11

6.6K 692 220
                                    

Wani numfashi yaja ya fitar dashi a wahalce kamun ya saki handle din kofar kamun ya karasa inda su tayyab suke, zulfa ta soma tasowa ta kama hannunshi.

"Yaya ummi ta haihu?"

Kallon tayyab yayi. Bai furta ba, amman yanayin shi ya nuna cewa shima kalar tambayar dake bakinshi kenan. Girgiza musu kai yayi, wani abu na mishi tsaye a kirji.

"Kuzo muje"

Ya fadi, muryarshi a dakushe. Ba musu suka bishi har dakin da ummi take. Babban dakine da gadaje guda biyu a ciki. Sai kujerun zama har shidda.

Ummi ce kadai a kwance kan gadon. Sai dawud yaga kaman cikin jikinta ya kara wani irin girma. Su duka suka karasa inda take suka ja kujeru suka zauna.

"Ummi sannu"

Dakyar tai musu murmushi, ta wahala, batajin karfi ko kadan a jikinta.

"Ko kina son wani abu?"

Tayyab ya bukata. Zulfa kuma hannun ummi ta kama tana rike shi dam cikin nata, kokarin hadiye kukan da yake zo mata takeyi.

Tambayar tayyab taima ummi tsaye, abu daya uku take bukata a yanzun, na farko Auwal, tana bukatar mijinta a kusa da ita.

Tana bukatar kulawarshi kaman yanda ya saba a haihuwar dukkan su, tana son abinda zata haifa ya zamana addu'ar abba yaji cikin kunnuwanshi.

Shi yai mishi huduba, in da Auwal kusa da ita a yanzun zata ji kaman sun raba wahalar ne. Yau tafi jin zuciyarta cike da wani irin kadaicin shi.

Cikin zuciyarta tace.

"Allah na yafe ma Auwal duk wani laifi da yaimun, wanda nasani da wanda bansani ba, Allah ka yafe mishi, ka ceto shi daga halakar da ya fada...."

Abu na biyu da take bukata shine taga sajda, bata san me yasa take son saka idanuwanta akan sajda ba. Abu na uku da take bukata shine ace wani cikin kawunnanta ko wanda suka hada jini yazo.

Saidai tasan bazai yiwuwa ba, ba su damu ba. Bata san dalilin dazai sa su fara ba a yanzun din.

"Ummii...."

Zulfa ta sake kiranta a karo na hudu, tana katse mata tunanin da take. Cikin idanuwa ta kalli dawud.

"Ka kawomun sajda in ganta dawud, kaje ka fadama abban ku ko bazai zo ba, mu sauke hakkin shi da yake a kanmu......."

Ko bata furta ba yasan abinda take son fada amman kalaman sun makale mata. Kai ya daga mata hadi da fadin.

"Barin tafi yanzun ummi, Allah ya baki lafiya"

Su duka suka amsa da amin. Hankalinshi ya mayar kan tayyab.

"Ka kula da zulfa"

Dakai ya amsa shi, hannun ummi dake hannun zulfa dawud ya kama, ya sumbata yana jin kaunar ummi dabai hadata da kowa ba a zuciyarshi na kara yawaita.

Sannan ya fita daga dakin yana ja musu kofar, bayanshi ya jingina da bangon wajen. Kokawa yake da zuciyarshi. Baice bazai sake ganin abba ba. Amman bai taba kawo ma ranshi zai ganshi nan kusa ba.

Duk abubuwan nan da suke faruwa sun saka shi danne abinda yake ji kan abban. Yanzun tunanin ganinshi, yai mishi magana, zuciyar shi rawa take sosai.

Jikinshi babu karfi yake takawa harya fita daga gidan. Machine ya tarba yahau zuwa malali.

*

Kwankwasawa yayi. Yakai shekara daya da wani abu rabon da kafarshi ta tako gidan. Yakan kai musu ziyara lokaci zuwa lokaci saboda ummi najin dadin hakan.

RAYUWAR MUWhere stories live. Discover now