35

9.1K 654 200
                                    

*Epilogue*

*BAYAN SHEKARA BIYAR*

"Ummi ruwa..."

Arif ya fadi yana riko Ateefa dake kokarin maida kayan da Iman mai sunan mummyn su Labeeb wato Habiba ta janyo mata. Juyowa tayi tana jin kaman ta kwada ma Iman din mari

"Ban ma hanaki shigomun daki kimun jaye-jaye bane?"

Shagwabe mata fuska Iman tayi hawaye fal idanuwanta.

"Hijab din ne bangani ba wanda Amu ta siyomun rannan"

Iman ta fadi hawaye na zubo mata. Arif ta kalla

"Sake mun kafa. Ba akwai ruwa a gefen gado ba yanzun na fito dashi?"

"Dan Allah ummi ki dauko mun"

Iman ta fadi wasu hawayen na zubo mata.

"Zaki bani waje ko saina kwada miki mari?"

Ateefa ta fadi fuskarta babu alamun wasa, wucewa Iman tayi tana kuka. A bakin kofa taci karo da zulfa da a shekaru biyar din nan da suka wuce musu kaman wata biyar. Tun Labeeb na kaita asibiti harta ce mishi su hakura kan haihuwa.

Sai gashi da suka barma Allah komai yanzun cikine wata uku a jikinta. Iman na ganinta ta ruga da gudu wajenta.

"Amu..."

"Waye a gidan nan baison zaman lafiya ya taba mun Iman dina?"

Zulfa ta fadi tana sa hannu ta goge ma Iman din fuska. Dai-dai lokacin da Ateefa ta fito daga daki, Iman ke fadin

"Ummi ce taqi dauko mun hijab dina da kika siyomun..."

"Kinga kayan da yarinyar nan ta janyo mun? Nama hanata kawomun kayanta dakina bata jin magana"

Rike Iman zulfa tayi tana murmushi

"Tunda baki dauko mata hijab din ba saikin samun ita kuka?"

Labeeb ne ya shigo da sallamar shi. Da gudu Iman ta karasa tana tarbarshi.

"Abbu sannu da zuwa"

Daga ta yayi yana karasowa inda suke, banda sajen dake fuskarshi shekarun nan biyar haka suka wuce basu nuna komai a jikin shi ba. Kaman yanda yace musu baisan yanda zaiyi wani abun banda harkar film ba, sai dai akwai acting din da bazai iya ba yanzun saboda yaranshi.

Akwai abubuwa da yawa dazai ajiye domin kare mutuncin su. Dan haka kacokan ya matsa ma sauran sabbin stars dake tasowa waje ya koma bangaren production.

"Har yanzun baku shirya ba wai?"

Ya tambaya yana kallon su.

"Ni Hijab dina kawai zan dauko"

Zulfa ta fadi.

"Abbu... Ummi taki dauko mun nawa"

Ateefa ya kalla

"A dauko mata hijab dinta"

"Banganshi ba nikam... Bama najin yana dakina"

Ware mata idanuwa Labeeb yayi.

"Dan Allah ki duba mata tunda shi take son sawa"

"Kai da zulfa kuna bata yarinyar nan wallahi...kaman Iman sai abinda take so ne dole za'ayi"

Karasawa inda Labeeb yake zulfa tayi ta karbi Iman daga hannunshi.

"Bari muje mu dubo wani ko?"

Sumbatar zulfa Iman tayi a kuncin ta

"I love my Amu"

Ta fadi, mayar mata da sumbar Ateefa tayi

"Amu love Iman da yawa..."

RAYUWAR MUWhere stories live. Discover now