29

7.5K 606 231
                                    

Dukkan su anan asibitin sukai sallar isha'i. Dan khateeb ma dawud yaje ya dauko shi daga makaranta ya kawo shi nan asibitin. Har lokacin zulfa bata tashi ba.

Ko doc bai shigo ba dawud kan duba yaga komai stable. Hutu ne kawai take samu. Hira suke abinsu, dan kallo daya zakai musu kasan suna cikin nishadi da su kadai suka san ma'anar shi.

"Dare nayi Dawud. Ka je ka dauki yumna ku tafi gidanku"

Cewar mami tana kallon shi.

"Don haddani zaka tafi ko?"

Khateeb ya fadi tun kamun dawud din ya amsa yana kara makalewa a jikin shi. Dan sadda kai dawud yayi yana jin kunyar mami din.

"Da nabari sai gobe in Allah ya kaimu"

Girgiza mishi kai mami tayi

"Dawainiyarta duka ta dawo hannunka... Iya kokari antynta ta muku ai. Ko kwanciyarta asibiti mu ya kamata mu kula da ita... Yanzun zaka tashi ka tafi"

Mami ta karasa babu wajen musu a muryarta. Khateeb ya ci gaba da tsalle tsalle a jikin dawud yana fadin zai bishi.

"Zo nan... Ba yau ba"

Mami ta fadi, shagwabe fuska khateeb ya sake yi yana kallonta. Girgiza mishi kai tayi. Dole ya sauka daga jikin dawud yana komawa inda mami ta nuna mishi gefenta ya zauna yana turo baki.

Mikewa dawud yayi

"Sai da safenku mami. Zan kira anjima... Indai kuna bukatar wani abu ku kirani"

"Allah ya tashemu lafiya. Babu ma abinda muke bukata. Ka kwanta ka huta dan Allah"

"In shaa Allah..."

Tayyab ne ya mike yana binshi suka fita tare. Har saida suka je wajen parking din cikin asibitin tukunna dawud ya zaro mukullai daga aljihunshi yana ware na motar ya mika ma tayyab.

"Ka riqe wannan a hannunka. Sai inje gida in dauki dayar..."

Karba tayyab yayi

"In sauke ka gidan mana yaya"

"A'a ka zauna ko za'a siyo wani abu. Zan hau machine"

Jinjina kai tayyab yayi, fuskarshi dauke da wani yanayi yace

"Allah ya sanya maka albarka da alkhairi a rayuwar auren ka yaya. Allah ya kula dakai fiye da yanda ka kula damu. Allah ya baka farin ciki fiye da yanda ka bamu..."

Lumshe idanuwa dawud yayi yana bude su hadi da sauke numfashi mai nauyi. Addu'ar da tayyab yai mishi na nutsar da zuciyarshi.

"Amin tayyab... Indai kuna sona a kusa daku... Fadamun kawai zakuyi. Kasan hakan ko?"

Murmushi tayyab yayi

"Kana tare damu a zuciyar mu ko yaushe yaya. Da tafiyar Haj. Beeba nake jin komai zai dai-dai ta..."

Murmushi dawud yayi da yake ji har cikin zuciyar shi. Koya ya tuna Haj. Beeba bata gidan nan sai yaji wani farin ciki a zuciyarshi. Dan ya tsani ya koga inuwarta balle ita da kanta.

Sai da tayyab yaga yahau machine tukunna ya juya. Yana zuwa gida kanshi tsaye dakinshi ya wuce yana dauko mukullin dayar motar. Tukunna ya fito, duka akwatunanshi na nan falo inda suka barsu da safe.

Dauka ya shiga yi yana kaiwa mota. Saida ya gama tukunna ya shiga motar. Ya kunna yana juyawa da motar ya fita daga gidan.

Wakar (Free by zain bhikha) ya kunna yana kure volume din. Wakar na sashi shiga wani yanayi mai wuyar fassara. Ita yabari on repeat har ya karasa gidan su yumna tukunna yai parking yana kiranta a waya.

RAYUWAR MUWhere stories live. Discover now