02

8K 749 89
                                    

Ba masu yawan kudi a account bane mawadata. Ba masu katon gida bane masu rufin asiri. Ba masu tarin motoci bane manyan mutane.

Mawadata sune masu godiya da abinda suke dashi a koda yaushe. Mawadata sune masu hangen wanda bashida abinda su suke dashi.

Masu rufin asiri sune wanda suke da lafiya da kwanciyar hankali. Masu rufin asiri sune wanda zuciyarsu take a wanke babu hassada ko kadan a cikinta.

Manyan mutane sune masu darajta na kasa dasu. Masu girmama na gaba dasu. Allah ya datar damu. (Amin Ya Rabb)

Yakai mintina sha biyar kofar gidan su Yumna yana kiran wayarta bata picking. Hankalinshi ya soma tashi.

Wata yarinya yagani. Ya aiketa cikin gidan ta kira mishi ita. Sai ta dawo tace ance bata gidan. Yasan karya ne.

Wayar El ya kira. Not reachable.

"Damn..."

Ya fadi yana running hannunshi cikin sumar kanshi. Ya sake gwada number din yumna. Wannan karin dagawa tayi.

"Kinsan me kikayi kuwa? Kinsan in na shigo cikin gidan nan abin bazai kyau ba.

Ki fito in kaiki gidan aunty binta"

Muryarta can kasa tace.

"Sun tafi ma. May be kawai na tsorata ne. Ka koma in shaa Allah ba abinda zai faru"

Girgiza mata kai yake kaman tana ganinshi.

"Ki fito yumna. Ban yarda da zamanki a gidan nan ba. Banma san me yasa kika dawo ba"

Muryarta a tausa she ta amsa shi da.

"Ya zanyi to? Ina bukatar albarka baba ko ya take a auren nan. Nasan kome yake faruwa ba laifinshi bane ba"

Sauke numfashi yayi. Ji yake kaman ya janyo goben tazo ya dauketa daga wannan kangin da take ciki. Dan yafi kowa fahimtar halin da take ciki.

"*Rayuwar Mu* kenan Yumna. Tamu kaddarar da wannan kalar tazo."

Da yarda da abinda ya fadi a muryarta tace.

"Allah yasan damu. Yasan zamu iya dauka shisa ya dora mana. Kwana daya ya rage"

Fara.a wahalar bayyana take a fuskarshi saboda dalilai da yawa.

"Allah ya kaimu goben. Ki kula da kanki please. In kinga abinda baki yarda dashi ba ki kirani"

Saida tai alkawarin ko ya wani abu ya faru zata kira shi tukunna sukai sallama ya shiga mota ya juya.

****

Taji wani iri data taso Dawud. Tasan bazai rasa hidimar da yake yi ba ya ajiyeta ya taho.

Ita kanta bata san dalilin tsoron ba. Kawayen Mami taga sunzo suna kallonta tazo wucewa.

Ta sake fitowa taga sun mike suna nufota. Mami zata iya komai dan ganin auren nan ya fasu. Dan gara taga mutuwar yumna data ganta nutse a gidan dawud kuma tasan hakan.

Jin shiru hayaniyarsu da take ji a falo ta yi shiru yasata mikewa ta kasa kunnenta jikin kyauren dakin. Still babu wani motsi. Sauke ajiyar zuciya tayi.

Wata irin azababbiyar yunwa ke addabarta. A hankali ta bude dakin ta fito. Cikin sanda take takawa zuwa kitchen.

Yanayin shirun gidan kaman ba gobe daurin aurenta ba bai dameta ba. Ba taron biki bane a gabanta. Ta zama mallakin dawud shine bukatarta.

Tana shiga plate ta dauka ta bude warmer ta soma zuba shinkafar dake ciki. Kaman daga sama taji muryar mami.

"Munafuka. Uwarki ta dafamun abincin?"

RAYUWAR MUWhere stories live. Discover now