28

6.8K 641 297
                                    

Hannun tayyab yaji kan kafadar shi yana janyo shi da fadin.

"Yaya fito..."

Tukunna ya kula da su mami basa cikin motar, girgiza kanshi yayi yana sake dafe shi saboda yanda yake jin komai ya mishi shiru a ciki.

Bangaren dake fahimtar abubuwa cikin kanshi ya dauki hutu, saida tayyab ya girgiza shi sosai.

"Yaya... Muna bukatar ka dan Allah... Bansan yazanyi ba. Kamun magana!"

Numfashi dawud yake ja a hankali yana fitar dashi, tukunna yadan daga ma tayyab kai hadi da fitowa daga motar yana tura murfin.

Bin tayyab yayi a baya. Sai lokacin ya kula da asibitin su ne ma tayyab din ya kawo su. Gaisawa yayi da wasu cikin likitocin kamun su wuce.

Tsaye yayi. Dan baisan ina zai soma cewa tayyab yakai shi ba. Wajen abba ko wajen zulfa. Ganin hakan yasa tayyab fadin

"Wajen abba... Mami na tare da zulfa"

Binshi a baya dawud yayi har dakin, a bakin kofa tayyab ya tsaya shi ya shiga ciki.

"Dr. Dawud..."

"Dr. Amir"

Dawud ya amsa shi yana mika mishi hannu.

"Kace ku kuka kawo marar lafiyar"

Kai kawai dawud ya iya daga mishi. Kamun yai mishi bayanin cewar babu abinda ke damun abban banda gajiya. Sunyi sedating dinshi dan ya samu hutu.

Godiya dawud yai mishi, kamun ya fita, kujera dawud ya ja ya zauna saitin abba. Yana jim shigowar tayyab sai dai bashi bane a gabanshi. Abba ya kura ma idanuwa kaman bazai kifta su ba.

Zuciyarshi na nutsuwa da tashin hankalin da ta shiga na tunanin rasa abba. Bazai iya dauka ba, fuskarshi yasa cikin hannuwan shi yana sauke ajiyar zuciya. Wata dariya tayyab yayi da bata da alaka da farin ciki.

Hakan yasa dawud bude fuskar shi ya kalli tayyab din.

"Ina mamaki ne. Na dauka duka mun tsane shi. Na dauka mun hakura dashi tuni... Kalle mu yanzun"

Ya karasa yana nuna kanshi da dawud dake zaune. Cikin wani sanyin murya dawud yace

"In akwai abinda yake da tabbas a *Rayuwar Mu* shine cike take da sabbin abubuwa ko yaushe. Ka zauna tare dashi in duba su mami..."

Dawud ya fadi yana mikewa. Batare da tayyab yace komai ba ya dawo kujerar daya tashi sannan ya kama hanya yana ficewa daga dakin.

Gano mami bai mishi wuya ba, dan asibitin ba bakonshi bane ba, a tsaye ya sameta, kallo daya zakai mata kasan hankalinta ba a kwance yake ba.

Tana ganin shi ta mike daga zauniyar da take. Karasawa yayi yana fadin

"Mami... Ya jikin nata?"

Girgiza mishi kai tayi, tana jin maganar na tsaya mata a wuyanta, saboda wani irin daci da take ji. Dakyar muryarta na rawa tace

"Ban sani ba...jini take ta zubdawa kamun su shiga da ita... Bansani ba... Bazan iya rasata ba ita ma... Bazan iya ba dawud..."

Mami ta karasa maganar hawaye na zubar mata, hannu dawud yasa yana goge mata fuska. Yana jin kaunar ta har cikin zuciyarshi.

"Ba abinda zai same ta mami... Kukan ki zai dagamun hankali. In bakiyi karfin zuciya ba ina zan samu nawa? Ina bukatar mami na...yau zai zomun da sauqi in mami na na tare dani"

Kai tadan daga ma dawud din tana jin shi kamar daga cikin ta ya fito. Kaman ita ta haife su gabaki daya. Allah bai bata haihuwa ba, sai ya kawota rayuwar su dawud ya zaunar dasu a zuciyarta.

RAYUWAR MUWhere stories live. Discover now