06

5.6K 511 77
                                    

Dana tashi yau abinda ban tabayi ba nayi. Shin in yau aka sanar dani itace rana daya tak ta karshe da nake da ita me zanyi?

Abubuwa da yawa suka dinga mun yawo. Tunanin me nake dashi na guzurin zaman kabari dazan tafi dashi ya fi komai rikitani.

Wacce shaida mutane zasu yi akaina lolacin da babu ni ya sakani son sake abubuwa da yawa cikin halayyata. Tunanin mutanen dana kullata ya dameni.

Tunanin mutanen dana batama rai ya sakani cikin kunci. Nafilata bata da yawa. Salati na bashida yawa. Karatun Qur'an din danai bamai yawa bane.

Ina da gyara sosai da nake sonyi kamun in tafi. Mutanen da nake son ba hakuri. Mutanen da nake son roka su yafe mun. Mutanen da nake son in yafe wa.

Impression din da nake son bari. Abinda nake so in samu a kabarina amman lokaci yamun kadan.

Yan' uwa. Yau zata iya zama ta karshe tamu. Muyi rayuwa a kowacce rana kaman ba zamu sake samun wata ba.

Muyi ayyuka masu kyau. Mu zauna da kowa lafiya kaman ba zamu sake samun wata damar ba. Mutuwa bata sallama. Abinda mukayi shi zamu samu. Babu kari babu ragi!!!

Allah ka yafe mana ka saukaka mana kwanciyar kabari.(Amin thumma amin.)

Tun farkon satin har karshen shi Aisha ta rasa gane kan auwal. Tun tana iya kokarinta wajen ganin yaran basu gane akwai matsala tattare da abban su ba harta hakura.

Garama sajda. Dan inkaga murmushi a fuskarshi cikin gidan yanzun to sajda ke bayyana shi. Tun da aka haifeta wata irin shakuwa ke tsakanin ta da abban nata.

Har yanzun da canji ya same shi da Aisha ta rasa ko daga ina matsalar take akwai shakuwar nan duk da bata kai karfin ta da ba.

Idanuwa ta dauka ta saka mishi. Duk dare tana tashi ta salloli ta gabatar da addu'o'i abinta. Yanzun ma zaune take kan gado tunda ranar asabar ce ba aiki ke akwai ba.

Tana ta kallon Auwal din yana kai kawo cikin dakin. Ita take tayashi shiryawa da. Yanzun kam baya so tana taba mishi komai.

Idanuwa ta saka mishi badon baya mata ciwo ba. Sai don hakan zai fi musu sauki su dukansu. Wani farin yadi ne ya saka ya dauki bakar hula ya dora.

Turaruka ya feshe jikinshi da su. Sannan ya dauko brief case dinshi da yake zuwa office da ita da ya dauko wasu kayan kala biyu ya saka a ciki.

Kasa jurewa tayi tace mishi.

"Sai ina haka?"

Yanda ya yamutsa fuska kaman jin muryarta kawai wata takura ce a wajen shi yasa wani abu mai zafi sukar mata zuciya.

Kaman bazai amsa ta ba. Can yace.

"Zamu bar gari da yaya. Sai ran litinin zamu dawo"

Lumshe idanuwata tayi. Tana kiran sunayen Allah a ranta. Tana kin barin zuciyarta karanta mata abinda tagani a fuskar Auwal.

Kome yake faruwa bai kai girman abinda bai taba shiga tsakaninsu ya samu wajen zama ba. Ba zata bari ba.

Bude idanuwanta tayi tana kakaro murmushi ta dora a fuskarta da fadin.

"Allah ya kaiku lafiya ya dawo daku lafiya. Daka karya kamun ka fita ai"

Girgiza mata kai yayi. Ya tsugunna gefen gado ya dauko takalmanshi. Ya dauki jakarshi yana ficewa daga dakin batare daya juyo ko ya sake ce mata komai ba.

Mikewa tayi tabi bayanshi. Yana tsaye bakin kofar falon yana saka takalma. Ganin ya sakai ya fice baice mata komai ba yasa ta sake binshi har tsakar gidan.

RAYUWAR MUDonde viven las historias. Descúbrelo ahora