03

6.6K 815 74
                                    

Kar ya zama kaga kaman addu'ar ka bata karbuwa dan kayi shekaru kana neman abu daya baka samu ba.

Komai yana da dalili. Komai yana da sanadi. Komai kuma yana da lokaci. Karkayi gaggawa a al'amuranka.

Dalilin zai iya zama baka Addu'ar taka da dukkan imaninka. Babu yarda a lokacin addu'arka. Kasa kokwanto a ciki. Kai addu'a kana mai mika komai wa Allah.

Sanadin zai iya zama kankanin abu daka raina. Abinda kake ganin bai kai ba. Karka zama mai raini a al'amura ko ta wacce fuska suka zo maka.

Lokacin zai iya zama a duniya sai dai zai zo da jinkiri. Ka zamana mai yawan hakuri. Lokacin zai iya zuwa sai a lahira saboda shine mafi alkhairi a gareka. Ka zama nai godiya. Allah ya datar damu (Amin thumma amin)

Tuna baya. (Rayuwar dawud)

Da zai iya dora kalmar 'Perfect' zai kira family dinshi da haka. Tun tasowarshi bai san wani tashin hankali ba balle bacin rai.

Ba masu kudi bane su. Sai dai suna da rufin asiri dai dai gwargwado. Dan babu abinda suka nema suka rasa ta bangaren abinci. Suttura da makaranta me kyau dai dai karfin abban su.

Yakan yi mamaki in yaji ance mata da miji na fada. Dan bai taba gani a nasu gidan ba. Maman shi da Aisha da suke kira da ummi mata ce mai hakuri da kauda kai a al.amura.

Haka rayuwa taci gaba da tafiyar musu da sauyi na ci gaba har lokacin da Dawud ya shiga aji biyar secondary.

Bazai manta ranar talatar da tazo musu a hargitse. Talatar da tai digo a rayuwar su dayai sanadin canza musu komai. Kaman yanda ya saba.

Da sallama ya shiga gidan nasu yana dorawa da.

"Sajda...."

Baiji motsinta ba. Takalman shi ya cire ya ajiye gefe. Ya taka zuwa cikin folonsu. Ummi ya samu zaune da alama ko shigowar shi bata ji ba saboda zurfin da tayi cikin tunani.

Jakar makarantar shi ya ajiye ya zauna gefenta. Hawaye ne a fuskarta abinda bai taba gani ba. A tsorace ya dafa hannunta yana fadin.

"Ummi?"

Sai lokacin ta jishi. Hannu tasa da sauri tana goge fuskarta. Kamun ta dora murmushi a fuskar ta kalle shi sa cewa.

"Dawud. Har an dawo. Ya makarantar?"

Sam bai yarda da murmushin ta ba. Yasan akwai matsala.

"Ummi me yake faruwa ne?"

Girgiza mishi kai tayi.

"Kaje kitchen ka dauki abincin ka"

Gyara zama yayi. Yunwar daya shigo da ita ta dauke gabaki daya. In akwai abinda ya tsana a zuciyarshi bai wuce ganin ummi cikin damuwa ba.

Muryar shi da rauni a cikinta yace.

"Ummi ki fadamun ko menene. Bazan iya cin abincin nan ba bayan nasan da damuwa a tattare dake"

Wani numfashi yaga taja tana fitar dashi. Kamun tace.

"Na fada maka za.a rage ma.aikata a company din abbanku ai ko?"

Kai ya daga mata. Ya tuna amman sam abin bai dame shi ba. Dan bai kawo ma ranshi zai shafe su ba. Abba na komai babu ha.inci a cikinshi.

"To harda shi aka sallama a cikin su. Tun jiya abin ya faru. Ban fada maka bane saboda muna tunanin wasu cikin manyan wajen da suke mutunci zasu taimaka mishi.

Saidai mutane basu da tabbas Dawud. Sunyi kaman basu ma taba hada hanya dashi ba...."

Ta karasa hawaye na zubo mata. Takai hannu ta goge su. Shiru Dawud yayi yana tauna maganganunta da jinjina ma.anarsu a wajen su.

RAYUWAR MUWhere stories live. Discover now