17

8K 599 172
                                    

Flashback (Rayuwar El-labeeb Maska)

Kaman yanda mukaji a baya. Alhaji ibrahim shi kadai yaci gaba da harkar kasuwancin da yai gado na mahaifin shi. Inda bai tsaya iya cikin garin kaduna ba.

Soyayya mai karfi ta shiga tsakanin shi da matarshi hajiya habeeba. Inda yan uwanta suke ganin ta kowanne fanni Alhaji Ibrahim bai dace da ita ba. Bai kai ajin namijin da zata aura ba.

Saboda masu kudine na gaske, a lokacin babanta shine minister mai ci, sannan mamanta lawyer ce babba, su bakwai ne a gidansu. Maza hudu, mata uku, itace ta biyar.

Gabaki daya gidansu, daga doctor,engineer sai daya daga cikin yayenta babban producer ne a industry ta kannywood.

Aurensu da Alhaji Ibrahim ya fuskanci matsaloli da barazana daga danginta. Amman rubutaccen al'amari. Da kuma kaunar ita kanta hajiya habeeba. Haka suka hakura bayan kafa mishi sharudda kala kala.

Na cewar zata ci gaba da aikinta da kuma business dinta da take. Ana kawo mata kaya da dubai da Italy tana siyarwa gari gari. Haka wasu cikin manyan companies na garuruwa takan hada hannun jari dasu.

Soyayyar da Alhaji Ibrahim yake mata yasa ya amince da duk wani sharadi na family dinta. Dan burin shi ya sameta kawai. Hakan akayi. Allah ya azurta su da ya'ya biyar.

El-labeeb shine na farko, Anees da Asad yan biyu ne, zainab sai autansu Arif. Wanda daga Alhaji ibrahim har hajiya habeeba babu mai lokacin kula dasu.

El-labeeb shine dansu na farko, kuma shi hajiya habeeba ta dora duk wani burinta akai, tana so taga ya shahara ya zama wani abu a rayuwa. Yana da shekara shidda a duniya ta dauke shi ta mikama yayanta daya saka shi harkar film.

Hakan bai wahala ba, kasancewar tun yarintar El labeeb abinda yake so bai wuce yaga ya burge mumynshi ba. Dan yana ganin in yai abinda zatai alfahari dashi zaisa ta rage tafiye tafiyen da takeyi ta bashi lokacinta.

Haka rayuwa taci gaba da tafiyar musu, hajiya habeeba bata bada tazara tsakanin haihuwarta ba. Dan kawai so take taga ta huta, yara biyar take ganin sun isheta, dan dakyar ta yarda ta haifi arif bayan zainab.

Asalin labarinsu zai fara lokacin da labeeb ya cika shekaru goma sha biyar a duniya yake aji biyar a secondary school.

**

Zaune yake cikin aji amman gabaki daya hankalinshi na gida. Yana kan arif daya bari hannun yan aiki ga kuma zainab da batace makaranta ba, bata da lafiya.

Mikewa yayi, abdul dake kusa dashi ya kalle shi.

"Ina zaka je?"

Dan daga mishi kafada labeeb yayi.

"Gida, bazan iya zaman makarantar nan ba, beside gobe zan bar garin"

Kallon shi abdul yake kaman yana son suyi musayar matsayi. Girgiza kai labeeb yayi.

"Meye kake kallona haka?"

Murmushi yayi.

"You are so lucky, ka hada duka, kudi, popularity"

"Ba kaso ka zamani abdul, ka yarda dani ba abu bane mai sauqi kasan......."

Kallon da abdul yake mishi yasa shi daukar jakar shi dake ajiye.

"Forget it"

Ya fadi yana ficewa daga ajin. Yanajin yanda idanuwan sauran yan ajin ke binshi harya fice daga ajin ya nufi office din principal ya karbo permit kamun ya fice daga makarantar.

Ba driving bane bai iyaba. Dauko motar ne yake kara janyo mishi attention shisa yake biyo machine duk ranakun dazai zo makaranta.

Gabaki daya a gajiye yake, shooting din da sukayi a kano sam bai huta ba. Haka ya dawo gida ya samu su zainab shima bai hutan ba.

RAYUWAR MUWhere stories live. Discover now