20

7.6K 603 172
                                    

Hannu yasa ya mayar ma da zaphira gashinta daya zubo kan fuskarta, bacci take sosai, dan ko da yasa hannunshi ya shafi fuskarta bata motsa ba.

Dakyar ya samu ta tashi tai sallar asuba. Bai taba dauka wani abu zai canza tsakaninta da sauran matan da yake bi a waje ba sai daren jiya.

Mamakin kalar nutsuwar daya samu shine abinda ya hanashi bacci. Ya dauka mata duk kalarsu daya. Sai jiya yagane matarka da aka kulla igiyar aure tsakanin ku koda babu soyayya tana da banbanci tsakanin ta da matan banzan ka na waje.

Tattare da nutsuwar da yakan samu a wajen matan shi na waje yakan zo cike da tsana, kyamata, dana sani da jin daudar zunuban da ya dauka na aikata zina.

Zunuban da ko bacci yake yana jin nauyin su, sai gashi a karo na farko yagane daraja daya daga cikin dubban dake tattare da matar da take halattacciya a wajenka.

Har yanzun babu soyayyar zaphira ko digo a zuciyarshi. Ya dauki abinda ya hadasu a matsayin abinda ya dace yayi, da dabara ya zame hannunta dake kan jikinshi ya sauko daga kan gadon.

Lokaci daya maganganun da zainab tayi daren jiya wajen partyn shi ya fado mishi. Zuciyarshi tai wata irin dokawa. Zainab ta bada shaida akanshi bisa abinda ta sani na halayyarshi.

Ta bada shaida cewar zai riqe zaphira da gaskiya gaban mutane batare da shakkun komai ba. Dafe kai yayi.

"Haba zeezee..."

Ya furta a hankali yanajin yanda Maganganunta suka sake daure shi. Bandaki ya shiga ya sake wanka ya fito. Three piece suit ya saka a jikinshi banda vest din.

Cikin kanshi yake calculating raba dakin kwana da zaphira dan yasan akwai randa zaiso kwanciya shi kadai. Turaruka ya duba, babu kalar nashi ko daya, haka yadan fesa wasu daga cikin wanda yagani.

Ya duba mukullin mota, harya nufi kofa ya dawo, dube dube yake kozai samu yar takarda da biro dan yabarma zaphira sakon cewa ya fita ya samo musu abinda zasu karya dashi.

Bai samu ba, sauke numfashi yayi a gefe daya yanajin wata takura ta daban. Bai saba ma kowa bayanin cewa zai fita ba. In yaga su Asaad a falo yai musu sallama, in bai gani ba ya wuce abinshi.

Yanzun ma da bai samu takardar da biro ba ficewa yayi tunda yasan ba dadewa zai ba. Harya sauka kasa yaga babu mota ko daya sai wadda suka dawo gida cikinta jiya.

Sai yanzun cikin haske sosai yake ganin kwalliyar dake jikin motar, lumshe idanuwanshi yayi, yanzun ina zaije da mota haka. Wayarshi ya laluba ya tuna yabarta daki.

Dan karamin tsaki yaja yana koma cikin gidan. Har dakin ya shiga ya dauki wayar, Mamdud ya kira wayarshi a kashe, haryai dialing number din zulfa yai sauri ya kashe kamun ta shiga.

Asaad ya kira ya fada mishi abinda zai siyo ya kawo mishi. Takalman kafarshi ya cire ya koma kan gadon ya zauna yana jingina bayanshi jikin kan gadon.

A hankali zaphira ta bude idanuwanta ta sauke su kan fuskar labeeb, dan guntun murmushi yai mata.

"Hey lazy bones"

Ya fadi da wasa tattare da muryarshi, pillow din dake gefenshi ta ja tana kare fuskarta. Murmushi labeeb yayi.

"Zaki iya tashi ko in tayaki?"

Ya bukata, pillow din ta cire hade da girgiza mishi kai. Sauka tai daga kan gadon tana nufar toilet, labeeb ya bita da kallo. Duk inda ake son mace takai zaphira takai dan dai ko kadan baya jinta a ranshi.

Yana nan zaune ta fito daure da towel, wayarshi da kira ya shigo ne yasa shi dauke idanuwanshi daga kanta, ganij asaad ne yasa shi mikewa ya fice daga dakin.

RAYUWAR MUWhere stories live. Discover now