07

5.1K 666 77
                                    

Rayuwa ba komai bace ba face wata makaranta. Kaman yanda makaranta take da ajujuwa mabanbanta. Take dauke da darussa kala kala.

Haka rayuwa take tafiya da banban ci a wajen kowa. Kaman yanda kowanne darasi yake da bukatar abokin taimakawa kamun fahimtar shi.

Haka rayuwar take tafiya. Bazai rage ka da komai ba idan ka taimaka yayin da bukatar hakan tazo. Ka taimaka da zuciyarka daya.

Ko a wane hali. Ko a wane yanayi zakai bukatar taimako a taka rayuwar. Ba lallai sai a wajen dan uwanka dan adam zaka iya nema ba.

Dan kar kai tunanin matsayin daka kai a rayuwa. Kai tunanin baka da bukatar taimakon kowa. Kana da tarin bukatu a wajen Allah. Alfarma abu ne mai girma. Allah ka datar damu (Amin thumma amin)

Yau sati daya kenan da maganar kara auren Auwal. Wani abu daya danganci hakan bai sake hada su. Asalima babu abinda ya shiga tsakaninsu.

Abin kara gaba yake yi. Addu'a take ba dare ba rana. Dan zaman da suke da dare ma yanzun bayayi. Daya dawo sallar isha'i yake wucewa daki ya kwanta.

Kwana biyu kenan yaran ma basa zama. Kowa na daki. Gidan yayi wani irin shiru. Duk wata walwala tasu da nishadi kaman an yi ruwansu an dauke.

Indai kasan su a da. Kallo daya zakai musu yanzun kasan wani abu ya sauya tattare dasu. Yanzun ma zaune take falo.

Ita kadai da tunani barkatai a zuciyarta. Sajda ta shigo.

"Ummi ina abba?"

A sanyaye ta amsa ta da.

"Bacci yake. Me kika kika kawo a bashi?"

Hade fuska sajda tai hadi da girgiza mata kai.

"Abba baya hira damu yanzun ummi. Munyi laifi ne? Wallahi ina kokari sosai a makaranta. Kice abba yayi hakuri zan sake zuwa na daya in shaa Allah"

Wani abu Aisha taji yai mata tsaye a kirjinta mai zafin gaske. Kamo hannun sajda tayi tana janta jikinta. Cikin taushin murya tace.

"Kin san yanzun abbanku aikin kasuwa yake ko?"

Kai sajda ta daga mata. Fuskarta da alamar bata ga abinda ya hada kasuwar abba da daina hira dasu ba.

"To aikin kasuwa akwai gajiya. Daya dawo jikinshi ciwo yake shisa yake bacci da wuri.

Ba kuyi laifin komai ba. Amman zan mishi magana ya dinga samar muku lokaci kinji ko?"

Cikin idanuwa ta kalli ummin tata tace.

"Zaki masa magana? Zai dinga hira damu kaman da?"

"In shaa Allah"

Murmushi sajda tayi.

"Na tafi in kwanta ummi. Ya zulfa kemun wani tatsuniya mai dadi"

Yar dariya Aisha tayi.

"To maza kije. Karku manta da Addu'a dai"

Fita sajda tayi da gudun ta tana barin dakin. Aisha ta sauke numfashi mai nauyi hade da mikewa ta nufi dakin baccin su.

Kaman kullum a kwanakin nan. Kwance yake can karshen gadon. Ya bata baya. Tasan idonshi biyu ba bacci yake ba.

Bandaki ta shiga ta watsa ruwa. Ta fito ta sa rigar baccin ta. Tahau gadon gefen shi ta zauna. Muryarta babu kwari tace.

"Abban sajda....."

Shiru yayi ya kyaleta.

"Nasan ba bacci kake ba fa"

Muryar shi cike da alamun ta takurashi yace.

RAYUWAR MUWhere stories live. Discover now