya? Ko tsufa ne ya fara kamaka?"

Girgiza kai labeeb yayi.

"Ka samamun lafiya Mamdud"

"No, da gaske nake. Meke damunka? A waje muke fa, ina El-Maska? Nasan baka fitowa da El-labeeb"

Jan numfashi labeeb yayi, ya fitar dashi a hankali.

"Yarinyar nan ta tsayamun a rai mamdud"

"Mtsww shine me? Itace ta farko? Yara nawa ka zubda?"

Maganganun Mamdud din sun kara saka shi jin kazanta da girman laifin da yake aikatawa. Laifin da baisan ta yanda zai yabari ba.

"She is different. Ni ne na farkon ta"

"No shit!"

Mamdud ya fadi yana ware idanuwa. Kai labeeb ya daga mishi, yana tabbatar mishi da gaske ne abinda ya fada.

"Me yasa baka da kula ne? Ko yaushe sai kayi slipping?"

"Ta ya zansan virgin ce? Taya zan gane ba kaman sauran bace? Ya Rabb, na tsani kaina wallahi"

Dan bubbuga mishi kafada Mamdud yayi.

"Abinda ya faru ya faru. Just chill, ka daina dorama kanka laifi, ita tazo, ba dole kai mata ba"

Kai labeeb yadan daga mishi, yasan bazai fahimci yanda yake ji bane. Yanayin ta da komai zai jima bai mantu a wajen shi ba.

Maganganun datai mishi sun tsaya mishi a rai ba kadan ba. Yanajin Mamdud ya nata kai kawo cikin dakin kamun ya shiga toilet. Zage zip din jakarsu yayi yahau kan gadon ya kwanta.

Har Mamdud ya gama wankan ya fito ya kwanta shima idanuwan labeeb ko alamar bacci babu a cikinsu, wannan ne karo na farko dayasan wata damuwa banda ta family dinshi.

*

Labeeb zai iya cewa a hankali a hankali, da duk ranar da zata wuce da yanda hoton yarinyar nan yake dishewa a zuciyarshi. Har randa ya wayi gari ya neme shi ya rasa.

Rayuwa yaci gaba dayi abinshi kaman komai bai faru ba. Kaman yarinyar na daya daga cikin abinda ya wuce a rayuwarshi da bazai dawo ba balle kuma harya gyaru.

Daga dakinshi ya fito ya kalli Asaad dake kwance kan doguwar kujera, aseem kuma yana kasa ya jingina bayanshi da kujerar.

"Na fita, ku kirani in kuna bukatar wani abu"

"A dawo lafiya"

Suka fada a tare, ya daga musu kai ya fice.

"Na rasa me zan saima sajda. Tun satin nan nake tunani, gobe ne ranar saukan su"

Aseem ya fadi yana dafe kai.

Gyaran murya Asaad yayi.

"How about ka fada mata kana sonta?"

Juyawa aseem yayi ya harare shi.

"Duka sajdar nawa take? Kuma muna da sauran lokaci. I am fine da nuna mata ina sonta ba saina furta ba"

RAYUWAR MUOn viuen les histories. Descobreix ara