01

14.8K 1.1K 95
                                    

Kar kai tunanin abinda baka samu ba. Zaka kasance marar wadatar zuciya. Kai tunanin abinda ka samu ka zama mai godema Allah.

Karka kalli wanda ya ke gaba dakai. Ba zaka taba jin dadin inda kake tsaye ba. Ka duba wanda yake kasa dakai. Naka matsayin zai maka dadi.

Karka duba baiwar wani da baka da ita. Ka duba wanda bashida kalar baiwar dakai kake da ita. Rayuwa zata zame maka da sauki. Allah ya datar damu (Amin thumma amin)

"Ka nutsu dan girman Allah. Baka san wai gidan nan cike yake da mutane ba?"

Tayyab ke fadi yana kallon Dawud da yasan kiris yake da birkice musu. Numfashi yake ja ta hancin shi yana fitarwa ta baki.

Har lokacin idanuwan tayyab na yawo a fuskar Dawud din a tsorace da abinda yake gani.

"Bana son ganin shi tayyab. Waya fada mishi yana da damar yankemun hukunci?"

Dawud ke fadi muryarshi a dakushe. Kai tayyab ya daga cikin nuna mishi ya yarda da maganarshi hadi da fadin.

"Nasani. Dan girman Allah da matsayin ummi zakai hakuri a gama bikin nan lafiya. Ummi za....."

Katse shi Dawud yai da fadin.

"Karka fadamun abinda ummi zata so da wanda ba zata so ba tayyab. Kasan dan ita kadai nake zaune a gidan nan.

Dan ita kadai nake shakar iska a karkashin inuwa daya da *Shi*"

Yanda ya fadi kalmar shi din yasa wani abu matsewa a kirjin tayyab. Saidai yasan furta abinda yake ji bazai amfanin komai ba. Zaima iya kara musu matsaloli ne.

"Naji dai. Yanzun ka wuce ka shirya. Kaga lokaci na kurewa, karfe hudu muka so a fara program din nan wallahi"

Kallon me kake nufi Dawud yake ma tayyab. Scowl din dake fuskarshi yana kara zurfafa. Da mamaki tayyab ya dora da fadin.

"What is with the look? Kana mun kaman baka san da maganar ba"

"Nasan da maganar. Kaine kakeyin kaman ban baku amsa ta ba wata biyu da suka wuce"

Girgiza ma Dawud kai tayyab yake.

"Kar kace mun da gaske kake nufin maganar ka please. Ba zakai mana haka ba"

Juya idanuwanshi kawai Dawud yayi. Ya raba ta gefen tayyab yana wucewa da fadin.

"Zan dan kwanta"

Bude baki tayyab yayi da niyyar magana Dawud ya katse shi da fadin.

"Raina a bace yake. Don't.....just don't"

Mayar da bakinshi yayi ya rufe yana bin Dawud din da kallo har yabar falon. Sauke numfashi tayyab yayi badon abinda yai din yaba shi mamaki ba.

Saidan rasa mutum mai kalar halayya irin na Dawud din. Ya dauka zai canza tunda bikin nashi ne wannan karin.

Yasan mai zaiyi. In akwai wanda yake jin zai iya lankwasa Dawud yai abinda baya so El-labeeb ne. Wayarshi ya zaro daga cikin aljihu.

Key din jiki yake cirewa yaji motsi. Da sauri ya dago ya sauke idanuwanshi kan zulfa. Nazarinta yake. Idanuwanta sun zurma ciki kaman wadda tai kwanaki batai bacci ba.

Ga wani irin haske dayaga ta kara yi. Idanuwa suka hada tai saurin sauke nata.

"Lafiyarki kuwa?"

Ya bukata. A daburce ta amsa shi da.

"I am ok."

Yanayin amsarta kawai ya sake tabbatar mishi da karya take. Sai dai ba yanzun bane lokacin daya dace ya matsa ta dajin ko menene.

RAYUWAR MUWhere stories live. Discover now