27

7.1K 614 304
                                    

A hargitse suka shiga Harmony. Cikin su babu wanda yake iya cewa komai. Dawud ne yai ma cikin ma'aikatan magana aka fada mishi dakin da Mamdud din yake.

Suka nufi hanyar, suna zuwa gabaki dayansu suka nufi kofar, doc ya fito, ganin su har su biyar yasa shi janyo kofar yana dakatar dasu.

"Ina yan uwan shi?"

"Mu dukan mu"

Anees ya bashi amsa, asaad na karbewa da fadin

"Ya yake? Zamu iya shiga?"

Sauke numfashi Doc din yayi, da dawud ne kawai ya fahimci cewar akwai matsala babba. Dawud ya kalla ganin duk ya fisu nutsuwa yace

"Ka biyoni office"

"Abinda duk zak fada mishi dole zamu sani. Ko mu bika office din mu duka. Ko kuma ka fada mana anan..."

Zainab ta fadi da muryarta dake fita dakyar saboda kukan da tayi. Sosai yake kallon su, yana ganin abinda zainab ta fada a fuskokin su batare da sun furta ba.

Hanyar office din ya nufa suna rufa mishi baya. Cikin su babu wanda ya zauna, duka idanuwa suka zuba mishi cike da tashin hankali. Sai da ya nisa tukunna ya soma bayani a nutse

"Ya ji raunuka sosai, ya karye har waje biyu a hannu daya... Sai karaya daya a kafarshi... Ba zamu iya tsaida magana akan buguwar da yayi a kanshi ba in ba farkawa yayi ba..."

Girgiza kai Asaad yake yana jin sabbin hawaye na tarar mishi cikin idanuwan shi. Zainab kam tunda ya bude bakin sji ya soma magana hawaye ke zubar mata.

Sai dai tasa bayan hannunta ta goge su. Wani abu ne tsaye a wuyan labeeb yaki wuce wa. Ga kirjin shi dake zafi kaman zai fado. Dakyar ya bude bakin shi yace

"Babu wani permanent ciwo?"

Idanuwan shi doc din ya sauke cikin na labeeb cike da alamun tambaya ko zai iya fadar maganar a gaban su zainab.

"Ko meye ka fada kawai...suna da hakkin sani kaman yanda nake dashi..."

Kai yadan dagama labeeb din.

"Iya yanzun abinda zan iya kira permanent a raunukan daya samu shine. Bazai taba samun yara ba..."

"A'a... No... Banda wannan..."

Labeeb yake fadi yana girgiza kai. Bazai yiwu ba. Har a ranshi yanada niyyar daukar mataki akan Mamdud. Baisan Kowanne kala ba, amman ya gama tsarama zuciyarshi koma ta yaya zai dauki mataki.

Mamdud ya cancan ci hukunci mai yawa. Yasan kaunar dake tsakanin shi da arif. Rasuwar arif kawai ta ishe shi tashin hankali, zuciyar shi taki yarda cewa wannan kaddarar ce zata samu Mamdud.

"No... Ka fadamun wani abu banda wannan... Dan Allah kai fixing din wannan... Kowanne kasa... Ko nawa ne zan biya. Ka fadi wani abu banda wannan..."

Labeeb yake rokon likitan. Cike da tausayawa ya kalli labeeb.

"Babu abinda za'a iyayi akai... Kuyi hakuri Allah ya bashi lafiya!"

Hawayen dake shirin zubowa daga idanuwan zainab kansu ji tai sunyi tsaye cik, tare da bugun da zuciyarta take yi. Tasan Mamdud, tasan shi tana zaton fiye da labeeb.

Cikin idanuwan ta take kallon su shekarun baya...

*

Tana zaune dakinta kan gado tana sauraren karatun Qur'an cikin kira'ar sheikh minshawi tana bi a hankali ya turo kofar da murmushi a fuskar shi.

Murmushin ta mayar mishi, saida ayar takai karshe tukunna ta kashe.

"Ya Mamdud... Ka shigo mana"

RAYUWAR MUWhere stories live. Discover now