12

6.8K 651 129
                                    

Da wani irin yanayi ya bude ido, kiran sallar asuba yake ji. Bayanshi yaji ua rike saboda yanayin yanda yai bacci a kishingide.

Zuciyarshi ta doka cike da fargaba kamun lokaci daya komai ya soma dawo mishi, cikin hanzari ya mike yana duba khateeb.

Hannu yasa saitin hancin shi, yaji yana numfashi, ya taba jikinshi yaji komai lafiya kalau. Numfashi mai nauyi ya saki.

Goshinshi dafe da hannu yadan koma yana kishingida tare da mike bayanshi da wuyanshi da suke a rike. Inalillahi wa ina ilaihi raji'un yaci gana da jerowa dan kirjinshi yai nauyi.

Ga dacin da zuciyarshi take, inba wanda aka taba yima rashi ba babu wanda zai fahimci abinda yake ji. Dan gyara yanayin kwanciyarshi yayi, hannunshi nadan taba tayyab.

Da saurin gaske ya janye hannunshi yana mikewa zaune babu shiri. Sai lokacin yakejin nishi nishin da tayyab din ke fitarwa. Hannunshi yasa yana feeling goshin dayyab da wuyanshi.

Zafin zazzabin da yaji saida wani irin tsoro ya kamashi, ba shiri ya tsallake tayyab yana sauka daga kan gadon. Toilet din dakin ya shiga. Zuciyarshi ta sake dokawa.

Ganin toiletries din ummi dake ajiye. Hannu yasa ya dafe kirjinshi yana yamutsa fuska, radadi sosai wajen yake mishi. Ga kanshi yayi wani dumm kaman iska bata je mishi.

A daddafe ya fito daga toilet din yana bude dakin ya fita, nasu dakin ya nufa ya shiga toilet din ciki dan in yace yai amfani dana ummi matsala za'a samu,zuciyarshi bata da wannan karfin a yanzun.

Brush ya fara yi sannan ya daura alwala, ya dauko ma tayyab brush dinshi ya kuma dauko towel, kitchen ya biya ya hado da karamin roba yana zubo ruwa ciki.

Ajiye komai yayi, yana gabatar da sallar asuba tukunna,bazaice ga kaar addu'ar da yayi ba. Yasan dai ummi ce kadai a cikinta, dan bashida wata wadatacciyar nutsuwa.

Tsugunne yake kan gwiwar shi, a hankali yake girgiza tayyab wanda ya bude idanuwanshi dakyar.

"Yaya banda lafiya...."

Muryar shina dishe ya fadi. A sanyaye dawud ya amsa shi da

"Nasani tayyab, zaka iya tashi kai sallah"

Yana kallo ya dan daga mishi kai dakyar. Hannunshi ya kama yana taimaka mishi ya mike zaune. Towel din ya saka cikin ruwa ya matse ya soma goge ma tayyab jiki dashi.

Muryarshi na rawa yace.

"Da sanyi sosai"

"Kai hakuri tayyab, jikinka yai zafi sosai shisa"

Shiru tayyab yayi, yabar dawud din yana kula dashi, bashi yake so ba, yasan yanada hankalin da ya kamata kar yaji abinda yake ji a yanzun.

Ummi yake so, wani karamin waje a zuciyarshi ya kwanta da fatan ya bude idanuwa yaga duk abinda ya faru jiya ba komai bane sai mummunan mafarki.

Zazzabin daya farkar dashi tsakiyar dare kawai ya tabbatar mishi da hakan abune da bazai yiwu ba. Ba abinda yake son gani sai ummi a yanzun.

Muryarta yake son ji, ruwa dawud yaji mai dumi ya digo kan hannunshi, hakan yasa shi dago kai, runtsa idanuwanshi yayi yana bude su kan tayyab ganin hawayen dake zubo mishi.

"Kukan nan yasa ka maka zazzabi tayyab, gashi bansan yanda zan baka hakuri ba....."

Dawud ya fadi yanajin shi so helpless, kamub tayyab ya amsa shi khateeb ya tashi yana tsanyara kuka. Cikin hanzari dawud ya mike yana bude net din ya dauko shi.

Yasan dole yai kuka, ya isa ace yanajin yunwa, ga wanka tun wanda akai mishi ne a asibiti, maganan wanka yasa dawud tuna rabon su da wanka kwana biyu kenan.

RAYUWAR MUWhere stories live. Discover now