13

6.9K 711 244
                                    

Da wata irin gajiya ya dawo gida daga makaranta. Da sallama ya murza handle din kofar yana taka kafarshi cikin falon.

Tura kofar yai yana rufeta, kamun ya juyo yaji khateeb makale da kafafuwanshi. Baisan lokacin da murmushi ya kwace masa ba. Hannu ya zagaya yana kamoshi.

"Don"

Dago khateeb yayi.

"Khateeb..."

Dariya kawai khateeb yake yi. Duk ciwon da dawud yake ji a zuciyarshi indai khateeb na dariya haka yakanji kaman yaron na raba farin cikin ne tare dashi.

"Mamiiii......"

Dawud ke kira dan baiji motsinta ba, ya cire takalmanshi yana takawa, kitchen ya nufa ya dauko ruwa ya fito yana sake kiranta.

"Kaganni a daki dawud, harka dawo?!"

Mami ta fadi daga can ciki.

"Na dawo mami...."

Ya karasa maganar yana saukw khateeb kan kujera hadi da zama kusa dashi yana fitar da numfashi, kanshi ya jingina da bango yana sauke numfashi cike da gajiya.

Mami ce ta fito daga daki ta kalle shi.

"Sajda ke ta ciwon ciki, yanzun......"

Bata karasa maganar ba dawud yai wata irin mikewa yana wuceta ya nufi dakin data fito. Sajda ya gani kwance kan gado, zuciyarshi na dokawa ya karasa kan gadon ya zauna gefenta.

"Sajda.... Sajda....."

Yake fadi yana saka hannuwanshi duka biyun ya tallabo ta. Dakyar ta bude idanuwanta ta kalle shi.

"Yaya cikina ciwo"

Ta fadi tana yamutsa fuska, ji yake kaman ya karbi ciwon da take ji ya maida shi jikinshi. Bai damu da duk abinda zai same shi ba indai su suna nan lafiya.

Mami ce ta shigo ta karaso inda yake.

"Mu tafi asibiti...."

Kai kawai ya daga mata yana dago sajda ya mike da ita kaman wata yar tsana.

"Yaya zan iya tafiya"

Sajda ta fadi, ko kulata dawud baiba ya karbi hijab din da mami ta miko mishi na sajda, kan dayar kafadarshi ya rataya hijab din, bai jira mami ba dake saka hijab dinta.

Ya fito da sajda yana kama hannun khateeb.

"Ina zamuje? Ice cream?"

Khateeb yake tambaya. Dawud bai kula shi ba, kawai hannunshi yaja ya fita dasu. Mota ya bude ya saka sajda, dai dai fitowan mumy ta kulle gidan.

Hijab din sajda ya mika mata ya bude motar khateeb ya shiga sannan ya zagaya ta dayan bangaren shima ya shiga, ya kunna motar yana janta suna nufar dialogue.

*

Sanda suka karasa anata kiran sallar magrib, inda Allah ya taimaka suna da file a wajen. Nan yabar su a waiting area ya ja khateeb suka fita sukai sallar magrib suka dawo.

Nan yabar khateeb da mami ya shiga wajen ganin likita da sajda. Akwai abubuwa da yawa da mami ke barin dawud yayi dan tasan ba barinta zai ba.

Wannan na daya daga cikinsu, bawai dan bata da muhimmancin hakan a wajen shi ba. Iya zaman su ta fuskanci dawud, da zai iya ko yana da lokacin girki ma indai kannenshi ne zasu ci da wahala yabarta ta dafa.

Danta kula komai da kanshi yake so yai musu, baya son raba hakan da kowa. Kaunar dake tsakanin shi da kannenshi mai girma ce.

Sosai aka dudduba sajda din. Ga tambayoyi data sha, likitan ya tabbatar ma da dawud food poisoning ta samu.

RAYUWAR MUWhere stories live. Discover now