16

7K 611 245
                                    

Ruwa Tayyab ya mika mata, ta karba, saida ta shanye tas tukunna ta mika mishi cup din ya karba ya ajiye gefe. Hannu tasa tana goge fuskarta.

"Ya isa haka zulfa, inba so kike ki sama kanki wata cutar ba"

Ya fadi a tausashe. Cikin shessheka tace mishi.

"Ina yaya?"

Dan daga mata kafada Tayyab yayi hadi da fadin.

"Destroying duk wani abu dake cikin dakin shi"

Hannuwa biyu zulfa tasa ta dafe kanta tana jin kaman ta rusa ihu. Ta rasa inda zata tsoma kanta taji sanyi sanyi ko ya yake.

"Laifina ne, ni naja muku abin kunya...ni ya kamata yai destroying....."

Rikota Tayyab yayi jikinshi yanajin ciwo da dacin abinda ke faruwa dasu, bude baki yayi zai magana yaji an turo dakin. Ya juya dan ganin ko waye, ya sauke idanuwanshi kan Haj beeba.

Ranshi yaji ya kara baci, karasa takawa tayi, ta kalle su a wulakance.

"Abin kunyar da aka kunso kenan ashe shisa....."

Karar mari zulfa taji cikin kunnuwanta, ta dago kai da sauri, dai dai lokacin da tayyab ya sake dauke hajiya beeba da wani marin.

"Ke kina da bakin da zaki jefi wani da gori?!"

Tayyab ya fadi cikin hargowa, ihu hajiya beeba ta rusa tana fadin.

"Na shiga uku ni beeba, Alhaji yaranka zai kasheni!"

Hannu tayyab ya sake dagawa, zulfa ta rike shi tana girgiza mishi kai, dai dai shigowar mami dakin.

"Meke faruwa haka?"

Tayyab na maida numfashi yace.

"In nagama kirga abinda nake kirgawa cikin kaina matar nan bata bar dakin nan ba wallahi mami saina karyata!"

Hannun hajiya beeba dake rusa ihu tana zagin tayyab ta uwa ta uba mami taja tana tirjewa tana komai ta fitar da ita daga dakin sannan ta dawo.

"Wai me ya faru?"

Dafe kai Tayyab yayi yana jin wasu hawayen takaici na cika mishi Idanuwa. Saida ya tabbatar zai iya magana tana nutsuwa sannan ya bude bakinshi, kirjinshi da nauyi marar misaltuwa.

"Gori tai ma zulfa.... Mami gori tai mata... Ni bazan iya dauka ba"

Waje mami ta samu ta zauna gefen zulfa tana dafe kanta, hawaye suka zubo mata. Gori kam yanzun suka soma sha. Abinda ke faruwa da zulfa tambarine da zaibi har jikokinta.

Sai dai bata da zuciyar da zata fada ma Tayyab haka. Tana kallo ya fice daga dakin yana jan kofar kamar ita tai mishi laifi. Kwanciya zulfa tai kan gadon saboda jirin da taji yana dibarta.

Tanajin mami ta dafa mata hannu, tana son nuna mata tana tare da ita, sai dai ji take duniyar ta a yanzun babu wanda zai taba fahimta. Ga kanta ya mata nauyi lumshe idanuwanta tayi tana fahimtar abinda ake nufi da asalin tashin hankali.

"Rayuwata ba zata taba komawa dai dai ba ko mami?"

Shafa kanta mami tayi, tana jin kaman ace tana da wani sihiri da zata iya amfani dashi wajen batar da abinda ke faruwa da zulfa, sai dai bamai karfin ja da kaddara.

Muryarta can kasa tace

"*Rayuwar Mu* gaba daya zulfa. Allah ya san halin da muke ciki. Ba kowacce kaddara bace take zuwa maka da fuska me kyau.

Inka karbeta, inka mika lamurranka wajen Allah saiya sauya maka ita saboda baya dora maka abinda ba zaka iya ba"

Har lokacin idanuwan zulfa a lumshe suke, tana jin maganganun mami na ratsa ta.

RAYUWAR MUOnde as histórias ganham vida. Descobre agora