04

6K 743 61
                                    

Sauyi na rayuwa yakan zo lokaci daya. Wasu lokuttan sauyi na rayuwa yakan dauki lokaci bai zo ba.

Komai na da alaka da yanda tsarin kaddararka take. Ko yatsun hannuwanka suna da banbanci da junansu.

Saboda me zaka dauka kaddararka iri dayace data waninka? Kar kaga ya samu baka samu ba kai hassada. Kar kaga ya rasa ka samu kai murna.

Ka gode a yayin rashi. Ka gode a yayin samu. Allah na tare dakai a ko wanne yanayi. Allah kasa mu dace (Amin thumma amin)

®
✏📖
FIKRA WRITER'S ASSOCIATION

"Wai har yanzun abba bai dawo ba?"

Dawud ya tambaya yana neman wajen zama a falon. Kusa dashi sajda ta koma. Bai ko kalleta ba. Idanuwanshi kafe kan ummi.

Da alamun damuwa a muryarta tace.

"Wallahi shiru. Har isha'i na gabatowa. Bai taba dadewa a waje haka ba"

"Allah dai ya dawo mana dashi lafiya"

Tayyab ya fada. Su duka suka amsa da amin.

Zaune suke zugum. Babu mai abin fada. Dawud yaji sajda ta kwanto jikinshi. Dubata yayi yaga bacci take.

A hankali ya ke girgizata.

"Sajda tashi kiyi sallar isha'i tukunna"

Dakyar ta bude idanuwanta. Ganin baccin bai saketa ba yasa dawud kallon zulfa yace.

"Rakata tayi alwala"

Mikewa zulfa tayi ta kama hannun sajda. Machine din abba sukaji. Gabaki dayansu suka nufi hanyar fita.
Har sajda lokaci daya baccin ya saketa. Ita da zulfa rike shi sukai gam kaman wanda suka shekara basu ganshi ba

"Sannu da zuwa"

Ummi ta fadi da murmushi a fuskarta. Murmushin ya mayar mata yana dan daga mata kai. Sannan su tayyab ma sukai mishi sannu.

Ledojin dake hannunshi suka karba suka wuce falon tare.  Hira sukai cike da kaunar juna. Abba ke musu albishir din ya samu aiki.

Fadar farin cikin da kowa yake ciki a ranar bata baki ne. Litinin din tazo
musu da sauyi mai girma.

*

*Bayan wata biyu*

Ta kowanne bangare na rayuwar su Dawud yana tafiya dai dai. Har sunyi hutun gama aji biyar sun koma makaranta.

Yanzun haka watannin da ya rage musu su zana jarabawar aji shidda basu da yawa. Abu dayane ya canza musu. Shine basa samun lokacin abba kaman da.

Yanayin nisan wajen aikinshi yakansa sanda zai dawo daga ummi sai dawud ne basuyi bacci ba. Wani lokacin da tayyab.

Hakan na damun ummi fiye da kowa. Tana kewar mijinta. Dan in ya dawo a gajiye yake shigowa. Washe gari kuma ita tana fama da hidimar yara.

Shikuma yana shirin tafiya aiki. Danma yabarta taci gaba da teaching dinta tunda ya kula tana so sosai. Duk da inda yace ta hakura zata bari.

Takan kula da yanayin shi ya dan canza. Sai ta dora alhakin hakan akan gajiya da yake fama da ita. Abinda bata san yana faruwa ba shine.

*

Da safiyar ranar yana shiga office dinshi ya zauna hajiya beeba tana shigo mishi. Baya so har ranshi.

Saidai ta wuce shi mukami a wajen. Kuma itace sanadin samun aikinshi. Da murmushin nan nata da ya kasa gane ma.anar shi tace

RAYUWAR MUWhere stories live. Discover now