26

6.3K 559 517
                                    

Tun farko banyi alkawarin tafiyar nan mai sauki bace ba kaman yanda banyi alkawarin happily ever after ba. Saboda ban yarda dashi ba. Na yarda da farin ciki lokaci zuwa lokaci.

Duk wani emotions tare muke yin shi, duk wani page da ya taba ku saida ya fara tabani. Ku kara hakuri, cikin kashi uku na tafiyar daya kawai ya rage mana.

Ina kaunar ku dukkan ku. Nagode da kwarin gwiwa, addu'oi, da kuma yanda kuke bina. #AnaTare irin sosai da sosai.

Yana shiga bangaren su dakin shi ya wuce. Sai da yakai bakin kofa tukunna ya tuna yanda ya birkita komai na ciki. Lumshe idanuwanshi yayi, baisan meke damun shi haka ba in ranshi ya baci.

A hankali yasa hannu kan handle din kofar ya tura, kayanshi kawai zai dauka ya wuce dakin Tayyab ya sake yin wanka ya canza.

Ga mamakin shi dakin yagani fayau, duk abinda ya hargitsa an mayar dana mayarwa. Wanda ya fasa an kwashe, komai yai fes. Kamshin room freshner din dake dakin yasa shi sanin tayyab ne yai gyaran.

Numfashi yaja mai nauyi yana sauke shi, ya cire takalmanshi sannan ya tura kofar ya na shiga cikin dakin sosai, toilet ya nufa ya sake yin wanka ya fito.

Jeans ya dauka baki da farar riga ya saka, turaruka kawai ya iya fesa ma jikinshi ya koma kan gado ya zauna. Ya rasa yanda zaiyi kewar ummi da yake ji tun jiya tai mishi sauki.

Balle kuma abba, dayai mishi tsaye a wuya da wani irin yanayi. Mikewa yayi ya fito daga dakin. A karo na farko tun dawowar su gidan da kafafuwan shi suka dauke shi zuwa bangarensu abba.

Zuciyar shi ke dokawa kaman zata fito daga kirjinshi har ya karasa. Yai tsaye bakin kofar yana maida numfashi kaman wanda yaci gudu na tsayin lokaci.

Duka jikinshi ya mishi nauyi. Baisan iya lokacin daya dauka tsaye kofar dakin ba, yana shirin juyawa aka bude dakin. Idanuwa abba ya sauke kan dawud, fuskarshi na nuna mamakin da yake ji na ganin Dawud din.

Akwai wani abu tattare da dawud din, yanayi da abba ya kasa fassarawa. Wani abu na daukar zafi cikin kanshi.

"Dawud lafiya dai ko?"

Sosai dawud din yake kallon shi, abubuwa kala-kala na mishi yawo cikin kanshi. Searching yake yana neman abbanshi daya sani, abbanshi da zai kalle shi yasan yana cikin damuwa tun kamun ya furta.

Abbanshi da yake zama tare dashi su warware duk wata matsala. Abbanshi da shine karfin gwiwar shi, abban shi da yake nuna mishi yanda zaiyi da kome ya taso mishi.

Zuciyar shi ta sake budewa wajajen duk da babu ciwuka suka samu nasu ganin babu abban shi. Wannan mutumin tsaye a gabanshi wani ne daban.

Muryarshi a dakushe yace

"Abu nazo nema kuma bangani ba"

Kamun abba yace wani abu dawud ya juya ya tafi. Hannu abba yasa yana dafe kanshi daya ke sarawa kaman ana buga mishi wani abu. Dole ya koma daki yana fasa fitar dayai niyyar yi.

Bakin kofar dakin shi ya tsaya yana dan dafe kai, bai ma san abinda ya dauke shi yakai shi bangaren abba ba. Baisan me yake nema ba.

Ya riga da ya binne abban shi shekaru masu yawa tun kamun yaga gawarshi, ya kamata har zuciyar shi ya hakura dashi kaman yanda ya hakura da dawowar ummi.

Su duka sun barsu a duniya mai cike da rikici, sun barsu batare da sun san yanda zasuyi da rayuwa ba.

"Yaya..."

Kaman daga sama muryar zulfa ta katse mishi tunanin da yake yi, da sauri ya juyo yana karasawa inda take tsaye. Hannunshi ya fara sakawa ya taba fuskarta yaji babu zazzabi a jikinta. Tukunna ya kalleta sosai yace

RAYUWAR MUWhere stories live. Discover now