15

7.9K 619 100
                                    

"El yumna..... Bansan ya take ba, bata numfashi...."

Dawud yake fadi yana dafe kanshi cikin hannayenshi. Mikewa labeeb yayi daga tsugunnen dayake ya kama hannun dawud yana taimaka mishi ya mike.

Yana kallon jirin daya ke daukar shi, dam ya rike shi, yana fito dashi daga cell din, yan sandan dake wajen ya kalla.

"In wani abu ya same shi...... I will see you in court, zan tabbatar babu wanda ya kara saka uniform a cikinku!"

Yana jin yanda idanuwansu ke yawo a jikinshi har suka fice daga police station din. Mota ya bude ya saka dawud sannan ya zagaya ya shiga.

Ko ta ina yake jin rayuwa kaman tana janshi, ko wanne bari nason samun nashi kason. Kai tsaye asibiti labeeb ya nufa da dawud.

Suna shiga dawud yace mishi.

"Wayata..... I need to know yanda yumna take...."

Hannu labeeb yasa a aljihunshi yana zaro wayar hadi da fadin.

"Gata nan na karbo maka"

Hannu yasa ya karba yana cire ta daga key. Number din anty ya lalubo ya kira. Zuciyarshi dokawa take kaman zata fito daga kirjinshi.

Tana dagawa ko sallama bai bari ta karasa ba ya katse ta da fadin.

"Anty yumna......."

"Gamu nan tare dawud, muna asibiti ma...."

Numfashi dawud ya sauke yana mika ma labeeb wayar, saboda ba karamin karfin hali yake ba, ko ina na jikinshi ciwo yake.

Musamman kanshi da yake jin kaman ya cire ya ajiye gefe daya yadan huta, sama sama yake jin labeeb da anty suna magana, dan ya daina fahimtar abinda ake fadi.

Koya ya lumshe idanuwanshi sai yaga wani haske haske na gilmawa. Yana jin labeeb ya riko shi yana fadin.
"Dammit stay with me dawud....."

Komai jujjuya mishi yake, so kawai yake ya rufe idanuwanshi ko na mintina biyu ne yadan huta, hakan kuwa yayi, yana rufe su yaji komai shiru.

Ba cikin idanuwan nashi ba kawai harma kanshi, gabaki daya komai na duniyar ya tsaya cak.

*Bayan awa uku*

Sallar magrib ma labeeb bai sameta cikin jam'i ba. Sanda ya karasa masallaci an idar mutane ma har sun soma fitowa.

Dan haka yayi tashi shi kadai, bayan ya idar ne ya fito tunanin ya kira Ateefa ya fado mishi, dan haka ya dauko wayarshi.

Dialing ya sake yi a karo na hudu, har tai ringing ta gama bata dauka ba, ya dafe kanshi. Text ya tura mata :

"Tee ya kike so inyi? In zaki horani banki ba, karki hadamun da kanki da baby. Stay safe, bansan ko karfe nawa zan dawo ba. Love you"

Sai da yaga ya shiga sannan ya mayar da wayar aljihunshi yana komawa cikin asibitin. Har lokacin dawud bai tashi ba, dan doc ya cema labeeb din ya samu concussion a kanshi.

Amman da wadataccen hutu babu wata matsala da za'a samu. Kujera labeeb yaja ya zauna, yana dafe fuskar shi cikin hannuwanshi.

"Ciki gare ni wata uku!!!"

Maganar zulfa ta doki kunnuwanshi, da sauri ya bude fuskarshi yana jan numfashi, lokaci daya iskar dake dakin ta daina wadatar dashi.

Yanzun kalamanta guda biyar suke mishi yawo, nauyinsu da komai nasu ke ziyartarshi. Ciki zulfa take dashi. Ciki gareta har wata uku!

Da sauri sauri yake fitar da numfashi yana rasa kalar abinda yake ji, yadai san ko wanne kala ne yana da alaka da zuciyarshi saboda kunan da take.

Yaga abubuwa da dama, yaji abubuwa kala kala, da yawan su sun faru akan shi, amman bai taba sanin tashin hankali irin wannan ba.

RAYUWAR MUWhere stories live. Discover now