22

8.9K 621 150
                                    

"Ina zeezee din?"

Asaad ya tambayi zulfa, dan daga mishi kafada tayi.

"Nayi da ita ta fito komai bata cemun ba"

Sauke numfashi Asaad yayi, yana duba agogon dake hannunshi, biyar har da rabi, yasan mutane nacan sun taru. Yau sati daya kenan da tsaida sa ranar zainab.

Ita da kanta tace musu in aure zatayi tana son komai daban dana kowa. Tana son bikin da ba'a taba kalarshi a family dinsu ba. Labeeb ya mata alkawari in duka account dinshi zai karar zai mata kalar auren da take mafarki.

Su dukansu tun ranar suke busy. Lectures sai wanda ya zama dole suke zuwa, suna planning party din sa ranar ta. Suna tura invitations da shirye shirye.

Sai yau ranar kuma taqi fitowa su tafi wajen da za'ayi party din.

"Kuje kawai zulfa. A fara komai dan Allah, zamu taho yanzun"

Kai zulfa ta daga mishi ta wuce, Asaad ya sauke numfashi dan jinshi yake wani sama sama. Gabaki daya kwalliyar datai ta daburta mishi lissafi.

Karo yaci da Mamdud.

"Asaad wai baku tafi ba? El-Maska sai kirana yake... Gab yake da exploding"

Dan dafe kai Asaad yayi.

"Anees nacan fa, zeezee ce bansan meye matsalar ba. Taqi fitowa"

"Barin mata magana"

Cewar Mamdud. Da shakku a idanuwan asaad yake kallon shi. Murmushi Mamdud yayi.

"I got this..."

Ya tabbatar ma da Asaad. Kai yadan daga mishi, tukunna ya wuce. Dakin zainab Mamdud ya nufa, kwankwasawa yayi kamun ya tura a hankali.

Zaune take kan gadonta, jikinta sanye da doguwar riga, fara da stones farare sai daukar ido suke. Tayi kyau sosai, duk da kwalliyar fuskarta simple ce.

Dan yasha ganinta da kwalliya fiye data yau. Sai dai bai taba ganin tayi kyau irin na yauba. Tun zuwanshi yake ganin ita da arif sunfi kowa kyau a gidan.

Sosai suke kama da mumynsu. Takalmanshi ya cire sannan ya karasa inda take ya zauna. Cikin sanyin murya yace

"Sis anata jiranki...ki taso mu tafi"

Dan juyo kanta tayi ta kalle shi, muryarta na rawa tace.

"Bansan me yasa nake jin tsoro ba Ya mamdud. Inajin komai na tafiya da sauri, inajin komai na auren nan kaman ba dai dai bane ba.

Niba aure nake sonyi ba yanzun, bansan me yasa yaya yake so ya aurar dani ba..."

Ta karasa idanuwanta na cika da hawaye, dan kwana bakwai din nan sama sama tayi su. Har wayarta kashewa tayi dan bata son tai magana da ishaq din.

Kawai so take tajita shiru, tayi tunanin abinda auren yake nufi da rayuwarta. Komai data tsara ba haka yake tafiyar mata ba.

Kallonta Mamdud yake. A zuciyarshi akwai wajaje fiye da uku da suke jin haushin labeeb kowanne bangare kuma da nashi dalilin.

Amman ko ina ya duba cikin zuciyarshi kaunar su zainab bata da shakku. Yana jinsu har cikin ranshi. Musamman arif, kaunar da yake ma yaron ba zata fadu ba.

"How about kibar El da wannan tunanin? Ki raba mana rashin tabbas din mu daukar miki? Tunanin da zakiyi ya zama na kalar kayan da kike so a cikin gidanki.

Kalar kayan da zaku saka wajen biki, ni da El da su Asaad zamuyi tunanin auren nan shi yafi dacewa dake ko a'a. Baki yarda da El bane?"

Da sauri zainab tace

RAYUWAR MUWhere stories live. Discover now