32

9K 702 179
                                    

Fourth to the last page.

Bai koma gida ba sai wajen goma saura na dare ranar. A falon kasa ya samu Ateefa data mike jin shigowar shi tana karasawa tai hugging dinshi. Yanayin yanda ta rike shi kaman zai gudu yasa shi yin mamaki.

"Tee lafiya dai ko?"

Sake shigewa tai jikinshi.

"Babu komai... Ka dade sosai"

Sauke numfashi yayi.

"Ban kula dare yayi ba...Afuwan ban kira ba kuma"

Bata ce komai ba, tadan yi jim tana jin duminshi, yanayin muryarshi da yake a dakushe yai mata wani iri. A hankali ta dago daga jikinshi. Hannunshi ta kama, bai musu ba yabi ta suka hau sama.

Bata tsaya dasu ko ina ba sai dining area din, kujera yaja ya zauna. Wata irin gajiya yake ji da ko magana baya son yi, yana kallonta ta zuba mishi abinci. Plate din yaja gabanshi tana miko mishi cokali.

Sama-sama yaci abincin badan yana jin yunwa ba, ya sha ruwa.

"Har kayi me?"

Dan yatsina fuska yayi.

"Bana jin yunwa... Banajin dadin komai ne... Kwanciya kawai nake son yi"

Fuskarshi take kallo da take a kumbure. Kamun ta mike tana bashi hannunta daya kama yana mikewa shima. Bedroom dinsu suka nufa, nan tabarshi tsaye ta shiga ta hada mishi ruwan wanka ta fito da towel tana mika mishi tukunna ta fice ta koma dining area din tana hada kayan daya bata ta sauka kitchen dasu.

Sanda ta koma kayan bacci ta dauko mishi ta feshe mishi su da turaruka ta ajiye kan gadon, kamun ta sake kayan jikinta zuwa na bacci itama. Daya fito wankan ma baice mata komai ba, ta kula baya son magana.

Kayan shi ya saka yahau kan gadon ya kwanta. Ko ta ina yake jin yanda awannin nan da suka wuce suka fama mishi ciwukan da yake dauke dasu shekara da shekaru. A ko ina na zuciyarshi yake jin zafi da radadin da suke mishi.

A wanni fannin kuma yana jin kaman ya sauke wani katon nauyi daya jima yana dauke dashi. Yana jin yanda kannen shi suka karbi El-labeeb da El-Maska. Yanda ya raba Rayuwar shi ta baya tare dasu batare da sun kyamace shi ba.

Yanda suka fahimci kaddarar da baida iko akan faruwar ta. Zuciyarshi na mishi nauyi duk idan yanayin fuskar Mamdud da halin da yake ciki suka gifta mishi. Zai mika duk dukiyar daya mallaka in har hakan na nufin Mamdud zai samu yaro.

Sai dai yana da yaqinin addu'a zata iya canza kaddarar Labeeb. Allah mai Rahma ne ga bayinsa. Musamman masu yarda da dukkan fuskar da kaddara tazo musu da ita. Mai kyau ko mai muni.

Ateefa data hawo kan gadon ta katse mishi tunanin shi. Wutar dakin takai hannu ta kashe musu tana kunna ta gefen gadon marar haske. Sai da taja abin rufa ta soma rufe labeeb tukunna ta rufe kanta tana jan jiki ta kwanta.

Hannun shi yakai ya lalubi nata yana rikewa cikin nashi. Sannan ya matsa yana dora kanshi kan pillow dinta, gyarawa tai yanda zai kwanta sosai.

"Bana jin dadi... Komai ciwo yake mun"

Goshinta ta hada da nashi tana jin hucin numfashin shi kan fuskarta.

"Komai zai wuce... In shaa Allah. Allah baya dora mana abinda ba zamu iya ba... Yakan dora mana kaddara dan ya gwada karfin Imanin mu..."

Lumshe idanuwanshi labeeb yayi yana bude su, maganganunta na zama a zuciyarshi.

"Bansan ya Mamdud yake ji ba... Sai dai tunanin bazan taba samun yara ba kawai nasa inji numfashi na na shirin daukewa..."

RAYUWAR MUWhere stories live. Discover now