21

7.9K 624 250
                                    

Dakyar ya samu ya banbare ta daga jikinshi yana maida numfashi. Kokarin sake janyo shi take ya hankade ta.

"Stay the fuck away!"

Ya fadi yana matsawa sosai kaman tsoron yarinyar yake, hannu yasa ya dafe kanshi yana runtsa idanuwa. Ya rasa meke damunshi haka.

Tun bayan zaphira sam ya kasa hada shimfida da wata, kaman auren da yayi ya canza wani abu tare dashi daya kasa ganewa. Da duk wani salo da yarinyar zatai mishi duk mun kwarewarta sai yaji kaman dauda take liqa mishi a jiki.

Kaman hannuwanta nabar mishi marks a zuciyarshi da jikinshi. Daudar, zunubi da kazantar zina yake ji yanzun. Ya ji yanda zuciyarshi tai mishi haske da kalar nutsuwar da ya samu tare da zaphira.

Baya son zuciyarshi ta sake ziyartar duhun dake cikin zina. Sakko kafafuwanshi yai daga kan gadon. Ya dauki dogon wandonshi dake kasa, kudi ya dauko batare daya juya ya sake kallon yarinyar ba ya mika mata.

"Tashi ki fitarmun"

Ya fadi, hannu tasa ta karbi kudin, ta mike ta mayar da kayanta tana mamakin kalar El-Maska. Bata damu ba tunda taji dumus. Ficewa tai daga dakin.

Yana jin dokawar kofarta ya sauke numfashi yana mikewa kasa kasa yake fadin.

"Wani abu ya sake canzawa tare dani"

Ya jima yana zaune yana nazarin rayuwa kamun ya tashi ya shiga toilet ya tsarkake jikinshi ya dauro alwalar Asr ya fito.

Yasan kamun yakai masallaci an idar da sallah dan haka yai sallar shi a gida. Wayar zulfa ya nema taqi shiga. Sake fita yai daga bedroom din zuwa falo ya kunna kayan kallo.

Saidai tunda ya zauna yake flipping tsakanin tasha zuwa wata tashar ya kasa samun abin kallo, Komai baya mishi dadi tunda ya tashi, hakan yasa shi fita ya samo yarinya.

Saidai bata kara mishi komai ba sai rashin jin dadin da yake ciki. Kitchen ya nufa ya dauki cup ya bude fridge ya dauko kwalbar giyarshi ya bude ya zuba.

Ya mayar ya dauko kankara ya fasa ya zuba ya dauki cup din yana girgiza shi dan kankarar ta narke ya nufi hanyar falo, bai zauna ba wayarshi ta soma ringing.

Daukarta yayi kan table, yadan runtsa idanuwa ya budesu ganin Asaad ne, dagawa yai da fadin.

"Hello Asaad..."

Hadi da cika bakinshi da giyar dake cikin cup din da kamun ya hadiye Asaad yace mishi.

"Yaya sajdaa...sajda ta rasu!"

Giyar dake bakinshi ya furzar wadda ta fara wucewa ta shaqe shi, tari ya soma yi sosai daya saka shi sake kurba yana hadiyewa da sauri sauri wani tarin na sake bin wani.

Ajiye cup din yayi kan table, yana tarin yace ma Asaad.

"Kace...me? Sajda...menene?"

"Sajda ta rasu yaya!"

Asaad ya sake fadi muryarshi na rawa. Girgiza kai labeeb yake, lokaci daya wani abu na zauna mishi a kirji, babu yanda za'i ace mishi sajda ta rasu.

Sauke wayar yayi daga kunnenshi wata irin zufa na karyo mishi, ko ina jikinshi bari yake, ya rasa abinda zaiyi, gabaki daya komai ya kwance mishi.

Ba karamin kadawa mutuwar tai mishi ba, a lokaci daya kuma da mamaki da tsoro, hannu yasa ya goge bakinshi yana tuna abinda ya aikata dashi mintina ko talatin basuyi ba.

Tsikar jikinshi ce ta tashi, da ace shine ya rasu yanzun da wanne guzuri zai tafi? Me zaice ma Allah, ta ina zai fara bayani. Zuciyarshi ke dokawa da sauri sauri.

Yanda rudin duniya da gangar shaidan ke kada mishi tana mantar dashi cewar mutuwa bata nuna alama, bata bada notice, bata sallama balle ta jira saika shirya.

RAYUWAR MUWhere stories live. Discover now