25

6.9K 707 464
                                    

Chapter din nan ta tabani fiye da yanda zata taba ku. Addu'o'inku na samuna a koda yaushe. Banda bakin godiya, a duk inda kuke, Allah ya tabbatar muku da dukkan alkhairi.

Ina kaunarku fiye da yanda kuke kaunar Rayuwar Mu. Nagode sosai sosai 😍

Sallar magrib kawai yayi, saida ya kira anty ya tambayeta asibitin da suke kamun ya fadama mami yaje duba yumna. Tukunna ya sauko ya dauki mota.

Saida ya tsaya kan hanya ya siya musu fruits mai yawa tukunna ya karasa. Da sallama ya tura kofar dakin. Daga ita sai anty.

Idanuwanshi ya tsaida akan yumna da take kwance tana bacci, fuskarta, yanayinta da komai suka zauna a zuciyar shi da wani yanayi na daban.

Har a fatarshi yanajin igiyoyin da suka kulle su tare, yanajin hijabin dake tsakanin su ta yaye. Yanajin yanda zai kalleta duk yanda yake so, yanda ta zama halaliyar shi.

A duk yau, itace abu na farko mai kyau daya faru dashi, abu guda daya da yasa shi yake tsaye akan kafafuwanshi a yanzun.

"Dawud..."

Anty ta fadi a sanyaye, sai yaji kunya ta rufe shi, sam ya manta gaishe da ita ya kamata yayi. Karasawa yai cikin dakin sosai ya ajiye ledar dake hannunshi a kasa hadi da fadin.

"Anty ina wuni? Ya mai jiki? Sannu da kokari"

Cike da tausayawa ta kalle shi, da raunukan dake fuskarshi. Tasan duk wahalar da sukai kamun su kawo inda suke yanzun.

"Da sauqi, sannu kaima, Allah yasa yau ya zama karshen wahalhalun ku"

"Hmm..."

Kawai dawud ya iya amsawa, addu'ar ta na tabashi fiye da zatonta, yau zai zama karshen wahala a rayuwar yumna. Zai tabbatar da hakan.

Saidai bashida tabbas a tashi rayuwar da sabon hargitsin daya kunno musu. Kujera yaja ya zauna. A koda yaushe mutum ya zauna yakan samu wata nutsuwa ko yaya take.

Musamman shi daya samu awanni a tsaye, amman babu abinda zamanshi ya saukar mishi banda sabon tunani. Shiru suka zauna kowa da saqe saqen da yake a zuciyarshi.

Kamun dawud ya kalli anty, yasan tana da nata iyalan da suke bukatar kulawarta, iya kokari da karamci babu wanda batai musu ba.

"Anty bazan iya gode miki ba, babu kalaman da zan amfani dasu, addu'a ita kadai zan iya miki.

Nasan kina da naki hidimomin, zan kwana da yumna yau"

Kallon shi tai sosai

"Bakomai wallahi, in kana da hidimomin ka kaje, zan iya sake kwana"

Girgiza mata kai yayi, yumna na karkashin kulawarshi yanzun, tana cikin hidimonin shi.

"Babu abinda zanyi"

Sauke numfashi anty tayi ta mike, yan kayanta ta tattara, daman jikinta sanye yake da hijab dinta. Mikewa dawud yayi yana zaro wallet dinshi, dubu biyar ya zaro.

"Kihau mota anty"

Dakyar ya samu ta karba, saida ya dibar mata rabin fruits din yace takaima yara tukunna sukai sallama da cewa zasu yi waya.

Hannuwanshi dawud yasa ya dafe kanshi dasu yana maida numfashi, sai yanzun ciwukan dake jikinshi wanda ba daga ciki suke ba suke mishi zafi.

Ko ina na jikinshi ciwo yake, ga jirin da yake gani. Magunguna yake bukata, yasani, pain killers da kuma na hawan jinin shi.

Bazai iya barin yumna ita kadai ba, karta tashi tana bukatar wani abu, sosai yaja kujerarshi daf da gadon ya dora kanshi a jiki.

Sai yanzun yake tuna tun jiya da rana rabon cikinshi da wani abu, shima saida mami ta tsare shi tukunna yaci. Shi kadai ma ya isa yasaka shi jirin da yake ji.

RAYUWAR MUWhere stories live. Discover now