14

7.2K 650 143
                                    

Rayuwa suka ci gaba dayi kaman abba bai zo ba. Dawud na kula da sajda, yanda take ware mishi idanuwa duk idan ya shigo tana son tambayarshi yaushe zasu koma.

Hakan yasa ya zaunar da ita ya fada mata cewa jarabawa zai fara, saiya gama tukunna zasu koma. Cikin sati biyu dawowar abba uku gidan.

Yanda dawud ya fadama sajda cewar sai ya gama jarabawa haka ya fadama abban. Amman da alama bai yarda da maganar daya fadi mishin ba.

Dan yanzun haka da dawud ke zaune kofar gida da handout dinshi yana hango motar abban tana tahowa, yaja numfashi yana fitar dashi.

Ba karamin kokarin tsayawa yake yaima abba magana cikin hankali da nutsuwa ba, bayan babu abinda yake so yayi daya wuce yai mishi ihun dayake jin yana taruwa akanshi har saiya bace ya fita rayuwar su gaba ki daya.

Ganin shi da jin muryarshi bakomai bane a wajen dawud sai takura da tsanarshi dake karuwa. Yana kallonshi yai parking hadi da bude motar ya fito.

Har inda dawud yake ya karaso, hannu yasa ya taba wajen yana so yaga ko da datti, kamun ya zauna, kaman wanda aka tsirama wani abu dawud ya kara matsawa.

Abba na kallonshi da alama baya son jikinsu ko kadan ya hadu, ya rasa me yaron nan yake ji dashi haka.

"Kai baka iya gaisuwa bane?"

Kallon shi dawud yayi da wani irin na yanayi, kamun ya maida hankalinshi kan takardun dake hannunshi. In bai focusing kan wani abu ba matsala za'a samu.

Saboda ummi kawai, dan ummi yake jure duk wannan abin. Haka yaci gaba da fadi cikin kanshi da zuciyarshi. Ganin bashida niyyar cewa komai yasa abba cewa.

"Na ga shiru bakuzo din bane, yasa nace bara inzo mu tafi"

Muryar dawud can kasan makoshi yace.

"Bansan sau nawa zan maimaita magana daya ba, zamu zo da kanmu, sai nagama jarabawa nan da sati uku masu zuwa"

Sosai ran abba ya baci. Dan hajiya beeba tace mishi dawud din raina mishi hankali yake shisa yau a 360 dinshi ya taho.

"Dawud karka rainamun hankali dan kaga ina lallabaka, zan iya maka ku kotu ku dawo dole. Zanbarka sati ukkun ne inga gudun ruwanka.

Da sharadin in baka dawo ba duk matakin dana dauka ka dora laifin hakan a kanka"

Kallonshi dawud yake cikin fuska yana mamakin alaqar da da uba dake tsakanin su. Dan babu komai a zuciyarshi banda tsanar mutumin nan da yake ji har bayan zuciyarshi saboda ta cika fal.

"Bakai kadai kake da sharudda ba. In zamu dawo gidanka zamu dawo harda mami"

Cike da rashin fahimta abba yace.

"Wacece mami?"

So yake ya fada mishi itace matar data zauna tare dasu lokacin da basu da kowa, lokacin da su sajda suke neman soyayya ta uwa, lokacin da suke cikin danyen maraici.

Sai dai baida lokacin dazai asara yana ma mutumin nan bayani. Dan haka yace.

"Kaganta randa kazo, da ita zamu koma"

Abba yasan da wuya hajiya beeba ta amince da wannan abin, dawud na kallon rashin amincewa a fuskar abban tun kamun ya furta hakan.

"Babu inda zamuje babu mami. If ka shirya komawarmu ka shirya harda tata, in baka shirya ba ka aikomun lawyer dinka"

Dawud na karasa maganar ya tattara sauran takardunshi dake kasa yana hadasu dana hannunshi sannan ya mike ya shige cikin gida yana doko kofar kamar ita tai mishi laifi.

Idanuwanshi ya sauke kan na mami dake zaune.

"Lafiya dai dawud?"

Ta bukata, karasa takowa yayi ya ajiye takardunshi kan kujera, daga tsayen ya dafe goshin shi.

RAYUWAR MUWhere stories live. Discover now