10

5.6K 522 104
                                    

Kaman yanda na fadata, wannan tafiyar nada banbanci da kowacce, banyi alkawarin happily ever after ba. Rayuwa ce a yanda take faruwa saboda sam ban yarda da fiction ba.

Ina godiya da dukkan comments dinku, suna bani kwarin gwiwa fiye da zaton ku. Allah yabar zumunci (Amin thumma amin)

Sati biyu kenan. Rayuwa suke badan tana musu dadi ba. Suna iya kokarin su wajen ganin komai daya faru bai canza yanayin zamantakewar dake tsakanin su ba.

Sajda tafi komai daga musu hankali a yanzun. Kaman asibitin da aka kaita ya sake tunzura ciwonta ne. Dan yanzun da wuya take samun baccin awa biyu a rana.

Abinci dakyar ake dura mata yoghurt, haka ma ruwa, gashi in ba kowa kusa ta fara, haka zatai ta buga jikinta dakome ta samu. Labeeb na iya kokarin shi akansu.

Kome suke bukata ta bangaren kudi basu da matsalar shi. Ya dauke musu duk wannan. Yadai damu da ciwon sajda dinne shima. Kullum saiya bugo waya ya tambaya jikinta.

Haka satin nan yana dawowa suka dauketa shi da dawud suka mayar da ita asibiti. Zaune su ummi suke suna jiran dawowar su.

"Da ina da zabi zan dawo da ciwon sajda jikina ta samu sauki. Allah kadai yasan abinda take ji"

Tayyab ya fadi kaman zai fashe da kuka. Kallon shi ummi tayi.

"Kar in kuma jin irin maganar nan a bakinka. Addu'ar ku take bukata. Kaman yanda ka fadi. Allah kadai yasan abinda take ji. Saboda shi ya dora mata.

Shikuma zai yaye mata"

Zulfa ta kalli ummi tace.

"Me ya sameta wai? Kawayenta sunata tambayata a makaranta. Nace musu bata da lafiya"

Rausayar dakai ummi tayi. Inda tasan abinda ya ke damun sajda data ji saukin abinda take ji a zuciyarta. Bata nunawa ne, amman tare suke ciwon nan da sajda.

Da minti daya bai taba fita daga zuciyarta ba balle tai tunanin samun sauki, dan wajen ciwon sajda daban yake a zuciyarta. Ba tata lafiyar ba har rayuwa da kanta zata hakura da ita in hakan zai samarwa sajda sauki.
"Ban sani ba zulfa. Kawai bata da lafiya ne"

Shiru zulfa tayi nadan wani lokaci kamun tace.

"Allah ya bata lafiya"

Su dukan su suka amsa da amin.

"Zulfa dubamun girkin can a kitchen. In ya tsane ki kashe rishon"

Mikewa zulfa tayi ta nufi kitchen din, bata jima ba ta fito.

"Na kashe ummi"

"Yawwa sannu"

Tayyab zulfa ta kalla.

"Yaya ka kunna mana kallo"

Baice komai ba ya mike. Dan yanzun kwata kwata kallo baya gabanshi. Kunna mata yayi ya dawo ya zauna. Daga shi har ummi idanuwan su ne kawai akan Tv din. Hankalinsu nacan wani waje daban.

**

"No....... Bazan iya ba. Me zance ma ummi? El bazan iya ba"

Sai lokacin labeeb ya dago kanshi ya sauke idanuwanshi kan dawud dake kai kawo cikin office din.

"Dawud ka zauna"

Kai yake girgiza mishi batare da ya daina kai kawon da yake ba. Yana jin komai na kara kwance mishi.

"Sajda bata haukace ba. This is not happening......."

Yake fadi ma kanshi. Ganin yanda gabaki daya ya rikice ya sa labeeb mikewa ya kamo hannun shi ya dawo dashi ya zaunar.

RAYUWAR MUWhere stories live. Discover now