23

7.6K 634 377
                                    

Mamdud ke tuqin amman hakan bai hanashi ganin nishadin dake fuskar labeeb ba har suka karasa Naf club. Fita daga motar zaiyi yace.

"What is up with you yau din nan?"

Murmushi labeeb yayi har hakoranshi suka fito.

"Me ka gani?"

Ya bukata yana dan ware idanuwa. Girgiza kai kawai Mamdud yayi yana zare key din motar ya fice. Dariya labeeb yayi shima ya fito daga motar.

Da nishadi marar misaltuwa a tare da labeeb suka shiga Naf club. Yanayin music din dake tashi a wajen yayi dai-dai da abinda yake ji.

Hannuwanshi ya fara tafawa kamun ya soma rawa sosai, Mamdud kujera ya samu a bar din wajen ya zauna yana kallon yanda shigowar labeeb din taja hankalin mutane.

Yanda kowa yayi wajenshi suna rawa tare, karamin tsaki yaja. Wata yarinya da Mamdud bazai iya tuna sunanta ba, amman dai yasan ta ta karaso.

Jikinshi zata hau ya tureta da fadin.

"Ba abinda ya kawoni kenan ba"

Tabe baki tayi tana watsa mishi wani kallo kamun ta wuce abinta. Normal hadin da akan mishi bartender din wajen ya hada ya miko mishi.

Kudin Mamdud ya zaro a aljihunshi ya mika mishi hadi da ture cup din yana girgiza kai. Ya jima da barin shan komai, hakama mata, tun shigowar Ateefa rayuwar shi ya ajiye komai.

Daman can bai taba hangoma kanshi rayuwa kalar wannan ba. Gyara zamanshi yayi yana kallon labeeb na cashewa abinshi, sun cakude waje daya harda mata.

Hannuwan wata tsaf a kugun labeeb din, bai ko nuna hakan ya dame shi ba. Wasu lokutta har mamaki yakan ba Mamdud, komai yanayi kaman abin yazo mishi natural ne batare da koyo ba.

Abin na bashi takaici ba kadan ba, mikewa yayi yaje ya kamo hannun labeeb yana janshi wata yarinya kalar shuwa ta kama dayan hannun labeeb din.

Dariya labeeb yayi yana kallon Mamdud dake fassara 'ka sakar mata ni'. Yarinyar Mamdud ya kalla, muryarshi a dake yace

"Sake shi!"

Ganin ba da wasa yake ba yasata sakin shi. Janshi Mamdud yayi suna barin floor din rawar gabaki daya.

"Gida zamu tafi"

"What? Yanzun? Bamu dade da zuwa bafa"

Labeeb ya fadi yana kallon Mamdud daya saki hannunshi yana nufar hanyar da zata fitar dasu daga club din. Dole yabi bayanshi yana mita cewar shi bai gama having fun ba.

Ko kulashi Mamdud baiyi ba har suka shiga mota, fun din dayaga labeeb na having ne yasa shi jin bayason zaman club din kwata kwata, gara su koma gida suyi bacci.

Gidan kuwa suka koma, dakin su labeeb ya wuce yana barin Mamdud anan falo zaune. Saida ya fara watsa ruwa sannan ya kwanta, bai jima ba bacci ya dauke shi.

*

Da Ateefa manne a zuciyarshi ya farka safiyar ranar, sai dai jinta da yake bai hana mishi yin hidimarshi ta ranar lafiya kalau ba.

Bai samu zama free ba sai bayan azahar, komai bai sakama cikinshi ba duk ranar haka ya kama hanya yana nufar gidanshi. Sai dai yana mamaki, yasan ya kamata ace gabanshi na faduwa ko makamancin hakan.

Amman bai tabajin tabbaci akan komai ba a rayuwarshi irin soyayyar Ateefa, ko dar bayaji na shakkun cewar ba zata amince dashi ba. Yanda yake ji, yanayin da zuciyarshi take ciki ya tabbatar anyi ta ne kawai dan ita.

Yana da yaqinin bazai ji hakan ba inhar bazai same ta ba. Parking yayi ya bude gate din sai lokacin ya kula hannunshi na bari a hankali. Murmushi yayi ya wuce ya shigar da motar.

RAYUWAR MUWhere stories live. Discover now