31

8.8K 657 208
                                    

Ya rasa abinda ya kamata yaji, ya rasa tunanin da ya kamata ya tsaida zuciyarshi akai. Maganganun zulfa sun warware mishi wani abu dayake qulle da zuciyarshi.

Burin shi daya gama tarwatsewa akan Mamdud yake jin ya dawo. Inda yake zatan Mamdud ya tsallaka da babu dawowa har abada ya canza mishi.

A kasan duk yanayin da yake ji akwai farin ciki na nasara. Zai auri zulfa, zata dawo karkashin kulawarsa gabaki daya, zai daina tashi da fargabar wanda duk ta aura zai iya mata gori akan kaddarar da bata da laifi a ciki.

Yanda ya zaci fitowar gaskiyar cikin zulfa daban da yanda ya faru. Komai yazo cikin sauqi. Wata irin dokawa zuciyar shi tayi.

"Tee..."

Ya furta a fili, yasan yanda ta tsani karya a rayuwar ta, yasan yanda take son ya gaya mata gaskiya koya zatai mata ciwo, sai dai a cikin al'amarin daya faru baida wani zabi daya wuce yi mata karyar.

Sauke numfashi yayi mai nauyin gaske, yana tunanin laifukan dayai mata cikin satikan nan, dakyar ya samu ya ture tunanin ta gefen zuciyarshi. Ba yanzun ba tukunna.

Gani yake asibitin ya kara mishi tsayi yau, da tunani barkatai a zuciyarshi ya karasa harmony yai parking din motarshi. Saida kafafuwan shi suka fara taka cikin asibitin tukunna zuciyarshi tai wani irin matsewa.

Babu abinda yake so yagani sai mamdud din, yaga da gaske ya tashi, Allah kadai yasan yanayin da zuciyarshi take ciki akan mamdud a kwanakin nan, dauriya kawai yake yi saboda su Asaad na bukatar hakan daga gare shi.

Har kasan zuciyarshi yasan bazai iya jure rashin wani dan uwan ba. Yana kuma son magana da su Asaad, a bakinshi suka ji karyar cikin zulfa, a bakinshi ya kamata suji gaskiyar komai.

Zuciyarshi na dokawa da karfin gaske yasha corner din da zata kaishi dakin da Mandud yake. Ko sallama baiyi ba ya tura dakin. Su duka biyun suka juyo suna sauke idanuwan su akanshi.

Wani sanyi-sanyi yaji ganin farin cikin da ke shimfide kan fuskokin su, abinda ya kwana biyu baigani ba, baisan yanda yai kewar ganin su cikin walwala ba sai yanzun. Karasawa yai cikin dakin yana tura kyauren.

Ya maida hankalin shi kan mamdud...an cire mai robar abincin dake hancin shi, haka babu karin ruwa a jikinshi, yanayin fuskarshi yadan canza fiye da kullum da yake ganin kaman baida jini a jikinshi.

"Kuka ce ya farka?"

Labeeb ya fadi muryarshi dauke da wani yanayi.

Kai suka daga mishi, Asaad na amsa shi da

"Ya farka...magunguna ne basu sake shi ba. Bacci ya koma...doc yace ko yaushe zai iya tashi"

Numfashi Labeeb ya sauke yana janyo kujera ya zauna ya fuskanci su Asaad, yanayin fuskarshi yasa Anees fadin

"Yaya lafiya dai ko?"

"Ban ruwa in sha Asaad"

Labeeb ya bukata batare daya amsa tambayar da Anees din yai mishi ba. Ruwan ya bashi yasha sosai tukunna ya kalle su.

"Bansan ta inda zan fara ba... Ina son fada muku wani abu, ku dukan ku. Zee zee bata kusa kuma..."

A dan tsorace Asaad yace

"Menene? Na kira ishaq ma na fada mishi Ya mamdud ya tashi. Kasan zee ban fada mata ba tukunna. Yace in sun samu jirgi yau zasu taho ma... Saboda bata da nutsuwa tunda suka tafi"

Sai da yadan yi jim kamun yace

"Bari tazo din... Maganar zata iya jira"

Nazarin fuskarshi suke, yana jinsu, hakan yasa shi kauda kai gefe yana nutsar da hankalin shi akan mamdud. Sau daya yake son yai maganar nan yanda zai wuce ta har abada.

RAYUWAR MUWhere stories live. Discover now