08

5.1K 513 109
                                    

Rayuwa zata iya canza maka a cikin mintina kalilan. Abinda ka saba dashi zai iya sauyawa zuwa wanda baka taba tunani ba.

Bakin ciki ko farin ciki. Rashi ko samu. Allah na jarabtar bawa ta ko wanne fanni. Karka taba dauka kai kadaine a yayin da duniya tai maka kunci.

Jarabawa ce Allah ya dora maka dan yaga karfin imaninka a gare Shi. Ka zama mai tawakkali da addu'a. Zaka ga sakamakon hakan.

Ba lallai ya faru a lokaci daya ba. Karka gaza. Ka rike addu'a. Kayita cike da imani da mika lamurranka. Allah ya sa mu dace (Amin thumma amin)

Tsaye take tana jiran Auwal ya fito daga dakin hajiya beeba. Yau kwanan su biyar kenan. Idanuwa kawai ta dauka ta saka mishi.

Sai dai taji shigowarshi. Da safe kuma taji fitarshi. Kamar ya manta da ita da yaranne gabaki daya. Sajda ce kawai ke yawan mita abban su ya daina shigowa wajen su.

Su tayyab a fuskarsu taje ganin damuwarsu da yanayin yanda canjin komai na rayuwar yake taba su. Ba zata ce bata damuwa ba. Sai dai abin ya daina mata ciwo.

Balle yanzun data san bayin kanshi bane. Addu'a suke ita da yaranta ba dare ba rana. Canjin da take ji a jikinta ya tabbatar mata da tana dauke da juna biyu.

Haka duk cikin sauran. Ba ya damunta da laulayin nan. Dan zazzabi ne da takanji wasu lokuttan kuma shima da yayi wata biyu shikenan.

Yanzun ma tana jiran taga fitowar Auwal ne ta tambaye shi cewar zataje asibiti. Tunda yasan da zuwanta wajen aiki. Amman hakkinsa ne ta tambaya kamun ta wuce wani waje daban.

Dan gujema tsinuwar mala'iku da fushin Allah. Takai mintina talatin, tun tana tsaye har takai da tsugunnawa. Sannan taga ya daga labule yana wata dariya.

Sauke idanuwanshi yai a kanta. Lokaci daya fara'ar dake fuskarshi ta dauke. Ya koma Auwal din nan da ta kasa gane ko shine mijinta ko akasin hakan.

Muryarta na rawa ta mike da fadin.

"Abban sajda. Ina kwana"

A dakile yace.

"Lafiya. Menene?"

Ta bude baki zatai magana hajiya beeba ta leqo ta bayan Auwal da fadin.

"Alhajina. Ya akayi ne?"

Juyawa yayi ya kalleta da fara'a. Wani abu Aisha taji ya tsaya mata a wuya. Kamun nan yace

"Ina zan sani hajiyata. Na fito ne naga wannan zaune anan"

Wani kallon banza hajiya beeba tai mata.

"Lafiya?"

Ta bukata. Ko inda take Aisha bata kalla ba. Balle tayi tunanin zata kulata. Asalima idanuwanta a kafe suke kan Auwal. Cikin sanyin murya tace.

"Zanje asibiti ne daman. Nace zan tambayeka"

Yamutsa fuska yayi.

"Daga yanzun ba saikin tambayeni ba. Duk inda zakije kije ba matsalata bane"

Kallon shi take tana so tagano mijinta a cikin shi. Auwal dinta data Aura amman ko alamun shi bata gani ba. Hajiya beeba bata son kallon nan da take mishi.

Kishi take ji har kasan zuciyarta.

"Ke kinji saiki wuce ai ko?"

Ko kallonta batayi ba. Ta wuce tana fita daga gidan. Halin ko in kula da Aisha ke nuna mata yana ci mata zuciya.

Haka Shekaranjiya. Da ganga ta jawo Auwal tsakar gida. Dan taji Aisha ta fito ta sumbace shi tana gaya masa kalamai masu kashe jiki.

Amman ga mamakinta, ko inda suke Aisha bata kalla ba. Balle ma ta nuna abinda beeba din tayi ya dameta. Haka ta gama goge takalmanta.

RAYUWAR MUWhere stories live. Discover now