05

5.8K 583 75
                                    

Please don't skip the note below:

Ina fatan abinda zan fada a yanzun zai canza zuciyar koda mutum biyu ce. Saboda ya canza tunani na gabaki daya.

Na raina naira dari (#100). Ina ganin me zan siya da ita. Sai jiya danaje kasuwa naga wani tsoho yana siyar da yalo. Kallo daya zakai masa kasan yayi yawo harya godema Allah.

Gabaki daya yalon bazai wuce na naira dari biyar ba. Na dauki #100 dani na raina na bashi. Tsohone da zaikai shekaru 70. Hawaye ne cike da idanuwanshi lokacin da yake mun godiya.

Abin ya dame ni sosai da sosai. Maganata anan itace. Abinda ka raina zai iya canza rayuwar wani ta yini daya. Suna nan gefen hanya. Masu saida yalo, abin tsifar kai, igiyar guga, shebir, masu kasa yar albasa da bata wuce kudin powder din da wasun mu ke shafawa ba.

Mu daina dauka yayi kadan. Naira ashirin in kuka bayar yan uwa zata zama mai ma'ana a awa daya na rayuwar wani. Ku fara daga yau.

Karku jira ku samu da yawa kamun ku bayar. Karku jira ranar da baku da tabbas din zuwanta. Kuyi amfani da ranar da kuka gani ku bayyana murmushi a fuskar wani bawan Allah.

Abinda ka raina shi wani yake nema rayuwarshi ta canza ta rana daya. Dan Allah ku duba. Kuyi ko sau daya. Ku tura gaba wani yagani. In ba zaka iya canzawa da bayarwa ba ka tura sakon yaje gaba.

In wani ya karanta ya aikata zai zama kana da kaso a ciki. Allah ya bamu mu taimaka. Allah ya horema al'ummar shi (Amin thumma amin)

Nagode da lokacin ku.

®
✏📖
FIKRA WRITER'S ASSOCIATION.

Sati biyu kenan. Ba Auwal kadai ba. Hatta ita Aisha zatace Allah ya sanya musu albarka a kasuwancin daya fara. Kaman daman can duk wasu kofofin samun shi suna cikin kasuwancin.

Gane hakanne baiyi ba. Kuma su duka sunji dadi da yaya yabarshi nan garin kaduna. Daman yanata saka yara a harkar shi ta nan din. Mutane babu amana.

Sanin su auwal din basu da ra'ayi ne yasa shi bai neme su ba. Saida yaje da kanshi yai masa magana.

*

Zaune suke tana taya sajda yin assignment dinta dawud ya shigo da sallamar shi.

Littafin dake hannun ummi sajda ta karbe da gudu ta karasa inda wajen dawud din tun kamun ya zauna.

"Yaya zo ka koyamin"

"Inyee. Lallai sajda. Kamun kiga yayan wayake tayaki"

Dariya tayi hadi da fadin.

"Daman fa shi nake jira"

Karbar littafin yayi daga hannunta suka karasa inda ummi ke zaune kan tabarma. Zama yayi. Sajda tana gefenshi.

Gabaki daya hannuwanta kan cinyarshi suke. Ya kalleta hadi da fadin.

"Sajda son jikinki yai yawa wallahi. Dagani"

Turo baki tayi tana shagwabe mishi fuska. Girgiza kai kawai yayi ya kalli ummi da fadin.

"Sannu da zama ummi. Naji gidan shiru. Ina su tayyab?"

Murmushi ummi tayi.

"Tayyab sun fita da abokanshi. Zulfa kuma labeeb ne yazo"

Da fara'a dawud yace.

"Yaushe ya dawo?"

"Yace dazun da safe. Amman zai fita anjima koda zakaje ku gaisa da dare zaka same shi"

Jinjina kai Dawud yayi. Daga fara'ar dake fuskarshi zaka gane kusancin dake tsakanin su da labeeb din.

"Tare suka tafi da zulfa?"

RAYUWAR MUHikayelerin yaşadığı yer. Şimdi keşfedin